Sin Za Ta Dauki Matakai Don Kiyaye Hakki Da Muradun Kamfanoninta
Published: 27th, March 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce kasar Amurka ta yi amfani da batun kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje, kamar jerin sunayen kamfanoni, wajen sanyawa sauran sassa takunkumai bisa hujjar “barazana ga tsaron kasa, da kuma keta manufofin diplomassiyar Amurka”, wanda hakan ya zama wani babban mataki na nuna fin karfi.
Guo ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum na yau Laraba, lokacin da yake tsokaci game da matakin Amurka na shigar da kamfanonin Sin fiye da goma, cikin jerin sunayen wadanda ta hana su shigar da hajoji Amurka, bisa jadawalin da ma’aikatar kasuwancin Amurka ta fitar. Game da hakan, Guo ya ce bangaren Sin zai dauki matakai don kiyaye hakki da muradun kamfanonin kasar Sin.
Kwalara Ta Kashe Mutum 14, Ana Zargin 886 Sun Kamu A Nijeriya – NCDC ‘Yan ta’adda Sun Kai Hari Sansanin Sojoji, Sun Kashe Uku A BornoDangane da rahoton da Amurka ta fitar game da “ka’idar barazana ta kasar Sin”, Guo Jiakun ya ce, Sin na shawartar Amurka da ta daina kallon dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka da tsohon tunanin yakin cacar baka, ta kuma daina yada kalaman nan na “barazanar kasar Sin”.
Game da tattalin arzikin Asiya kuwa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin za ta sa kaimi ga samun ci gaba mai inganci, da bude kofa ga kasashen waje, da yin hadin gwiwa da sauran kasashen Asiya, wajen ba da sabbin gundumawa, don inganta ci gaban tattalin arzikin duniya. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Samarwa Sassan Kasa Da Kasa Damar Shigowa Ba Tare Da Bukatar Biza Ba
A kwanakin baya, an bude tashar jirgin ruwa ta fasinja ta kasa da kasa ta kasar Sin ta farko, wato tashar jirgin ruwa ta Shekou dake birnin Shenzhen. ’Yan kasuwa daga Argentina, da Chile, da Brazil sun shiga kasar Sin ta tashar bisa sabuwar manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, inda aka rage lokacin daidaita aikin canza jirgi daga awoyi biyu da rabi zuwa kasa da rabin awa. Wannan ya shaida cewa, an aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, ba ma kawai a filin jirgin sama ba, har ma a tashar jirgin ruwa. Hakan ya hanzarta raya cinikayyar Sin da kasashen waje.
Wannan batu ya kasance wani misali, bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba. A cikin shekaru 5 da suka gabata, wato cikin wa’adin aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na raya kasar Sin na 14, gwamnatin kasar ta kara kyautata manufofin shiga kasar ba tare da biza ba a fannoni daban daban, don sa kaimi ga yin mu’amala tare da sauran sassan kasa da kasa.
A halin yanzu, kasar Sin ta bada damar shiga kasar ba tare da biza ba ga kasashe 75, inda yawan kasashen da suke da izinin ratsa kasar Sin ba tare da biza ba ya karu zuwa 55, kana yawan tasoshin bincike dake kan iyakar kasar Sin da sauran kasashe makwabta, inda ake iya shiga kasar Sin ba tare da biza ba ya karu zuwa 60, kana tsawon lokacin da ake iya yada zango cikin kasar ya karu zuwa awoyi 240, wanda hakan ya kawo sauki ga al’ummun kasashen waje, dake zuwa kasar Sin don yawon shakatawa, da yin ciniki da kuma yin ziyara.
Manufofin shiga kasar Sin ba tare da samun biza ba sun shaida cewa, Sinawa suna son baki tun a da can, kuma gwamnatin kasar Sin ta yi imani da fadada bude kofa ga kasashen waje. A shekaru 5 masu zuwa, Sin tana maraba da karin al’ummun kasashen waje da za su shiga kasar Sin, da ganewa idanunsu yanayin kasar da kuma fahimtarta. Kazalika, hakan zai kara shaida cewa, bunkasar kasar Sin na da nasaba da duniya, kana wadatar duniya tana bukatar kasar Sin baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp