Bafarawa Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Mai Suna “Arewa Cohesion Initiative” Don Maganin Kalubalen Da Yankin Arewa Ke Fuskanta
Published: 10th, July 2025 GMT
Ganin irin yawan kalubalen tattalin arziki da siyasa a Arewacin kasan nan ya sanya Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya kaddamar da wata sabuwar kungiya mai taken Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative.
An kaddamar da wannan kungiyoyi ce a wajen wani babban taro da aka gudanar a Arewa House, Kaduna, inda manyan baki da mahalarta daga sassa daban-daban na Arewa suka halarta.
A yayin taron, Bafarawa wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na tafiyar, ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon hanyar da za ta yi maganin baraka da inganta fahimtar juna da kuma karfafa ci gaban mai dorewa a yankin Arewa.
Ya ce Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama da suka hada da rikice-rikicen al’umma, rashin tsaro, zaman kashe wando a tsakanin matasa da wariyar tattalin arziki da kuma lalacewar dabi’u da da suka hade mutanen yankin a da.
Tsohon Gwamnan jihar Sokoton, yace manufar tafiyar ita ce samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomi daban-daban a Arewa, tare da samar da hanyoyi na tattaunawa da sulhu da kuma warware rikice-rikice.
Bafarawa ya jaddada cewa tafiyar za ta maida hankali kan matasa, da aiki tare da gwamnatoci da Sarakuna da Malaman addini da kungiyoyin masu zaman kansu da abokan hulɗa na kasa da kasa, don gina Arewa mai aminci da karfi da kuma adalci ga kowa.
Ya bayyana cewa tafiyar ba ta da nasaba da siyasa, kuma babu niyyar mayar da ita jam’iyyar siyasa ko goyon bayan kowace jam’iyya. Ya ce burinsu ya wuce siyasa, domin suna son aiki da kowa muddin yana da burin ciyar da Arewa da Najeriya gaba. Ya kara da cewa su na bude wajen aiki da kowace kungiya da ke da manufofi irin nasu.
Duk da kasancewar tafiyar ba ta siyasa ba ce, Bafarawa ya bayyana cewa ’yan tafiyar na da ’yancin shiga harkokin siyasa a matsayin kansu ba tare da nasaba da tafiyar ba.
Bafarawa ya kuma sanar da cewa an kammala tsara wata cikakkiyar tsarin taswira (blueprint) da ke kunshe da hanyoyin farfado da Arewacin Najeriya, wadda aka samo daga bincike da nazari mai zurfi kan damar yankin.
A nasa jawabin, Darakta Janar na tafiyar, Dr. Abdullahi Idris, ya bayyana cewa an kirkiro tafiyar ne sakamakon tabbacin cewa kalubalen da ke fuskantar yankin ba za su warware sai da hadin gwiwa da fahimtar juna da tsare-tsaren ci gaba da zaman lafiya.
Dr. Idris ya bayyana tafiyar Arewa Cohesion Initiative a matsayin mafita mai muhimmanci da dacewa da lokaci, wacce ta ta’allaka ne a kan ginshikai uku: gina zaman lafiya, dunkulewar Arewa da ci gaban da za a iya jurewa.
Ya shawarci masu ruwa da tsaki su kasance masu hangen nesa wajen magance matsalolin yankin, yana mai jaddada cewa wadannan matsaloli ba a haifar da su cikin dare daya ba, kuma ba za su warware cikin dare daya ba. Sai dai da hakuri, hadin kai da jajircewa, ana iya samun sauyi mai ma’ana.
Shugaban taron kuma Janar mai murabus, Jon Temlong, ya jinjinawa Bafarawa bisa jajircewarsa wajen ci gaban kasa bayan barin siyasa. Ya ce wannan tafiya tana dauke da dabi’u na gaskiya da ke bayyana Arewacin Najeriya — zumunci, adalci da hadin kai.
Janar Temlong ya ce shugabancin tafiyar yana dauke da fatan al’umma da dama, yana mai bayyana cewa wannan kaddamarwa na iya zama sauyi mai muhimmanci a kokarin Arewacin Najeriya na neman zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Taron ya samu halartar jama’a da dama daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya, alamar goyon baya da hadin kai ga wannan tafiya.
COV: Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Arewa Cohesion Initiative Arewa Bafarawa Kaddamar KalubalenYankin Kungiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Najeriya ta casa Jamhuriyar Benin 4-0
Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta.
Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa. A gaba kuma, an hada Victor Osimhen da Akor Adams domin tayar da kura.
Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika masa. Cheetahs sun yi kokarin farkeaw a minti na 12, amma Calvin Bassey ya dakile harin.
Na yafe wa Maryam Sanda —Mahaifin Bilyaminu Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya AbdullahiA minti na 22, Osimhen ya kusa kara ci, amma dan wasan baya na Benin ya hana shi. Sai dai a minti na 38, Chukwueze ya sake aika masa da wata kwallo, kuma Osimhen bai yi wata-wata ba — ya zura ta biyu! Najeriya 2, Benin 0.
Bayan hutun rabin lokaci, Benin sun fara da matsa lamba, amma Osimhen ya sake daukar hankalin duniya — inda a minti na 51, ya cika hat-trick dinsa! Kwallo ta uku ke nan a hannunsa.
Super Eagles sun ci gaba da matsa lamba, inda suka nemi ci na hudu a minti na 68, amma Ndidi ya kasa cin kwallon da aka buga masa.
A minti na 90 Onyeka ya zura wa Super Eagles kwallon Najeriya na hudu a ragar Jamhuriyar Benin.
Wannan wasan ya nuna cewa Osimhen ba dan wasa bane kawai — jarumi ne, gwarzo ne, kuma jagora ne a fagen kwallon kafa.
Najeriya na kan gaba a wannan fafatawa, kuma alamu na nuna cewa Super Eagles na kan hanya madaidaiciya zuwa Kofin Duniya ta 2026.