Amurka Tana Son Matsawa Kasashen Afirka Karbar ‘Yan Gudun Hijira Da Wadanda Ta Koro Daga Kasarta
Published: 14th, July 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka ya dauki matakin matsin lamba kan shugabannin Afirka dangane da tarbar ‘yan gudun hijira da wadanda ya koro su daga Amurka
Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump, ta matsa lamba kan shugabannin Afirka 5 kan su yi maraba da bakin haure daga wasu kasashe a lokacin da Amurka ta kori su.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran Reuters ya fitar bayan ya nakalto daga wasu jami’ai da suke da masaniya kan ganawar shugaban Amurka da shugabannin kasashen Afirka biyar ya bayyana cewa; Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump, ta sanya matsin lamba a wannan makon kan shugabannin Afirka biyar da su yi maraba da bakin haure daga wasu kasashe idan za su bar Amurka.”
A ranar Laraba ne Trump ya karbi bakuncin shugabannin kasashen yammacin Afirka 5, Mauritania, Liberiya, Senegal, Guinea-Bissau, da Gabon, a wani karamin taron da aka shirya kawo karshensa a ranar Juma’a, a kokarin da Washington ke yi na zurfafa huldar kasuwanci da tekun Black Sea.
An gabatar da shirin ne ga shugabannin kasashen Laberiya, da Senegal, da Guinea-Bissau, da Mauritania, da Gabon, a ziyarar da suka kai fadar White House ranar Laraba, kamar yadda wani jami’in Amurka da wani jami’in Laberiya ya bukaci a sakaya sunansa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
’Yan sanda a jihar Legas sun kama wani tsohon fursuna tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a jerin laifukan fashi da yankan aljihu a jihar kwana biyar da fitowa daga kurkuku.
Tsohon fursunan mai shekaru 25 da haihuwa, Segun Kolawole, an kama shi ne bayan kwana biyar da aka sako shi daga cibiyar gyaran hali ta Kirikiri, a jihar Legas.
Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano SpalletiSauran wadanda aka kama tare da shi sun haɗa da Sodiq Isa mai shekaru 27 da Adekanmbi Ganiu mai shekaru 21.
Rahotanni sun nuna cewa an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifukan yankan aljihun mutane da sauran laifukan sata a sassa daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da cafke Kolawole, inda ta ce an kama shi da misalin ƙarfe 8 na safiyar Talata a kasuwar Oshodi, bayan jami’ai sun lura da motsinsa da ya zama abin zargi.
Adebisi ta ce an same shi da tsabar kuɗi ₦80,000 da wayar Infinix Note 40 Pro, waɗanda aka gano daga wani fashi da ya aikata a Opebi, inda ake zargin ya saci ₦200,000 da wayar daga hannun wani ɗan kasuwa da ke barci.
“Bincike ya ƙara tabbatar da cewa ya riga ya sayi sabbin kaya da takalma da wani ɓangare na kuɗin da ya sata, waɗanda suma aka kwato su daga hannunsa,” in ji ta.
Haka kuma, a wani samame daban da aka gudanar da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Juma’a, jami’an RRS sun kama Sodiq Isa da Adekanmbi Ganiu bisa zargin yunkurin satar wayoyin hannu daga hannun fasinjoji a sassa daban-daban na Legas.