2025-07-11@21:01:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4661

«yan sanda su»:

    An dai yi ta tsokaci kan cewa ko Obi zai amince da mukamin mataimakin shugaban kasa tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kamar yadda ya yi a 2019. Obi ya ce, “Takarar shugaban kasan Nijeriya zan yi a 2027, kuma na tabbatar da cancanta.” A kan ko zai hakura ya zama mataimakin takarar Atiku a 2027, Obi ya bayyana cewa, “Wannan abun wasa ba ne, babu wanta ya tattauna hakan. Mutane ne kawai yin irin wannan tunani. Amma a zahirin gaskiya babu wanda ya bayyana hakan.” Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya kuma jaddada cewa har yanzu yana shi mamba ne a jam’iyyar LP. LEADERSHIP ta ruwaito cewa Obi yana daga cikin shahararrun mutane a cikin hadakar ADC da...
    Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa na shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma sauran al’ummun duniya. Kowa ya san yankin Taiwan wani bangare ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, kuma wannan shi ne matsaya daya da al’ummun Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 ciki har da jama’ar yankin Taiwan da yawansu ya kai miliyan 23 suka dauka, wanda kuma ra’ayi ne daya tilo da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai. Sanawar Alkahira da sanarwar Potsdam da dai sauran takardun shari’a sun aza ingantaccen tubali ga dokar kasa...
    A dokar hukumar zabe ta 2010 sashe na 124, biyan kudi ga wani a matsayin cin hanci a kowane irin zabe ko karbar kudi ko kyauta domin jefa kuri’a ko hana jefa kuri’a a kowane zabe babban laifi ne da ke da hukuncin tarar naira dubu 500, 000 ko daurin watanni 12 a gidan gyaran hali ko kuma duka biyu. A kowane zabe kama daga na shugaban kasa zuwa kansila, Hukumar Zabe da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar kalubale daga masu sayen kuri’a da ke canzawa masu zabe zaben ra’ayin kan su zuwa zaben wanda aka ba su kudi ko ma kin yin zaben. Duk da kama masu sayen kuri’a da hukumomin yaki da cin hanci...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta bayyana dalilin da ya sa ta gayyaci malamin addini Sheikh Lawal Triumph. A wata sanarwa da ta fitar, ’yan sanda sun ce sun sani cewa wasu daga cikin wa’azozin da Sheikh Triumph ke yi suna haddasa rashin jituwa a tsakanin al’ummar jihar. Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote Rundunar ta ce kowa na da ’yancin faɗin albarkacin bakinsa, amma dole ne komai ya kasance bisa doka. Saboda haka ne Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, ya gayyaci Sheikh Lawal Triumph don tattaunawa da jami’an gwamnati, shugabannin addini da na al’umma. Manufar...
    Kamfanin dillancin labarun “Associated Press” wanda ya sami hotunan tauraron dan’adam na cibiyar sojojin Amurka dake “al-udid” a kasar Qatar, ya nuna yadda harin ya sami wata Qubba, da a cikinta akwai na’urorin sadarwa da Amurka ke amfani da su.” Hotunan tauraron dan’adam na ” Planet Labs” sun nuna yadda Qubbar ta sansanin Amurka a Qatar take sa’o’i kadan gabanin a kai harin a ranar 23 ga watan Yuni. Rundunar Amurka ta 379 mai aikin ttatara bayanai ta kafa wannan Qubbar ne tun a 2016 da kudin da sun kai dalar Amurka miliyan 15. Haka nan  kuma tauraron dan’adam din ya nuna yadda qubbar ta  bace, da kuma yadda ginin da yake  kusa  da ita ya illata. Kamfanin dillancin labarun...
    Tashar talabijin din “Cane” ta HKI ta bukaci Amurka da ta kafa kawance mai fadi na kasashe domin fuskantar kasar Yemen. A yayin ziyarar da Fira ministan HKI, Benjamin Netanyahu a Amurka ne dai ya bijiro da wannan bukatar, kamar yadda rahoton tashar talabijin din ta “Cane” ya ambata.  Rahoton ya kuma ce, Jami’an HKI sun sanar da Amurka cewa, ci gaba da hare-haren Yemen, ya tashi daga zama matsalarta ita kadai, don haka da akwai bukatar kai hare-hare na hadin gwiwa da Amurka da kuma shigar da kasashen wannan yankin da kuma wasu na duniya.” Tun daga 2023 ne sojojin Yemen suke kai wa jiragen ruwa na HKI hare-hare a cikin tekun “Red Sea” ko kuma wadanda su ka...
    Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar  wanda ya yi hira a wata tashar talbijin din kasar ya yi amfani da salon maganar wani mawakin Amurka  mai suna Flavour Flav da ya shahara a shekarun baya, wajen mayarwa da shugaban Amurka Donald Trump martani da cewa: Babu abinda zai iya yi ma ka.” Jaridar Wall Street Jouran ta buga labarin dake cewa; A yayin taron da aka yi a tsakanin wasu shugabannin kasashen Afirka biyar da shugaban kasar Amurka a fadar White House, an bijiro musu da karbar bakuncin ‘yan ci-ranin kasashe waje da Amurka take son kora daga cikinta. Jaridar ta ambaci Nigeria a cikin kasashen da Amurka ta bijirowa da bukatar ta karbi bakuncin ‘yan ci-ranin kasar Venezuela...
    Rundunar sojan mamaya ta sanar da kashe  daya daga cikin jami’an sojojinta dake karkashin rundunar “Golani” a yankin Khan-Yunus dake Gaza. Da safiyar yau Juma’a ne dai sojojin mamayar HKI su ka snar da cewa wani daga cikin mayakansu mai mukamin  Captain ya halaka a Gaza, kuma tuni sun bude bincike akan abinda ya faru. Rahoton tashar talabijin din ” Cane” ta HKI ya ambaci cewa, sojan da aka kashe yana cikin wadanda su ka kai hari a garin Khan-Yunus a jiya Alhamis. Sojojin mamaya sun kai hari ne a cikin wani gida a ci gaba da kashe ‘yan gwgawarmaya da suke yi, sai dai ginin gidan ya rufta da su, bayan da nakiyar da take cikinsa ta fashe. Tun...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shi ma Shugaban Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Wadada, ya bayyana cewa wannan kyauta alama ce ta gaskiya da amincewa da ayyukan hukumar. Ya ce NPA ta nuna ƙwazo wajen bin ƙa’idojin lissafi da kuma tallafa wa hanyoyin bayyana gaskiya a ayyukan gwamnati. Shugaban NPA, Dr. Abubakar Dantosho, wanda ya karɓi kyautar a madadin hukumar, ya sake tabbatar da ƙudirinsa na yin gyare-gyare da kuma tabbatar da gaskiya a dukkanin ayyukan hukumar. Dr. Dantosho ya ƙara da cewa yin adalci da riƙon amana wajen harkokin kuɗi na daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke da niyya a ƙarƙashin shirin “Renewed Hope”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    An kaddamar da shirin koyar da Sinanci mai taken “Hello China”, na gidan rediyon Nijeriya (FRCN), a Abuja babban birnin kasar. Kusan mutane 100, ciki har da jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai da darakta janar na FRCN Mohammed Bulama ne suka halarci bikin kaddamarwar da ya gudana a jiya Alhamis. Cikin jawabin da ya gabatar, Yu Dunhai ya ce kaddamar da shirin na koyar da Sinanci da gidan rediyon ya yi, zai samar wa ‘yan Nijeriya wani sabon dandali na koyon harshen Sinanci da fahimtar kasar Sin, tare da samar da kuzari mai dorewa ga hadin gwiwar moriyar juna a fannonin cinikayya da tattalin arzikin tsakanin Sin da Nijeriya Daga ranar 16 ga wata ne za a fara watsa...
    Ministar Raya Al’adu, Hannatu Musawa, ta ce ya kamata shugabancin ƙasar nan ya ci gaba da kasancewa a hannun ’yan Kudu domin a samu adalci da daidaito. Ko da yake kundin tsarin mulkin Najeriya bai tilasta tsarin karɓa-karɓa ba, manyan jam’iyyun siyasa suna bin tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu. An tsare mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote A wata hira da ta yi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Hannatu Musawa ta ce tun da an samu Shugaba daga Arewa (Muhammadu Buhari) na tsawon shekaru takwas, to ya dace yanzu kuma a bar ’yan Kudu...
    Taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adama, wanda aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga watan nan, mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya”, ya ja hankalin baki daga kasashe da yankuna 140 da suka hada da ‘yan siyasa da ministocin gwamnatoci da kuma wakilan bangarori daban daban, inda suka yi musayar ra’ayin tare da cimma matsaya a fannoni da yawa, da kuma fitar da sanarwar Beijing, bayan kammala taron. Sanarwar ta bayyana cewa, mu’amalar wayewar kai muhimmin karfi ne wajen inganta ci gaban wayewar kan bil’adama da bunkasuwar zaman lafiyar duniya. Kuma ya kamata kasashe da kabilu daban-daban su...
    Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari. Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar. Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki Mutanen da aka kashe suna cikin wata motar haya da ta taso daga Basawa a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna. Baƙin suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kwa a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure. Wasu ɓata-gari ne suka...
    Amurka ta bayyana dalilin sabunta manufofin, tare da lura da cewa “an tsara sharuddan bizar Amurka da ka’idoji domin kare tsarin shige da fice na Amurka.” Ofishin jakadancin ya kara da cewa “wadannan ka’idoji sun dogara ne kan ma’aunin fasaha da tsaro na duniya.” A cewar ofishin jakadancin Amurka yana aiki tare da hukumomin Nijeriya domin cimma wadannan matakan. Sanarwar ta ce “Tawagar Amurka tana aiki tare da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da cewa Nijeriya za ta iya cika sharuddan.” Misalin wannan sabon tsari ya hada da “Takardun tafiye-tafiye masu aminci: tabbatar da cewa kasashe suna ba da amintattun takaddun balaguro tare da ingantattun bayanan matafiyi, Kada aikin gudanar da Bisa ya wuce lokacin da aka dauka:.” Duk da sabbin...
    Kididdigar ta nuna cewa maimakon amfani da wannan kudaden shigar don rage basussuka, wasu jihohi suna kara amso bashin. Jihar Ribas ta zama ta farko a jerin jihohin da adadin bashin cikin gida na naira biliyan 364.39 a wata uku na farkon 2025, mafi girma tsakanin jihohi 10. Basukan Jihar Inugu sun tashi daga naira biliyan 82.48 a farkon wata uku na 2024 zuwa naira biliyan 188.42 a farkon wata uku na 2025, wanda ke nuna karuwa na naira biliyan 105.95 ko kashi 128.4 cikin dari. Jihar Neja ta biyo baya da karuwar naira biliyan 57.68 a kowanne shekara, daga naira biliyan 86.07 zuwa naira biliyan 143.75, wanda shi ne karuwa na kashi 67 cikin 100. Jihar Taraba ta nunka...
    Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari. Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar. Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki Mutanen da aka kashe suna cikin wata motar haya da ta taso daga Basawa a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna. Baƙin suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kwa a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure. Wasu ɓata-gari ne suka...
    Ɗangote Ya ƙara da cewa “A yau, bayan kashe sama da dalar Amurka biliyan 18 wajen gudanarwa tare da gyara matatun man har yanzu basa aiki. Kuma bana tunanin nan gaba za su iya ci gaba da aiki. Ƙoƙarin zamanantar da su kamar misalin zamanantar da tsohuwar motar da ta yi shekara 40 ne, ko an canja inji ba zai sa ta koma dai-dai da ta zamani ba”. Alhaji Aliko Ɗangote ya ce ya yanke shawarar gina matatar man fetur ne mai fitar da ganga dubu ɗari shida da hamsin a rana bayan da marigayi Umaru Musa Yar’adua ya yanke shawarar ƙin siyar masa da matatun man fetur ɗin ƙasar nan. Sabuwar matatar man fetur ta Ɗangote ana saran za...
    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce yana da shakku a kan ko matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya za su ƙara aiki a nan gaba. Najeriya dai na da matatun mai guda hudu mallakinta a biranen Fatakwal da Warri da Kaduna. Amma attajirin ya ce matatun man waɗanda ke ƙarƙashin kulawar Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), sun laƙume sama da Dalar Amurka biliyan 18 wajen gyaransu, amma har yanzu sun ƙi aiki. Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC Ɗangote ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin shugabannin kamfanoni wadanda ke Karatu a Lagos...
    “A wajen jahilai, tsagaggen lebe lahani ne a kan makogwaro da lebe, amma idan akwai shinge tsakanin hanci da baki, ana kiran sa da suna handa. Wani abu ne da ba a san abin da yake kawo shi ba, amma kuma ana danganta shi da abubuwa da dama kamar karancin rashin sinadarin bitamin B.” “Don haka, muna shawartar mata masu juna biyu da su mayar da hankali wajen yawan zuwa awon ciki, sannan kuma su rika shan magungunan da ake ba su na yau da kullum, ta yadda za a rage haihuwar masu dauke da wannan cuta. “Hakika wannan babban abin takaici ne a cikin al’umma, shi yasa kwararrun likitoci, ma’aikatan jinya, jami’an jin dadin al’umma da likitocin makogwaro, hanci...
    “An tsara kungiyar ne domin hada kan Arewa da magance matsalar rashin aikin yi Wanda hakan ya sanya aka tattaro manyan hafsoshin soja da suka yi ritaya, da tsaffin gwamnoni, da masu rike da sarautun gargajiya, da masu fafutukar kare hakkin jama’a, da kungiyoyin matasa, da kwararrun a fannin ci gaban kasa wadanda da yawa daga cikinsu sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da mulki da kuma mayar da muradun Arewa saniyar ware a ‘yan shekarun nan”   “Yankin arewa na iya shawo kan kalubalen da suke fuskanta ta hanyar hadin kai da kuma sabunta kudurin samar da ci gaba,”   Bafarawa ya kuma tabbatar da cewa ba an kafa kungiyar bace a matsayin dandalin siyasa ba, kuma...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da umarninsa ga sabbin kwamandojin da kansu a lokacin yakin baya-bayan nan Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, yayin da yake ishara da umarnin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar a yakin kwanaki 12 da aka kakabawa Iran, ya ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kasance a dakin kwamandoji sau biyu a lokacin yakin tare da bayar da umarninsa ga sabbin kwamandojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A wata hira da aka yi da shi ta gidan telebijin, Qalibaf ya kara da cewa kwamandojin da aka nada sa’o’i bayan fara kai hare-hare kan kasar Iran,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi tsokaci kan takunkumin Amurka ta kakaba kan jami’ar Majalisar Dinkin Duniya da cewa: Ba za a iya murkushe gaskiya ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi tsokaci kan takunkumin da Amurka ta kakaba wa wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese. A cikin wani rubutu a dandalin “X” a ranar Juma’a, Baqa’i ya bayyana cewa: “Ba za a iya murkushe gaskiya ba.” Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu,  Francesca Albanese, ta fuskanci takunkumi da girman kai saboda fallasa gaskiya da kuma tsayin...
    Mataimakin shugaban kasar na farko ya jaddada cewa: Kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Iran Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: kalmar mika wuya ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron kasar. Arif ya ce: Kamar yadda kuke gani kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa, su mutane ne masu wayewa, tare da ingantaccen tarihin al’adu wanda ya wuce dubban shekaru. Ba su neman yaki, kuma ba su fara shi ba. Sun yi imani da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma a shirye suke don tattaunawa, amma ba za su mika wuya a...
      A daya bangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; wadannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma hadari duk da ke dauke cikin wannan labari. Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna...
    Albarkacin taron ministocin kasa da kasa na tattauna mu’ammalar wayewar kai ta duniya, CGTN ta hada hannu da jami’ar Renmin ta kasar Sin, domin jin ra’ayin al’ummun kasashe 41 da yawansu ya kai dubu 12. Masu bayyana ra’ayoyin na ganin cewa, mu’ammala, da cudanyar al’adu, da wayewar kai muhimmin karfi ne na ciyar da bunkasar wayewar kan daukacin bil’adama da zaman lafiyar duniya gaba, don haka ne ma darajanta al’adu da magabata suke dora muhimmanci a kanmu, da kirkire-kirkire, na da babbar ma’ana ga zamanantar da al’ummun bil’adama, wanda hakan ya sa shawarar bunkasa al’adun duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta samu karbuwa tsakanin sassan kasashe daban-daban, yayin da suke kokarin tinkarar kalubaloli a duniya. Yayin da aka tabo...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matasan Najeriya da dama suna son yin arziki amma ba tare da sun sha wahala ba.   Sau da yawa matasa sun fi neman hanya mafi sauki da za ta basu arziki ba tare da sun sha wahala ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa bin yanke don tara abin duniya. Domin sauke shirin, latsa nan  
    shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibof ya bayyana cewa asarorin da HKI ta yi a yakin kwanaki 12 da JMI suna da yawa. Kuma babu shakka ya fi abinda ta bayyana. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a lokacinda yake hira da wata tashar talabijin a nan Tehran . Ya kuma kara da cewa. Maganar cewa uahudawa 3500 kawai suka ji rauni a yakim gaba daya karya ce. Qalibof ya ce yana da tabbacin cewa yahudawa akalla 500 suna halaka sanadiyyar hare-haren da sojojin Iran suka kai a kan HKI a yankin kwamaki 12. . Ya ce sojojin yahudawan sun saba boye yawan mutanen...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar tattaunawa da Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya a bude take, amma kafin haka sai gwamnatin kasar Amurka ta biya diyyar kura kuran da ta yi a bayan. A wata hirar da yayi da Jaridar Le Monde na kasar Faransa Aragchi ya kara da cewa da farko Amurka yakamata ta canza halayenta, na rashin kaiwa kasar Iran hare-hare a lokacin tattaunawa. Ya ce diblomasiyya hanyace mai tituna biyu na zuwa da komawa, amma Trump ya zo ya rufe dayar.  Kuma tattaunawar diblomasiyya a wajen Iran a ko yauce a bude yake, Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Iran a cikin yakin kwanaki 12 keta hurumin diblomasiyya...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya fadawa shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa, kan cewa huldar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA zai kasance tare da sharudda. Saboda hukumar ta yi watsi da ayyukanta na asali ta koma siyasa. Ta fita daga bangaren kwararru ta zama tana bin bukatun wasu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar ta IAEA a da can ta zuciya guda ce, bata boyewa hukumar wani abu a cikin ayyukanta na makamashin Nukliya. Amma a halin yanzu mun gano cewa hukumar ce take bawa HKI bayanai dangane da ayyukammu na Nikliya ta kuma bada sunaye dadireshin masana fasahar Nukliya na kasar HKI ta zo ta kashesu...
    Rahotanni na cewa ’yan fashin daji masu yawan gaske ne aka tabbatar da kashewa a wani kwanton ɓauna da sojoji suka yi musu a ranar Laraba a jihohin Zamfara da Kebbi. Sojojin ƙasa da na sama sun yi amfanin da bayanan sirri wajen buɗe wuta kan ayarin ’yan fashin da ke kan ɗaruruwan babura suna zirga-zirga a yankin Yarbuga da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara. Kakakin Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Alhamis, inda ya ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun rika kokarin guduwa a kafa da kuma kan baburan, amma sojojin suka ci gaba da yi musu ruwan wuta ta ko ina. Muna so a...
    Ƙwallon da Chinwendu Ihezuo ta zura a minti na 89 ya isa ya kai babbar tawagar mata ta Nijeriya da akeyiwa lakabi da Super Falcons zuwa matakin Kwata Fainal na gasar cin kofin Afrika ta mata da hukumar CAF ke shiryawa ta shekarar 2025, Super Falcons ta doke kasar Botswana da ci 1-0 a wasan da suka buga yau Alhamis da karfe 8 na dare agogon Nijeriya a Casablanca. A fafatawar da aka yi a filin wasa na Stade Larbi Zaouli, Ihezuo ce gwarzuwar wasan, sakamakon kwallo daya tilo da ta jefa a ragar kasar Botswana dake Kudancin Afirika, Nijeriya ta lallasa Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga, duk da cewa an tafi hutun rabin lokaci...
