Aminiya:
2025-07-11@09:10:12 GMT

Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara

Published: 11th, July 2025 GMT

Rahotanni na cewa ’yan fashin daji masu yawan gaske ne aka tabbatar da kashewa a wani kwanton ɓauna da sojoji suka yi musu a ranar Laraba a jihohin Zamfara da Kebbi.

Sojojin ƙasa da na sama sun yi amfanin da bayanan sirri wajen buɗe wuta kan ayarin ’yan fashin da ke kan ɗaruruwan babura suna zirga-zirga a yankin Yarbuga da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Kakakin Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Alhamis, inda ya ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun rika kokarin guduwa a kafa da kuma kan baburan, amma sojojin suka ci gaba da yi musu ruwan wuta ta ko ina.

Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya

Ya ce, “A wani mummunan hari da dakarun rundunar Fansan Yamma na rundunar sojojin sama ta Najeriya suka kai, sun hallaka ’yan ta’adda masu yawan gaske a ranar tara ga watan Yulin 2025, kan wani ayarinsu da ke tafiya a tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.

“An kai harin ne bisa wasu bayanan sirri da aka tattara da suka nuna ’yan ta’addan da ke kan Babura sama da 150, kowannensu na dauke da akalla mutum biyu da ke dauke da makamai a kusa da kauyen Yarbuga na karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

“Bayan samun gagarumar nasarar a harin ta sama, kashegari dakarun sojojin kasa sun sake kai wani harin, inda suka gano gawarwaki ’yan ta’addan masu tarin yawa da kuma konannun baburansu. Hare-haren sun y mummunan ta’adi ga gungun ’yan ta’addan da ke yankin,” in ji Kakakin sojojin saman.

Kazalika, wata majiya da ke yankin da aka kai harin ta shaida wa wakilinmu cewan ’yan ta’addan na kan hanyarsu ce ta zuwa kauyen Maga a karamar hukumar Zurun jihar Kebbi, lokacin da suka kwashi kashin nasu a hannu.

Ana dai zargin sun fito ne daga wani daji da ke karamar hukumar Anka, daya daga cikin kananan hukumomi hudu na Zamfara da yanzu haka sojojin rundunar Fansan Yamma ke ruwan wuta a kan ’yan ta’addan na tsawon kwanaki.

“Da alama ’yan ta’addan na cikinn mawuyacin hali a yankin, saboda sojoji na ragargazarsu, kuma gas hi an yanke sabis din waya saboda sojoji su ji dadin aikinsu, sannan su kuma ’yan ta’addan bas u da hanyoyin yin waya da ’yan uwansu domin samun dauki,” in ji majiya tamu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Zamfara yan ta addan

এছাড়াও পড়ুন:

HKI: Sojoji 62 Ne Su Ka Halaka A Gaza A Cikin Wannan Shekara Ta 2025

 Jaridar HKI ta “Haaretz'” ta buga labarin da yake cewa: A cikin wannan shekarar ta 2025, sojojinsu da su ka halaka sun kai 62.

A cikin watannin bayan nan an sami karuwar sojojin mamayar da ‘yan gwgawarmaya suke kashewa a Gaza.

Yankin Khan Yunus dake Arewacin Gaza da HKI take riya cewa ta nike shi, sannan kuma ta kori Falasdinawa daga cikinsa, yana daga cikin wuraren da aka yi wa sojojin mamayar kwanton bauna.

Bugu da kari, har yanzu ‘yan gwgawarmayar suna ci gaba da harba makamai masu linzami daga Gaza zuwa matsugunan ‘yan share wuri zauna da suke kusa da Gaza.

A jiya ma dakarun “Sarayal-Quds” na kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da harba makamai masu linzami zuwa  matsugunan da suke da Gaza.

Jaridar ta “Haaratz’ ta kuma ce, Fira ministan na HKI bai yi wa iyalan ko daya daga cikin iyalan sojojin da aka kashe a Gaza ta’aziyya  ba, balle ya gana da su.

Jaridar ta kuma ce, hotunan da ake nunawa na Netanyahu yana ganawa da iyalan sojoji tsoho ne ba sabo ba ne.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya
  • An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba
  • Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja
  • HKI: Sojoji 62 Ne Su Ka Halaka A Gaza A Cikin Wannan Shekara Ta 2025
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 30 A Katsina
  • Kakakin Hafsan Hafsoshin Sojin Iran Ya Ce: Iranta Dorawa Amurka Alhakin Duk Harin Da Ta Fuskanta
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • Kakakin Rundunar Izzuddeen Qassam ya Bayyana Yadda Suka Yi Kofar Rago Ga Sojojin Mamayar Isra’ila