Lakurawa sun kashe ’yan sanda 3 a Kebbi
Published: 12th, July 2025 GMT
’Yan ta’addan Lakurawa sun karbe ’yan sanda uku har lahira a yankin Gozirma da ke Ƙaramar Hukumar Bunza a Jihar Kebbi.
’Yan sandan sun kwanta dama ne a yayin musayar wuta a yayin da ’yan ta’addan da ke ƙoƙarin kai hari ga matafiya a kan Babbar hanyar Gozirma zuwa Till.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Kebbi, ya sanar da cewa a yayin ƙazamin faɗan, “an kashe ’yan ta’adda da dama, amma wasu sun tsere da raunukan harbi a jikinsu.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Bello M Sani, ya yaba da namijin ƙoƙarin jami’an rundunar da ke yankin Zurmi da suka kai wa matafiyan ɗauki.
Direba ya tsere da buhun masara 463 Ɗalibi ya ƙone budurwarsa mai tsohon ciki har lahiraYa yi musu addu’ar samun rahama tare da kiran jama’a da su kwantar da hankali su ci gaba da harkokinsu.
Ya kuma buƙaci su kai wa cibiyar jami’an tsaro mafi kusa rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi ko wani take-taken da ba su aminta da shi ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a RibasMajiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.
“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.
Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).
Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.
Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.
Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.