    Mataimakin babban magatakardan MDD, kana sakataren zartarwa na kwamitin tattalin arzikin Afirka Claver Gatete, ya bayyana cewa, kasar Sin aminiya ce da kasashen Afirka za su iya dogaro da ita. Gatete ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da ya karbi takardar wakilcin kasa daga sabon wakilin kasar Sin a kwamitin tattalin arzikin Afirka na MDD, kana shugaban tawagar jakadun kasar Sin dake kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Jiang Feng a birnin Addis Ababan kasar Habasha, mazaunin kwamitin na tattalin arzikin Afirka na MDD. A yayin ganawarsu, Claver Gatete ya taya Jiang Feng murnar gudanar da sabbin ayyuka, ya kuma yi fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, domin ba da taimako ga bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya ta buƙaci Majalisar Tarayyar da ta amince da ƙudirin dokar da zai ba ta damar bincikar ɗaiɗaikun ’yan Najeriya game da yadda suka tara dukiyarsu. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito Shugaban EFCC, Ola Olukayode yana cewa ƙudirin mai suna “Unexplained Wealth Bill” ya je gaban ’yan majalisar tun a majalisa ta tara, wanda suka yi watsi da shi. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba “Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɓarnar da ake yi arzikin ƙasarmu da kuma matsalar tsaro,” a cewarsa yayin wani taro da kwamatocin majalisar...
    Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 24 a wasu sabbin hare-hare da suka ƙaddamar a maɓoyar ’yan ta’addan a yankunan daban-daban a Arewa maso Gabashin Nijeriya. Kwamandan haɗakar rundunar Operation Haɗin Kai a Arewa Maso Gabas, Janar Abdulsalam Abubakar ya ce an kai samamen ne bayan tattara bayanan sirri. A cewarsa, an kuma kashe mutum biyar da suke samar wa ’yan ta’addan kayayyakin amfani, a wani kwanton ɓauna da aka yi musu da daddare. An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu An gudanar da waɗannan ayyuka ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Yuli a...
    An tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, tare da ƙona gidaje sama da 100, wanda ake zargin wasu makiyaya ne a unguwannin manoma da ke Ƙaramar hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba suka yi. An kai wa mazauna unguwar Bandawa Gwenzu, waɗanda suka haɗa da: Gwenzu da Langwanshin da Danzhan hari a daren Laraba. Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno Da yake magana da tashar Talabijin na Channels TV ta wayar tarho a ranar Alhamis, shugaban matasan Uunguwar yankin, Ishaya Peter ne ya bayyana harin a matsayin rashin gaskiya da abu mai muni kuma ya yi Allah-wadai da harin. A cewarsa, mazauna garin na zaune suna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban yahudawan Iran Rabbi Younes Hamami Lalezar ya  ce, Isra’ila tana amfani da addini yahudanci domin cimma manufofinta, tana kuma bayyana Iran a matsayin wacce take fada da addinin yahudanci,alhali a cikin iran da akwai zaman lafiya tsakanin Mabiya dukkanin addinai. Haka nan kuma ya ce, kiyayyar da Isra’ila take da shi akan Iran ne, yake sa take jinginawa Iran din kin jinin yahduawa,wanda aikin ‘yan sahayoniya ne su samar da rabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Iran bisa addini da kuma kabila. Isra’ila tana bayyana kanta a matsayin mai bai wa yahudawa kariya, sai dai  da dama daga cikin Mabiya addinin yahudanci, wadanda ba ‘yan sahayoniya ba, suna zarginta da amfani da addini saboda manufofi na siyasa. Fiye da  shekaru ...
    Sojojin Sahayoniya suna ci gaba da yi wa mutane Gaza kisan kiyashi a kwana na 643 a jere. Sojojin sahayoniyar suna amfani da dukkanin kayan yaki da su ka hada jiragen masa masu matuki da marasa matuki, da kuma manyan bindigogi. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare da tankokin yaki bayan kutsawarsu cikin yankin “Bi’irut-Turki” da “maslakh” dake kudancin Khan-Yunus. Tankokin sun rika bude wuta akan mai uwa da wabi da gidajen mutane a cikin yankin, da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da yawa.” Majiyar Falasdinawa ta tabbatar da shahadar mutane 16, da su ka hada mata da kananan yara a wuruin da suke jiran karbar abincin agaji a shataletalen al-Dhayyarah,...
    Kungiyar al-shabab mai alaka da alka’ida ta kai harin kunar bakin wake a wani barikin soja da yake birnin Magadishu a jiya Laraba da marece. Shaidun ganin ido sun ce, harin ya yi kara mai tsanani wacce ta girgiza babban birnin kasar Magadishu, sannan kuma harbe-harbe su ka biyo baya. Kungiyar al-shabab mai alaka da alka’ida ce ta dauki alhakin kai harin. Sai dai kuma babu wani cikakken bayani akan ko harin ya yi sanadin jikkata ko rasa rayuka. Ita dai kungiyar al-shabab ta dade tana kai hare-hare a cikin kasar Somalia da hakan ya sa gwamnatin kasar take daukar ta a matsayin kungiyar ta’addanci. A shekarar 2023 ma dai kungiyar ta al-shabab ta kai wani harin kunar bakin wake...
      Ganin irin yawan kalubalen tattalin arziki da siyasa a Arewacin kasan nan ya sanya Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya kaddamar da wata sabuwar kungiya mai taken Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative.   An kaddamar da wannan kungiyoyi ce a wajen wani babban taro da aka gudanar a Arewa House, Kaduna, inda manyan baki da mahalarta daga sassa daban-daban na Arewa suka halarta.   A yayin taron, Bafarawa wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na tafiyar, ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon hanyar da za ta yi maganin baraka da inganta fahimtar juna da kuma karfafa ci gaban mai dorewa a yankin Arewa.   Ya ce Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da...
    A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adam. A cikin sakonsa, Xi ya jadadda niyyar Sin na hadin gwiwa da kasashe daban-daban, don tabbatar da shawarar raya wayewar kan duniya bisa tushen adalci, da koyi da juna, da mu’ammala da yin hakuri da juna, ta yadda za a kafa nagartaccen tsarin mu’amalar wayewar kan bil Adam a duniya, matakin da zai gaggauta bunkasa wayewar kan bil Adam, da bunkasar duniya cikin lumana. Shugaba Xi ya kuma yi fatan mahalarta taron za su zurfafa mu’amala, da cimma matsaya daya, da taka rawar ganin wajen karfafa cudanyar al’ummun kasa da kasa, da...
