Jamhuriyar Nijar Da China Sun Kusa Warware Sabanin Dake Tsakaninsu Akan Batun Man Fetur
Published: 12th, July 2025 GMT
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ce, wata majiya mai karfi a jamhuriyar Nijar ta ce; An kusa kusa kawo karshen sabanin dake tsakanin gwamnatin jamhuriyar Nijar da kamfanonin kasar China da suke aiki a fagen hako da tace man fetur, bayan da bangarorin biyu su ka yi nisa a tattaunawar da suke yi.
Sauyin da aka sami shi ne amincewar kamfanin man fetur na kasar China ( CNPC) da sauya tsohon manajan dake tafiyar da ayyuka a Nijar, da wani sabo kamar yadda gwamnatin Yamai ta bukata.
Su ma kamfanonin WAPCO da SORAZ za su dauki sabbin matakai na samar da sauye-sauye a cikin harkokin tafiyar da su.
Ana sa ran cewa, sabbin matakan da kamfanoni na China da Nijar suke dauka zai bude sabon shafi a alakar kasashen biyu da za ta kare manufofin kowane bangare.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai Kan Laifuka A Intanet
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA October 13, 2025
Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025
Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025