Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno
Published: 10th, July 2025 GMT
Dakarun sojojin Nijeriya na rundunar sojojin sama tare da haɗin gwiwar Operation Haɗin Kai sun kai farmaki kan wasu muhimman wuraren da ’yan ta’adda suka mamaye a tsaunin Mandara da ke Jihar Borno.
An samu labarin cewa rundunar sojin sama ta gudanar da samamen ta ne a wani wuri da aka san shi da tudu mai tsauni, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, bayan samun bayanan sirri.
Daily Trust ta ruwaito cewa, samamen share fagen ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umurci sojoji da su kawar da duk maƙiya da ke barazana a ƙasar nan.
Kakakin rundunar sojin sama na Nijeriya, Ehimen Ejodame ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, aikin sa ido da binciken da sojojin ke yi ya ba da alamun cewa maharan na shirin kai hare-hare.
Air Commodore, Ejodame ya yi bayanin cewa matsugunin da suke amfani da shi mai amfani da lantarki da na’urar hasken rana da baƙaƙen tutoci, alama ce ta sake farfaɗowar maharan a wurin kafin a kai musu harin bam a tarwatsa su.
A cewarsa, manyan samamen, Wa Jahode da Loghpere, sun daɗe suna zama mafaka ga Ƙungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS), ɓangaren ’yan Boko Haram da ke da matsuninsu a can.
Ya ce, baya ga yadda aka tarwatsa matsunin ta sama da ya lalata kayan aikin ‘yan ta’addar, an kashe da dama daga cikinsu ciki har da kwamandojin su a harin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: tsaunin Mandara
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa.
A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya bikin Pulling Out Parade ɗin ne da ƙarfe 09:00 na safe, inda manyan hafsoshin Soja, da jami’an gwamnati da ƴan uwa za su halarta. Wannan biki na nuni da kammala aikin Soja a matakin ƙoli, kuma yana ɗaya daga cikin manyan al’adun da ake yi wa manyan jami’an da suka yi aiki da ƙwarewa da sadaukarwa.
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP Kasashen Afirka Biyar Da Suka Fi Karfin SojiJanar Musa ya yi aikin Soja na tsawon shekaru masu yawa, kuma ya yi shugabanci a matsayin Shugaban Tsaron Ƙasa daga Yuni 2023 zuwa Oktoba 2025. A wannan lokaci, ya jagoranci manyan hare-haren yaƙi da ta’addanci tare da ƙarfafa hulɗar haɗin gwuiwa tsakanin sassan Sojojin Nijeriya.
A ranar 24 ga Oktoba, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sabon tsarin jagorancin rundunar Soja, inda ya naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Shugaban Tsaro, wanda hakan ya kawo ƙarshen wa’adin Janar Musa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA