Gwamnatin Kano Ta Maida Gidan Marayu Zuwa Cibiyar Gyaran Mata Masu Shaye
Published: 22nd, July 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano ta kara zage damtse wajen farfado da mata masu shaye-shayen miyagun kwayoyi ta hanyar mayar da Cibiyar Gyaran Matan Gaya, wadda a da ya kasance gidan marayu, zuwa wurin gyaran tarbiya.
Kwamishiniyar harkokin mata, yara da masu bukata ta musamman, Hajiya Amina Abdullahi Sani, ta jagoranci wata babbar tawaga zuwa cibiyar da ke Gaya domin tantance bukatun gyare-gyare da kuma hada kai da ma’aikatu domin gudanar da aikin.
Tawagar ta hada da kwamishinan ayyuka Engr. Marwan Ahmad Badawi, tawagarsa ta fasaha, daraktoci, da mataimaka daga ma’aikatar harkokin mata.
A yayin ziyarar, kwamishinar ta bayyana wa takwararta na ma’aikatar ayyuka irin ayyukan da ake bukata domin inganta cibiyar, da suka hada da gyare-gyare da fadada gine-gine domin daukar da kuma gyaran tarbiyar mata masu shaye-shayen miyagun kwayoyi a cikin yanayi mai aminci da tallafi.
A nasa jawabin, kwamishinan ayyuka Eng. Marwan Badawi ya bayar da tabbacin cewa ma’aikatar ayyuka za ta hada kai da ma’aikatar harkokin mata domin bayar da tallafin fasaha da ababen more rayuwa.
“Za mu tabbatar da cewa wannan ginin ya cika ka’idojin da ake buƙata don tallafawa yadda ya kamata don farfado da matan mu da ke fama da shaye-shayen ƙwayoyi,”
Tawagar ta kuma kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Gaya, inda suka sanar da shi shirin gwamnatin jihar na yin wannan hubbasa.
Sarkin ya bayyana goyon bayansa tare da yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya bayyana a matsayin jagoranci mai hangen nesa da tausayi.
Gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ci gaba da jajircewa wajen baiwa masu karamin karfi tallafi tare da samar da yanayi mai kyau na farfadowa da sake dawo da mutanen da suke fama da shan miyagun kwayoyi musamman mata.
Rel/Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.
Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.
Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.
BBC