Gwamnatin Iran Ta Kira Yi Al’ummar Kasar Da Su Fito Domin Halartar Jerin Gwanon Ranar Kudus
Published: 26th, March 2025 GMT
Mai Magana da yawun gwamnatin Iran malam Fatima Muhajirani ta yi ga al’ummar Iran da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar jerin gwanon ranar Kudus ta duniya, wacce take fatan ganin ta taka rawa wajen taimakawa al’ummar Falasdinu.
Muhajirani wacce ta yi bayanin haka a wata hira ta tashar talbijin ta kuma kara da cewa; Gwargwadon yadda al’umma za su fito wajen yin jerin gwanon saboda hadakar da ake da ita a tsakanin al’ummar Iran da Falasdinawa ta fuskokin addini da al’adu, da kuma tarayya akan manufofin juyi, tasirin haka zai fi fitowa.
Malama Fatima Muhajirani ya kuma ambato maganar Imam Khumaini ( r.a) akan fatansa na ganin an sami fitowa mai yawa domin karfafa al’ummar Falasdinu.
A na gudanar da jerin gwanon ranar Kudus ta kasa da kasa ne a kowace ranar juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Gwamnonin Jihohi Ta Jajintawa Jihar Adamawa Bisa Ambaliyar Ruwa A Yola
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhinin sa kan rahotannin ambaliya mai tsanani da ta faru a Yola, Jihar Adamawa, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane, da asarar dukiyoyi da kuma raba dimbin jama’a da muhallansu.
A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya ce kungiyar NGF na jajantawa gwamnatin Jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayin da suke kokarin tara kayan agaji da daukar matakan rage illar wannan iftila’in.
Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yaba da matakin gaggawa da ‘yan sanda da kuma dakarun sojin Najeriya suka dauka na tura rundunonin ruwa, bisa gayyatar gwamnatin jihar, domin taimaka wa al’ummar da abin ya shafa a wannan lokaci na halin kaka-ni-ka-yi.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa kungiyar za ta bayar da nata tallafin domin taimakawa al’ummar jihar bisa halin da suka tsinci kansu a ciki.
Ali Muhammad Rabi’u