Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari
Published: 11th, July 2025 GMT
A daya bangaren kuma
Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka.
Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna fuskantar kalubale na yi wa al’umma aiki ta hanyar samar da damammaki, rage talauci da kuma tsantseni wajen sarrafa dukiyar al’umma.
Duk da cewa, har yanzu akwai sauran rina a kaba, amma abin da na gani a dan wannan lokaci da na ziyarci wadannan jihohi uku, tattakina zuwa Jihar Zamfara; shi ne mafi matukar tsoro a wajena
Zuwa Gusau
A karon farko da aka gayyace ni zuwa babban birnin jihar, Gusau, sai na yi watsi da tafiyar. Domin kuwa, a tafiya irin wannan akwai bukatar yin tunani da nazari mai zurfin gaske, musamman ganin yadda nake samun munanan labarai a kan Ado Aliero da sauran tawagarsa ta ‘yan ta’adda da ke yankin.
Har ila yau, sai aka sake turo min da wata gayyatar. Amma dai, a wannan karon akwai dan kwarin gwiwa, musamman ganin cikin tawagar da zan bi na tattaunawa ta farko da za a yi da Gwamna Dauda Lawal kai tsaye a kan wa’adin shekaru biyu da ya kwashe kan mulki. Tawagar ta kunshi; Gbenga Aruleba daga gidan talajin na AIT, Reuben Abati, ARISE TB da matarsa, Kiki, sai Ahmed Shekarau daga Media TRUST, Onuoha Ukeh daga SUN da kuma Babajide Otitoju, wanda Olajumoke Olatunji ya maye gurbinsa daga TBC.
ChatGPT da Gusau
Amma fa akwai matsala. Ta yaya za mu isa Gasau, duk da sanin abin da muka sani, na tambayi ‘ChatGPT’. Sai amsa min da cewa, kada ku tafi idan har tafiyar ba mai muhimmanci ba ce.
Ya ba da sanarwar tafiye-tafiye daga ofishin harkokin waje na burtaniya, Australia, Canada da kuma Amurka tare da gargadi game da tafiye-tafiye saboda tashin hankali, ta’addanci da kuma garkuwa da mutane, yana mai bayyana cewa; “Babbar matsaya daga hukumomin kula da tafiye-tafiye, ba ta ba da shawarar yin tattaki zuwa Jihar Zamfara, idan har ba akwai bukatar yin hakan ba.
“Titin Zariya zuwa Zamfara, musamman Funtua da ke Jihar Katsina, Tsafe, Maru-Dansadau, an bayyana su a matsayin wasu yankuna na mutuwa, wato wani filin wasa ne na Dogo Gide da Bello Turji, wanda tawagarsu ta ‘yan ta’adda suka kashe matafiya akalla 20, kamar yadda rahoton AP ya bayyana a watan Afrilun wannan shekara. Ina kan hanya, amma na kudiri niyyar tafiya.
Mutuwa da dawowa
Na yi ta mutuwa ina dawowa a cikin awa biyu da minti sha biyar, tsoro ya gama kama ni tare da alhinin cewa; idan na mutu a shekara 60, ba wai na mutu da kuruciya ba ne. Ban san cewa, matata ta lallaba ta sanya min wani abin kariya a cikin wata ‘yar karamar kwalba.
Gaba-daya ban lura ba, sai da na dawo daga tafiyar ina goge jakata, wannan ya isa ta bugi kirji da cewa; ta taimaka min da wani sirri na kariya. Na kasance a ankare cikin tsawon wannan tafiya ta kimanin kilomita 450 daga Abuja, cike da dimuwa.
Abin da ya ba ni mamaki, titin da ke tsakanin Zaiya da Katsina, mai layi biyu ne, sannan kuma yana da kyau sosai; titin bai tsuke ba sai da muka shiga Katsina, kana kuma ya sake bude bayan mun yi nisa ga duwatsu masu ban sha’awa da tsaunika da dukkanin bangarorin titin biyu. Amma titin Abuja zuwa Kaduna, abin kunya ne idan aka kwatanta shi da wannan, amma duk da haka; babban titin Abuja zuwa Kadunan ya lalace, kai ka ce shi ne kofar shiga Arewa Maso Yamma.
