Aminiya:
2025-07-23@05:06:05 GMT

NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa

Published: 22nd, July 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Tashin farashin takin zamani yana hana manoma da dama noman wasu nau’ukan abinci.

Manoma da dama sun ƙaurace wa noman masara da shinkafa da aka fi amfani da su a Najeriya sakamakon tsadar takin zamani, abin da masana ke ganin in ba a ɗauki mataki ba, hakan zai kawo ƙarancin abinci a ƙasar.

NAJERIYA A YAU: Abin da ya sa muke yi wa PDP zagon ƙasa —Sule Lamiɗo DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa farashin takin zamani ya yi tashin gwauron zabo a ƙasar.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Masara Tsadar taki tsadar takin zamani

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin

Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ta ce ta ceto wani bene mai hawa biyu daga rugujewa gaba daya sakamakon wata gobara da ta tashi a garin Ilorin.

 

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda y ace gobara da ta tashi a hanyar Muritala Muhammed, daura da Cocin C & S, Ilorin.

 

A cewarsa da isar su, ma’aikatan kashe gobara sun gano cewa wani gini mai hawa biyu da ya kunshi dakuna 8 da shaguna 10 na fuskantar barazana. Ya bayyana cewa, ta hanyar daukar mataki cikin gaggawa da hadin kai, jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar yadda ya kamata, tare da hana yaduwarta zuwa gine-ginen da ke kewaye, inda ta kara da cewa a sakamakon haka, daki daya ne lamarin ya shafa.

 

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wutar lantarki ce dalilin ta tashin gobarar.

 

Da yake mayar da martanin Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara Prince Falade Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su kasance cikin shiri da kiyaye lafiya a gidajensu da wuraren kasuwancinsu.

 

REL/ALI MUHAMMAD RABIU

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hana Natasha Zaman Majalisa Barazana Ne Ga Dimokuraɗiyya — CLO
  • An rufe masana’antu 1,724 bisa rashin bin dokokin aiki a Guinea
  • Asibitin ATBUTH za ta fara gwajin rigakafin zazzaɓin Lassa
  • A tsananta hukunci kan masu dukan mata — Sarki Sanusi
  • Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC
  • Manoma A Kaduna Sun Yabawa Irin Masara Na TELA Saboda Juriyarshi Ga Kwari
  • An kaddamar Da Wani Shiri Na Ba ‘Yan Mata 200,000 Tallafin Audugar Mata A Kano
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin