Ranar Kudus: al’ummar Iran zasu nuna hadin kan su ga duniya_ Pezeshkian
Published: 27th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar JUma’ar kashe ta watan Ramadana da ke gabatowa, yana mai jaddada cewa hakan zai nuna matukar goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Falastinu.
Pezeshkian, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar ministocin kasar na farko sabuwar shekarar kalandar farisa, inda yake cewa “Ina fatan tare da halartar al’ummar kasar, za a gudanar da ranar Kudus mai daraja, kuma a wannan rana al’umma za su nuna hadin kai ga duniya.
Ranar Kudus ta duniya dai marigayi Imam Khumaini ne ya ayyana ta kuma ana gudanar da ita a kowace shekara a ranar Juma’ar karshe ta azumin watan Ramadan domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu.
Ta kasance wani gangami na duniya ga musulmi da masu neman ‘yanci a wajen bayyana goyon bayansu ga al’ummar Falastinu tare da yin Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa yankunan Falastinawa da kuma cin zarafin da take yi wa masallacin Kudus.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ga al ummar ranar Kudus
এছাড়াও পড়ুন:
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata
Shugabannin biyu sun yi nazari kan muhimman fannonin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Faransa, inda suka amince da zurfafa hadin gwiwa don samun ci gaban juna da kwanciyar hankali a duniya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa ba a bayar da wani dalili na sauya wannan hutun ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp