An kaddamar Da Wani Shiri Na Ba ‘Yan Mata 200,000 Tallafin Audugar Mata A Kano
Published: 22nd, July 2025 GMT
An shawarci mata da su daina amfani da tsumma ko soson katifa, da takarda a lokacin al’adar su don inganta tsafta da rigakafin matsalolin lafiya.
Jami’ar tallafawa masu kula da tsaftar jinin haila a jihar Kano (MH-NoW) Amina Sabiu Musa ta yi wannan kiran ne a lokacin wani taron karawa juna sani na tsaftar jinin haila ga kwararrun ‘yan jarida da masu fada a ji a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Kano.
A cewarta, shirin na MH-NoW ya shafi ‘yan mata da mata masu shekaru 10 zuwa 24 su 200,000 da nufin magance matsalar talaucin kudin sayen audugar mata a fadin Najeriya.
Ta bayyana cewa shirin wanda Population Services International (PSI) Nigeria ta aiwatar, zai hada da masu raba kayan aikin tsaftar muhalli da za a sake amfani da su don taimakawa wajen rage radadin talauci a wannan banagen.
“Ana gudanar da aikin a wasu jahohin Najeriya, tare da mai da hankali kan dalibai da mata matasa a al’ummomi 15 dake fadin kananan hukumomin Ghari, Tsanyawa, da Nasarawa a Kano,” in ji Amina.
Shima da yake jawabi a wajen taron, mataimakin daraktan bincike da kididdiga na ma’aikatar mata, yara da masu bukata ta musamman ta jihar Kano, Alhaji Zubair Abdulmumin Zubair ya bukaci iyaye da su ba da fifiko ga tsaftar jinin haila ta hanyar samar da kayan tsafta da kuma jagoranci mai kyau ga ‘ya’yansu mata.
Ya nuna damuwarsa kan rahotannin da ke cewa dalibai mata da yawa ba sa zuwa makaranta a lokutansu sakamakon rashin samun kayayyakin tsaftar muhalli da kuma rashin audugar mata a lokacin al’ada.
Ya yi kira ga maza, iyaye, maza da mata da duk masu ruwa da tsaki da su yi watsi da tatsuniyoyi masu cutarwa game da jinin haila tare da tallafawa ilimin haila.
“Dole ne kuma a ilmantar da maza game da jinin haila don su fahimci sauyin yanayi da yanayin da mata ke fuskanta a lokacin al’ada,”
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka zanta da gidan rediyon Najeriya Aminu Abdullahi da Hannatu Sulaiman Abba da kuma Maimuna O. Yusuf sun bayyana taron da ya dace.
A matsayinsu na masu yada labarai, sun yi alkawarin ba da horo ga wasu kuma za su yi amfani da dandamali daban-daban na don Magana akan haila.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa taron bitar ya samu halartar dimbin mahalarta.
Khadija Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA