NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki
Published: 11th, July 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Matasan Najeriya da dama suna son yin arziki amma ba tare da sun sha wahala ba.
Sau da yawa matasa sun fi neman hanya mafi sauki da za ta basu arziki ba tare da sun sha wahala ba.
NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu?Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa bin yanke don tara abin duniya.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa.
Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News.
Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a KebbiƊaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki.
Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a fi buƙatar ƙwarewarsa.
Da aka tambayi inda za a tura shi, majiyar ta ce Sufeton Janar na ’yan sanda ne zai bayyana hakan, tare da jaddada cewa Adewale ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a matsayin kwamishina.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta ƙasa, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da wannan sauyi, inda ya ce sauyin wajen aiki al’ada ce da ake yi domin inganta ayyukan jami’an rundunar.