Fargaba da dimuwa…
Bayan Zariya, a wasu lokuta, mun wuce garuruwa masu yawan jama’a, amma mafi shahara a cikinsu shi ne garin Funtua, garin wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa da suka hada da marigayi Malam Ismail Funtua da kuma fitaccen dan kasuwa, Umaru Mutallab.
Kowa ya yi tsit, kuma na kasa tambayar kaina cewa; ko mutanen da ke zaune a kauyukan da kananan garuwan da muke ratsawa, sun san abin da ake fada game da su kafafen yada labarai? Yayin da muka shiga Tsafe, garin daya daga cikin manyan ‘yan ta’addan da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane, wadanda suka samu nasarar share wajen zama a Jihar Katsina kafin ziyarar tamu, duk gashin da ke jikina sai da ya tashi.
Duk da cewa, mun samu rakiyar jami’an ‘yansanda ga kuma shingayen sojoji da dama a hanyar, yayin da muka isa Tsafe, kilomita 48 zuwa Gusau, ba ku ga irin tsoro da firgicin da ke cikin motarmu ba. shiru kake ji kowa ya yi dif.
Bayan Tsafe, na yi zaton tashin hankali ya kare a wannan tafiya. Sai kuma na ji na samu sauki tare kuma da shiga rudani da muka shiga Gusau. Saukin shi ne da muka isa lafiya, rudanin kuma saboda titi mai hannu biyu da ake dab da kammala, wanda ya hade da na Zamfara mai tattare da hadari da ban tsoro a tare da shi.
An samu canji
Ashe da rabon zan ga irin wadannan al’amuran a Enugu, inda rabo da zuwa tun
2006 (lokacin Chimaroke Nnamani yana gwamna). Ziyarar da na yi zuwa Zamfara na yi ta tun a farkon shekarun 1990, lokacin tana hade da Jihar Sakkwato
Jiha
Bayan wani Kantoman Mulkin Soji daya, da kuma wasu gwamnonin farar hula hudu, kafin Dauda, na biyar, Zamfara ta kasance wani abu kamar tallan shirin wasan kwaikwayo na Kannywood, inda ‘yan siyasa ke kwashe dukiyar kasa, ciki har da jama’arta, tare da nuna iko ko shakka babu Dauda zai iya nuna bambanci a wannan tsari. A cikin shekaru biyu, ya inganta asibitocin tuntuba da ke Gusau zuwa asibitin koyarwa mai dauke da wasu kayan aiki na zamani, ya kuma inganta harkar samar da ruwan sha, sannan ya kawar da koma bayan kudin WAEC da NECO na dalibai, lamarin da ya sa jihar ta kasance da ta samu kyakkyawan sakamako na tsawon shekaru. Haka kuma ya gina sabon filin jirgin sama wanda za a iya budewa kafin Satumba.
Gwamnati ta ce ta biya basussukan gratuti da kuma fansho ga ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha tun daga shekarar 2011, da aka kiyasta kudin sun kai Naira biliyan 13.6, baya ga biyan bashin albashin watanni hudu da ya gada tare da kara mafi karancin albashi daga Naira 7,000 duk wata zuwa Naira 70,000.
“Komawar harkoki”
A lokacin da ake tattaunawar kai tsaye da Abati ya tambayi Dauda yadda ya sanya jihar a kan turba mai ban sha’awa, ciki har da ba ta wutar lantarki ta farko tun bayan da aka kirkiro ta shekaru 29 da suka gabata, gwamnan ya ce hakan ya faru ne ta hanyar toshe leken asiri ta hanyar amfani da fasaha, da kuma ba da fifiko wajen bunkasa albarkatun jama’a da kuma inganta karfinsu.
Ya ce an kuma yi amfani da fasaha don tattarawa da yin amfani da bayanan sirri don gina jiha mafi aminci, yana mai shan alwashin cewa ba za ai yi sulhu da ‘yan fashi da masu laifi ba.
Idan rayuwar dare ta daidaita a Gusau, babu shakka dukkan jama’ar da suka rasa matsugunai da wuraren sana’a za su dawo inda suke musamman gonaki a hankali. Wannan kuma wani hangen nesa ne da mutum zai iya duba jihar da aka ayyana kusan shekaru talatin ta hanyar cusa tsattsauran ra’ayi na addini, sata da kuma ‘yan fashi.
Ishiekwene Babban Editan LEADERSHIP kuma mai Rubuce-rubuce a Kafofin watsa labarai da harkokin Kudi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Labari
এছাড়াও পড়ুন:
Na Biya Bashin Garatutin Naira Biliyan 13.6 Da ’Yan Fanshon Zamfara Ke Bi Tun 2011 – Gwamna Lawal
Sanarwar ta ƙara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga ƙarananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin kuɗaɗen garatuti.
Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen daidaita biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati, musamman waɗanda suka yi ritaya bayan shekaru 35 suna aiki kuma suka kai shekaru 60.
“Gwamnatinmu ta gaji sama da Naira Biliyan 13 a matsayin bashin kuɗaɗen garatuti na waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomin daga 2011 zuwa 2023, jinkirin ya jawo wahalhalu, kuma wasu da suka yi ritaya sun mutu su na jiran a biya su haƙƙin su, Allah ya jiƙan su da rahama.
“Don magance wannan rashin adalci, mun kafa kwamitoci guda biyu domin su duba tare da ba da shawarar biyan duk wata garatuti da aka riƙe wa waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomi, a lokacin da muka karbi ragamar mulki shekaru biyu da suka wuce, duk da ƙalubalen tattalin arziki da zamantakewa, mun biya ma’aikatan gwamnati albashin watanni uku tare da biyan su alawus-alawus. Mun kuma daidaita alawus-alawus na alƙalai da ma’aikatan shari’a na tsawon shekaru.
“Mun daidaita duka waɗannan abubuwa. Lokacin da muka karbi mulki, mafi ƙarancin albashi a jihar ya kasance Naira 7,000.00 ne kacal, mafi ƙarancin albashi na N30,000, wanda aka amince da shi a shekarar 2019, gwamnatin da ta shuɗe ba ta taba aiwatar da shi ba, saboda sanin nauyin da ya rataya a wuyanmu, mun aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N30,000.00 nan take.
“Bayan mun duba tsarin mafi ƙarancin albashin da ya ƙaru daga N30,000 zuwa N70,000.00 a watan Yulin 2024, mun aiwatar da sji bayan duk matakan da suka dace, ta yadda a cikin shekaru biyu na mulki, mun ƙara mafi ƙarancin albashi a jihar daga N7,000.00 zuwa N70,000.00.
“Bugu da ƙari kuma, mun bullo da kuma aiwatar da hanyoyin kyautata wa ma’aikata a yayin bukukuwan Sallah da kuma ƙarin garabasar albashin ƙarshen shekara, wanda aka fi sani da albashin wata na 13 ga duk ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman gwamnati, ba a taba yin hakan ba a tarihin jihar.
“Sakamakon biyan kuɗaɗen garatuti ya ƙara wa ma’aikata kwarin gwiwa tare da dawo da amincewar jama’a kan harkokin mulki, za mu ci gaba da tabbatar da samar da kuɗaɗen fansho cikin gaggawa, domin yin hakan, gwamnatin jihar a shirye take ta haɗa gwiwa da ƙungiyoyin ‘yan fansho domin tafiya daidai da sauye-sauyen da muka yi.
“Yayin da nake samun wannan rahoton, ina so in yaba wa ƙoƙari da jajircewar ‘yan kwamitin, wannan ba abu ne mai sauƙi ba, ina sane da ƙalubalen da ‘yan kwamitin suka fuskanta a yayin gudanar da aiki, ba yaba da jajircewarsu.
A yayin ƙaddamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da yin garambawul a harkokin fansho na jiha da ƙananan hukumomi.
“Gwamnatina ta kafa wani kwamiti da zai duba ayyukan da suka gabata na hukumar fansho a jihar, kwamitin ya kammala aikinsa tare da bayar da shawarwari kan yadda za a ci gaba, wani bangare na shawarwarin shi ne kafa kwamitin aiwatar da ayyukan fansho.
“Don bin tsarin Ma’aikatar Shari’a, Hukumar Fansho ta Jiha, da duk masu ruwa da tsaki za su duba tare da sabunta dokar fansho ta Jihar Zamfara domin Majalisar Dokokin Jihar ta amince da ita cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp