Mataimakin shugaban kasar na farko ya jaddada cewa: Kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Iran

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: kalmar mika wuya ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron kasar.

Arif ya ce: Kamar yadda kuke gani kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa, su mutane ne masu wayewa, tare da ingantaccen tarihin al’adu wanda ya wuce dubban shekaru.

Ba su neman yaki, kuma ba su fara shi ba. Sun yi imani da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma a shirye suke don tattaunawa, amma ba za su mika wuya a kowane hali ba.

A wata hira da ya yi da KHAMENEI.IR, Aref ya jaddada cewa: An sha ambaton hakan, sannan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa ba za mu fara yaki ba, amma idan aka tsokani Iran, to Iran zata mayar da martani, kuma haka yake har yanzu. Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba za a taba amince da su ba. An dai tsagaita bude wuta a kasar Labanon, amma kamar yadda ake gani bayan tsagaita wuta an samun adadin shahidai masu yawa. Sadaukarwarsu ta kasance domin kare Iran ce.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: jaddada cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Yemen Ta Bayyana ‘Yancin Kowa Na Walwala A Teku Amma Ban Da ‘Yan Sahayoniyya Azzalumai

Shugaban Majalisar Kolin siyasar kasar Yemen ya jaddada ‘yancin kowa da kowa wajen gudanar da zirga-zirga a teku in banda makiya ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu

Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen, Field Marshal Mahdi al-Mashat, ya jaddada aniyar kasar ta Yemen na ba da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa ga kowa da kowa in banda makiya yahudawan sahayoniyya da kuma masu goya musu baya a lokacin da suke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza.

A cikin wata sanarwa da Al-Mashat ya fitar ya ce: Ba su da wani sha’awar kai hari ga duk wanda ba shi da alaka da goyon bayan makiya yahudawan sahayoniyya, yana mai kira ga dukkanin kamfanonin jiragen ruwa da su mutunta umarni da shawarwarin sojojin Yemen, kuma duk wanda ya yi watsi da shawarar zai dauki nauyi abin da zai biyo baya.

Ya kara da cewa: Sun kafa wata cibiyar gudanar da ayyukan jin kai da za ta hada kai da kamfanonin sufurin jiragen ruwa, domin kauce wa illa sosai.

Al-Mashat ya shawarci kowa da kowa da ya guji yin mu’amala da makiya yahudawan sahayoniyya, yana mai jaddada cewa: Dakarun Yemen masu girma da kuma da’a za su ci gaba da gudanar da ayyukansu da nufin kawo karshen hare-haren da ake kaiwa Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Aragchi: Kofar Iran Ta Tattaunawa A Bude Take, Amma Amurka Sai Ta Biya Kudade Kan Kura-Kuranta
  • Bafarawa Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Mai Suna “Arewa Cohesion Initiative” Don Maganin Kalubalen Da Yankin Arewa Ke Fuskanta
  • Ministan Tsaron Iran Ya Bayyana cewa: Martanin Da Iran Ta Mayar Ne Ya Sanya Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta
  • Kwamandan Sojin Iran Ya Jaddada Kare Kan Iyakokin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci  ya Bayyana Yadda Iran Da Mayar Da Martani Mai Gauni Kan Isra’ila
  • Babban Kwamandan Sojin Iran Ya Bayyana Cewa Iran Ta Koyawa Gwamnatin Isra’ila Hankali
  • Trump Ya Kakabawa Wata Jami’in MDD Takunkumi Bayan Ta Fallasa Laifukan HKI Da Hannun Amurka A Ciki
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Fatali Da Mahangar Yahudawan Sahayoniyya Ta Neman Falasdinawa Su Rusuna Musu
  • Kasar Yemen Ta Bayyana ‘Yancin Kowa Na Walwala A Teku Amma Ban Da ‘Yan Sahayoniyya Azzalumai