    A yau Alhamis, aka bude taron ministoci na dandalin tattaunawa game da wayewar kai a duniya a birnin Beijing, inda aka mayar da hankali kan muhimmancin mabanbantan al’adu da fahimtar juna wajen samun ci gaban harkokin dan Adam. Taron na yini biyu mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya” ya ja hankalin baki sama da 600 daga kasashe da yankuna 140. Yayin wasu kananan taruka da za su gudana lokaci guda a karkashin dandalin, mahalarta za su lalubo muhimmiyar rawar da musayar al’adu daban-daban da fahimtar juna ka iya takawa ga ingiza dunkulalliyar duniya da inganta ci gaban duniyar da kwanciyar hankali da gadon al’adu da kirkire-kirkire da fahimta da abota...
    Ban da haka, bayan da aka tsara “shirin shekaru 5”, yana da muhimmanci a aiwatar da shi. A kasar Sin, bayan da aka gabatar da wani “shiri na shekaru 5”, dole ne a aiwatar da shi yadda ake bukata. Kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar za su tsara salon aiwatar da dukkan ayyuka, da raba su ga sassa da yankuna daban-daban, don a aiwatar da su a matakai daban daban. Bayan haka, hukumomi daban daban su kan gudanar da ayyukan sa ido a tsakiyar wa’adin shirin, kuma za a tantance ainihin sakamakon da aka samu bayan karewar shirin. Ta wadannan halayen musamman, za a iya ganin abubuwan da za su tabbatar da aiwatar da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun sojojin Nijeriya na rundunar sojojin sama tare da haɗin gwiwar Operation Haɗin Kai sun kai farmaki kan wasu muhimman wuraren da ’yan ta’adda suka mamaye a tsaunin Mandara da ke Jihar Borno. An samu labarin cewa rundunar sojin sama ta gudanar da samamen ta ne a wani wuri da aka san shi da tudu mai tsauni, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, bayan samun bayanan sirri. An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Daily Trust ta ruwaito cewa, samamen share fagen ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umurci sojoji da su kawar da...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa unguwar Qua da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato. ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Adadin waɗanda aka kashe mutum 32 da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara suna cikin...
    Wannan sabon birni na da ganuwa mai tsawon kilomita 8.5 da zai kare Legas daga ambaliyar ruwa, kuma yana da gidaje, ofisoshi da wuraren kasuwanci da na nishaɗi. Dangote ya ce wannan aiki yana daga cikin manyan abubuwan tarihin da Shugaba Tinubu zai bari. Hakazalika, ya nuna godiyarsa bisa fara aikin titin gaɓar teku daga Legas zuwa Kalaba da kuma aikin titin Sakkwato zuwa Badagry, waɗanda za su inganta sufuri da tattalin arziƙi a faɗin ƙasar. Ya kwatanta hangen nesan Tinubu da yadda ƙasar Netherlands ta kasance wajen samar da muhallai a cikin ruwa don raya birane. Dangote ya ƙara da cewa kamfaninsa na jin daɗin irin goyon bayan da gwamnati ke ba shi wajen sauƙaƙa kasuwanci da bunƙasa tattalin...
    Gwamna Malam Umar Namadi na Jihar Jigawa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na farfado da harkar kasuwanci mara shinge a Maigatari, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin ginshikin bunkasar tattalin arziki, kasuwanci da masana’antu a jihar. Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kwamandan Yankin K da Jigawa na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Kwamanda Dalhat Abubakar, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a Fadar Gwamnati da ke Dutse. Gwamna Namadi ya taya Kwamanda Abubakar murnar nadin nasa, tare da yaba wa hukumar Kwastam bisa goyon bayan manufofin cigaban jihar Jigawa, musamman wajen farfado da aikin Maigatari da aka yi watsi da shi. Ya nuna godiya bisa goyon bayan  Kwamandan ya bayar, tare da yabawa da rahotannin da ke...
    Ministan Tsaron Iran ya bayyana cewa: Hare-haren da Iran ta kai ne suka tilasta wa gwamnatin mamayar Isra’ila daukan matakin tsagaita bude wuta Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewa: Munanan hare-haren da sojojin kasar Iran suka kaddamar a matsayin mayar da martani ga yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita bude wuta. A wata tattaunawa ta wayar tarho guda biyu da ya yi da ministocin tsaron Venezuela da Armeniya, Birgediya Janar Nasirzadeh na rundunar sojin sama ya jaddada cewa: Hare-haren da sojojin Iran suka kaddamar kan yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita wuta. Ministan tsaron na Iran ya kara da cewa: Sojojin kasar Iran sun shirya tsaf domin mayar da martani ga...
    Kwamandan sojojin kasa na sojojin Iran ya jaddada wajabcin Karin daukan matakan kare iyakokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kwamandan sojojin kasa na kasar Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya jaddada wajibcin kare cikakken kan iyakokin kasar akida, al’adu, da yanki, yana mai cewa: Dole ne dukkanmu al\umma su zama masu kare wannan kasa da kuma samun kwarin gwiwa daga tafarkin shahidai. A yayin wata ganawa da iyalan shahidan kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyawa ta kakaba wa Iran a birnin Sarpol-e Zahab na lardin Kermanshah a ranar Larabar da ta gabata, Birgediya Janar Heidari ya bayyana cewa: Sojojin kasar suna kan gaba wajen kare ‘yancin kai da yankinsu na kasar, kuma a kodayaushe suna nuna godiya da irin hakurin da iyalan...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Mayar da martanin Iran ga ‘yan sahayoniyya sun murkushe girman kan makiya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Martanin da Iran ta mayar wa yahudawan sahayoniyya a lokacin arangamar da suka yi a baya-bayan nan abin nuni ne, domin kuwa a duk tsawon tarihin haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta taba samun irin wannan martanin mai gauni ba. Ghalibaf, wanda ya karbi bakwancin jakadan Belarus a birnin Tehran, Dmitry Kaltsov, a jiya Laraba, ya yaba da matakin da gwamnatin Belarus ta dauka dangane da hare-haren da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauika na kai wa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran hare-haren wuce gona da iri. Yana mai...
    Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya. A wata ganawa da iyalan shahidi Kanar Bostan Afrouz, Manjo Janar Hatami ya kara da cewa: Makiya sun kasa cimma tsare-tsare da shirye-shiryensu da suka rigaya sukaaniyar cimmawa, kuma sun fuskanci mummunar martani da shan kashi. Ya ci gaba da cewa: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya duk da karfin soja da kudi da suke da su, baya ga bayanan sirri da suke tabbatar...
    Ya ce: “Ba mu kai inda muke so ba a fannin tattalin arziki, amma muna iya gani cewa abubuwa suna tafiya a hankali. Shugaban Ƙasa ya faɗa sau da dama cewa mun fara fitowa daga ƙunci.   “Na san mutane da yawa za su ce ba mu kai ga cikakken cigaba da jin daɗin tattalin arziki ba tukuna. Gaskiya ne! Ni ma na yarda. Amma ba za mu ce babu cigaba ko kaɗan ba.”   Ya ƙara da cewa: “Ko hukumomin ƙididdiga na duniya suna fara ba Nijeriya kyakykyawan matsayi. Muna ganin alamu na ɗagawa a hanyar da ake tafiyar da tattalin arzikin mu.”   Idris ya ce manyan matakan sauyi kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar...
    Hadimin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi, ya mayar wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha martani, kan cewa Tinubu bai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba wajen zama shugaban ƙasa a 2015. Ajayi, ya ce Buhari yana da ƙarfi sosai a Arewa amma hakan bai hana shi faɗuwa zaɓukan 2003, 2007 da 2011 ba. Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Ya bayyana cewa a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi a 2014, Tinubu ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya lashe. Ya ce Tinubu ne ya shawo kan gwamnonin APC da...
    Ya kuma yaba wa Garba Shehu bisa rubuta littafin, yana mai cewa hulɗa da jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen tafiyar da mulki da kuma gina ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.   Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi  ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya. NAJERIYA A YAU: Sarƙaƙiyar da ke gaban Haɗakar ADC: Atiku ko Peter Obi DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata. Domin sauke shirin, latsa nan
    Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce ba Shugaban Kasa Bola Tinubu kaɗi ne ya sa Muhammadu Buhari ya ci zabensa a shekarar 2015 ba. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Abuja ranar Laraba, yayin kaddamar da littafin da mai magana da yawun tsohon Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya wallafa kan abubuwan da ya gani a zamanin mulkinsu. Buhari dai ya shugabanci Najeriya ne daga shekarar 2015 zuwa 2023. ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II Daga cikin manyan bakin da suka halarci kaddamar da littafin akwai tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Yakubu Gowon da tsohon Mataimakan Shugaban Kasa, Atiku Abubakar...
    Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, ciki har da ɗan sanda da ’yan sa-kai guda uku, a wani hari da ’yan bindiga suka kai garin Mongoro da ke Ƙaramar Hukumar Mariga, a Jihar Neja. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Laraba. Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II ’Yan ƙabilar Ibo ne suka fi aikata laifi a Jihar Anambra ba Fulani ba — Gwamna Soludo Mazauna garin Wamba, sun ce har yanzu suna cikin fargaba saboda ‘yan bindigar ba su bar yankin ba. A ranar 24 ga watan Yuni, maharan sun kai hari wani sansanin sojoji da ke Kwanan-Dutse, inda suka kashe sojoji 17, tare da jikkata wasu 10. A cewar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamana Charles Soludo na Jihar Anambra ya ce mafi rinjayen kaso na waɗanda jami’an tsaro ke kamawa da aikata laifuka tsawon shekara uku da suka gabata ’yan kabilar Ibo ne. BBC ya ruwaito Soludo yana bayyana hakan a yayin wani taro da ’yan asalin jihar mazauna ƙetare suka gudanar a Amurka. Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya Soludo wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne ya yi watsi da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya na aikata satar mutane a jihar. “Yanzu shekara uku da wata uku ke nan ina kan mulki. Idan muka kama masu laifi 100 to kashi 99 cikin 100 matasan ƙabilar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 30 a ƙauyukan Kadisau, Raudama, da Sabon Layi da ke Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina. Jami’an tsaron sun haɗa da ’yan sanda, sojoji, da rundunar sojin sama ta Najeriya. HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN Jami’an sun kai ɗauki ne bayan samun rahoton ’yan bindigar sun kai farmaki a lokaci guda a wurare daban-daban. Amma, ’yan sanda uku da sojoji biyu sun rasa rayukansu a yayin artabu da ’yan bindigar. Wani jami’in tsaro mai suna Ya’u Aliyu ya samu rauni. Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba. Ya...
    Game da koma bayan tattalin arziki da duniya ke fuskanta, ana matukar bukatar bullo da sabbin hanyoyin samun bunkasa. Shi ya sa, yin kirkire-kirkire da habaka hanyoyin samun bunkasa, ya zama mataki mafi jawo hankula daga cikin tsarin hadin gwiwar mambobin BRICS. Sin ta sanar a wannan taro cewa, za ta kafa cibiyar nazarin sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ta Sin da kasashen mambobin BRICS.   Kazalika, game da babakeren da Amurka ke nunawa, mambobin BRICS sun yi kira da a kiyaye ra’ayin kasancewar mabambantan bangarori a duniya da gaggauta kafa kyakkyawan tsari da dokar tattalin arziki da cinikin duniya mai adalci da bude kofa. Albarkacin cika shekaru 10 da kafuwar bankin NDB na BRICS, Sin...
    Tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgediya  Muhsin Rizai, ya sanar da cewa; Dakarun IRGC sun yi nasarar harbo jirage manya da marasa matuki na HKI har guda 80, kuma da akwai baraguzai 32 daga cikinsu da ake rike da su. Birgediya Rizai ya kuma kara da cewa; Daga cikin wadanda aka harbo din da akwai samfurin “Hermes” da “Hermon” da sune kira ta karshe da ‘yan sahayoniya suke takama da su. Birgediya Muhsin Rizai wanda memba ne a majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci ta Iran, wanda tashar talbijin ta yi hira da shi da marecen jiya Talata, ya yi Magana akan bangarori da dama na  kallafaffen yakin kwanaki 12 inda ya ce:” Gabanin mu yi...
    Shugaban kungiyar Kurdawa ta kasar Turkiya ( PKK) Abdullah Ojlan ya sanar da kawo karshen amfani da makamai a fafutukar da kungiyarsu take yi na kare hakkokinsu a kasar Turkiya. Shugaban kungiyar Kurdawan na Turkiya wanda yake tsare a kurkuku na shekaru masu tsawo, ya aiko da sako na bidiyo da a cikin ya ce; Har yanzu ina kan kiran da na yi a ranar 27 ga watan Febrairu  na ajiye makamai”. Ojlan ya kara da cewa; Muna sanar da kawo karshen amfani da makamai ne bisa radin kanmu, haka na kuma ya ce; Mun shiga Zangon aiki da doka da kuma siyasa da tsarin demokradiyya, wanda shi kanshi nasara ce mai dimbin tarihi ba asara ba.” Kuniyar PKK ta...
     Jaridar HKI ta “Haaretz'” ta buga labarin da yake cewa: A cikin wannan shekarar ta 2025, sojojinsu da su ka halaka sun kai 62. A cikin watannin bayan nan an sami karuwar sojojin mamayar da ‘yan gwgawarmaya suke kashewa a Gaza. Yankin Khan Yunus dake Arewacin Gaza da HKI take riya cewa ta nike shi, sannan kuma ta kori Falasdinawa daga cikinsa, yana daga cikin wuraren da aka yi wa sojojin mamayar kwanton bauna. Bugu da kari, har yanzu ‘yan gwgawarmayar suna ci gaba da harba makamai masu linzami daga Gaza zuwa matsugunan ‘yan share wuri zauna da suke kusa da Gaza. A jiya ma dakarun “Sarayal-Quds” na kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da harba makamai masu linzami zuwa  matsugunan da...
    Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ziyarci iyalin marigayi, Alhaji Aminu Dantata a Jihar Kano, don yi musu ta’aziyya. Obi, ya bayyana cewa ya yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar Alhaji Ɗantata, inda ya bayyana shi a matsayin “uba ga kowa.” An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN 2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo Ya yaba yadda Ɗantata ya zama babban attajiri kuma ya taimaka wa mutane da dama suka samu nasara a rayuwarsu. Ya ce Ɗantata ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya. “Mun zo nan yau don jimami tare da iyalinsa da kuma ɗaukacin ‘yan Najeriya, saboda...
    Sanarwar ta ƙara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga ƙarananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin kuɗaɗen garatuti. Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen daidaita biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati, musamman waɗanda suka yi ritaya bayan shekaru 35 suna aiki kuma suka kai shekaru 60.   “Gwamnatinmu ta gaji sama da Naira Biliyan 13 a matsayin bashin kuɗaɗen garatuti na waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomin daga 2011 zuwa 2023, jinkirin ya jawo wahalhalu, kuma wasu da suka yi ritaya sun mutu su na...
    Karuwar tasirin da kasar Sin ke yi a fagen ci gaban kimiyya da fasaha a duniya ba barazana ba ce, sai dai wata dama ce ta kawo ci gaba mai gamewa. Diamond ya kara da cewa, “Kasancewar na yi aiki kafada da kafada da wasu jami’o’i da cibiyoyin kasar Sin na tsawon shekaru masu yawa, na yi amanna da yadda kasar Sin ta dukufa ga samar da kimiyya da fasaha mai bude kofa ga duk duniya bisa adalci.” Kazalika, masanin kimiyya, mamba a makarantar nazarin kimiyya da fasaha ta Afirka, Farfesa Felix Dapare Dakora, ya nuna yadda kasar Sin ke karfafa shigar kasashe masu tasowa cikin harkokin kimiyya a duniya. Yana mai cewa, “A halin yanzu, an gode da samuwar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan Sin Li Qiang ya bayyana a yau Laraba cewa, a matsayinsu na muhimman membobin kasashe masu tasowa, ya kamata Sin da Masar su karfafa hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare, domin kare muradunsu na bai daya. Li Qiang ya bayyana haka ne bayan isarsa birnin Alkahira, a ziyarar aiki da yake yi a kasar bisa gayyatar takwaransa na Masar din, Mostafa Kamal Madbouly. Firaministan Masar da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar ne suka tarbi Li Qiang tare da shirya biki domin yi masa maraba. Kafin isarsa, Li Qiang ya halarci taron kungiyar BRICS karo na 17 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ta ƙara sanya wa ’yan Najeriya da ke son ziyartar Dubai sabbin sharuɗa. Haka kuma, ta dakatar da bayar da bizar wucin gadi ga ’yan Najeriya. Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Aminiya ta samu labarin cewa hukumomin shige da fice na Dubai ne suka bayar da umarnin sabbin matakan ga ofishin jakadancin ƙasar da ke Najeriya. Daga cikin sabbin dokokin, duk ɗan Najeriyar da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 45 ba zai samu bizar yawon buɗe ido ba sai idan zai yi tafiya tare da wani. Wannan na nufin cewa yawan ’yan Najeriya...
    Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce akwai yara akalla miliyan biyar da dubu 400 da ke fama da matsalar karancin abinci a jihohi tara na arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro. A cewar kungiyar, jihohin su ne‎ Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, Zamfara, Neja, Binuwai da kuma Kano. Mai rikon mukamin Darktan Lafiya da Kula na kungiyar Dr Aminu Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a yayin taron gangamin neman tallafi kan karancin abinci na kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma da ya gudanar a Kano ranar Talata. Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sanar da cewa: Iran ba ta gabatar da wata bukatu na ganawa ga bangaren Amurka ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta kalaman shugaban Amurka dangane da muradin Iran na gudanar da tattaunawa, yana mai jaddada cewa: A bangaren Iran ba a gabatar da wata bukata ta yin wata ganawa da bangaren Amurka ba. Da yake mayar da martani ga kalaman Donald Trump, Ismail Baqa’i ya ce: Iran tana musanta abin da Trump ya fada game da bukatar Iran na gudanar da tattaunawa, kuma ba ta gabatar da wata bukata ta ganawa da Amurkawa ba. Yayin ganawarsa da Fira ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu da yammacin ranar Litinin, Trump ya yi ikirarin cewa an...
    Shi ma Uban taro mai masaukin baki, shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana a jawabinsa na taron kolin cewa, “Idan har ba a samu sauyi a tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa a wannan karni na 21 ba, to ya zama wajibi kasashen BRICS su taimaka wajen ganin an sabunta shi.” BRICS taska ce ta hadin kai, daidaito da kuma kokarin tafiya tare don samun ci gaba da tsira tare, da kuma karfafawa kasashe masu neman ‘yancin fadin albarkacin bakinsu a harkokin tsare-tsare na hadin kan kasashen duniya. Taron kolin kungiyar na bana, na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwannin duniya ke cike da firgici biyo bayan yakin cinikayya da kasar Amurka ta kaddamar,...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki. Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a...
    Shugaban Majalisar Kolin siyasar kasar Yemen ya jaddada ‘yancin kowa da kowa wajen gudanar da zirga-zirga a teku in banda makiya ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen, Field Marshal Mahdi al-Mashat, ya jaddada aniyar kasar ta Yemen na ba da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa ga kowa da kowa in banda makiya yahudawan sahayoniyya da kuma masu goya musu baya a lokacin da suke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza. A cikin wata sanarwa da Al-Mashat ya fitar ya ce: Ba su da wani sha’awar kai hari ga duk wanda ba shi da alaka da goyon bayan makiya yahudawan sahayoniyya, yana mai kira ga dukkanin kamfanonin jiragen ruwa da su...
    Ministan Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen sake kara kudin wutar lantarki domin rage yawan bashin da bangaren lantarkin ke bi. Bayanai dai sun nuna yanzu haka, bashin lantarkin da ake bi a Najeriya ya haura Naira tiriliyan hudu. Amma a cewar ministan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki 300 a Abuja, yunkurin wani bangare ne na tabbatar da cewa bangaren lantarki ya tsaya da kafarsa. Matar tsohon Gwamnan Adamawa ta sauya sheka daga PDP zuwa ADC Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda Idan dai za a iya tunawa, duk da Karin kudin wutar da aka yi wa kwastomomin da ke tsarin Band A,...
      Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan.   Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a Zaria, inda ya nuna alhini da ta’aziyya ga dangin waɗanda wannan al’amari ya shafa.   Tsohon Akanta Janar na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Kajuru, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na kashe...
    Jam’iyyar ADC ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu shugabanni daga yankin Kudu sun buƙaci Atiku Abubakar, da ka da ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan labari ƙarya ne, wanda aka ƙirƙira don haddasa rikici , musamman a wannan lokaci da ake ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya. Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense Jam’iyyar ta ce: “Ba mu taɓa zama da wasu wakilai daga Kudu domin yin irin wannan magana ba. “Wannan rahoto ba kawai ƙarya ba ne, yana kuma...
    Matar tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Zainab Boni Haruna, ta fice daga tsohuwar jam’iyyarta ta PDP zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. Zainab, wacce asalinta ta fito ne daga karamar hukumar Nangere a Jihar Yobe ta bayyana haka ne a wani taro da mata magoya bayan jam’iyyar ta ADC da aka gudanar a Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe. Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda Zainab Boni ta kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Tinubu kan rashin tsaro, wahalhalu, cin hanci da rashawa da kuma rashin shugabanci na gari a kasar nan. “Mutane suna shan...
    Amma yanzu, sabon tsarin ya rage wa’adin bizar zuwa wata uku kacal, kuma mutum zai iya shiga sau ɗaya ne kawai da ita. Ma’aikatar ta ce wannan mataki yana daga cikin gyaran tsarin alaƙar diflomasiyya da tsaro da Amurka ke yi da sauran ƙasashe. Sai dai ta bayyana cewa za a iya sauya wannan tsari a nan gaba, idan an samu canji a dangantakar diflomasiyya, tsaro ko dokokin shiga ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan ya janyo tambayoyi kan ko za ta iya komawa nan take. A lokacin da aka tambaye ta me take yi a lokacin da aka dakatar da ita, Sanata Natasha ta ce ba ta tsaya ba, har yanzu tana gudanar da ayyuka tare da wakiltar mutanenta. “Na kasance ina aiki a duk lokacin. Na ci gaba da aiki kuma ina shirin gabatar da wasu dokoki a kan ma’adanai. Ba zan iya miƙa su ga wani ba,” in ji ta. Ta ƙara da cewa duk da cewa ba ta halartar zaman majalisa, ta ci gaba da yin ayyukan ci gaba ga mutanenta. “Fitar da ni daga majalisa ba kawai ni aka daƙile ba, an hana muryar Kogi ta Tsakiya fitowa fili,”...
    Gwamnan jihar Texas ta Amurka ya ce sama da mutane 160 ne har yanzu ba a gano ba sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Juma’ar da ta gabata. Greg Abbott ya ce wannan adadi na lardin Kerr ne kaɗai, ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya fi muni. Hukumomi dai sun bayar da rahoton mutuwar fiye da mutum 100. Masu aikin ceto na aiki a sannu a ƙoƙarin kawar da tarkacen da ruwan ya janyo domin gano ko akwai mutanen da ke maƙale a ƙarƙashinsu musamman a yankin gaɓar kogin Guadalupe. A jihar New Mexico da ke makwabtaka da Texas, ruwa ya tafi da wani gida inda wani uba ke zaune da ‘ya’yansa biyu a yankin Ruidoso, kuma...
    Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Ilorin ta kai wa daliban makaranta yakin da ta yi da cin hanci da rashawa domin fadakar da su illar cin hanci da rashawa.   Da yake jawabi ga dalibai a makarantar Nursery da Primary School, Tanke, Ilorin, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a, Daraktan Hukumar EFCC, Ayodele Babatunde, ya ilmantar da daliban a kan ma’anar cin hanci da rashawa, daban-daban da illolinsa da yadda kowa da kowa, ciki har da yara, za su iya bayar da tasu gudunmuwar wajen gina Nijeriya mara cin hanci da rashawa.   Ya ce cin hanci da rashawa yana yin abin da bai dace ba ne, musamman idan ya shafi wasu...
    Kungiyar Kano Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (Kano-ACReSAL) ta kaddamar da yakin neman ilimin sauyin yanayi zuwa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ’Yan Mata da ke Kano a wani bangare na shirinta na “Catch Them Young”. Wato Ilmantar da Matasa.   Gangamin wayar da kan jama’a wani bangare ne na kashi na biyu na yunkurin aikin na jawo dalibai, malamai, da kwararrun muhalli wajen tattaunawa kan sauyin yanayi da kuma shigar da matasa wajen magance shi.   Mukaddashin mai kula da ayyukan, Dr. Abdulhamid Bala, ya sanar da daliban cewa sauyin yanayi ya kasance babban kalubalen da ba za a yi watsi da shi ba.     “Sauyin yanayi ya kasance barazana mai dorewa ga dorewar duniya. Amsarmu dole ne...
    Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Kukah Centre ta ce ta kuduri aniyar horar da jami’an tsaro a jihohin Sokoto, Kaduna da Benue.   Daraktan Cibiyar Kukah Reverend Father Atta Barkindo, wanda ya bayyana hakan ya ce an dauki matakin ne domin taimakawa kokarin gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar al’ummar kasar.   Reverend Father Atta Barkindo, ya jaddada cewa an shirya horon ne domin inganta tsaro a tsakanin al’umma a cikin dimbin kalubalen da jihohi da dama ke fama da su a fadin kasar nan.   Ya kuma bayyana bukatar kafa jami’an tsaro na Jihohi su samar da ingantattun tsare-tsare don tabbatar da samar da ayyuka masu inganci.   Shima da yake...
    An kaddamar da jam’iyyar African Democratic Party, ADC a Gombe mako guda bayan wasu jiga-jigan ‘yan adawa sun hada kai cikin jam’iyyar.   Shugaban jam’iyyar ADC a jihar Gombe kuma tsohon ministan sufuri Alh. Idris Abdullahi, ya ce makasudin shiga jam’iyyar shi ne ceto kasar nan daga kangin tattalin arziki da dora ta kan turbar ci gaba.   A cewarsa gamayyar jam’iyyun adawa sun zabi jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyya daya tilo da za ta samar da hanyar kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.   Sanata Idris Abdullahi ya jaddada kudirin kungiyar a Gombe na ci gaba da kasancewa da hadin kai domin cimma burin ta.   Shugaban jam’iyyar ADC na jihar Gombe Alh. Auwal Barde ya ce...
    Na Biya Bashin Garatutin Naira Biliyan 13.6 Da ’Yan Fanshon Zamfara Ke Bi Tun 2011, Inji Gwamna Lawal Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana jin daɗinsa na biyan bashin Naira Biliyan 13,944,039,204.64 da aka riƙe wa ’yan fansho a Zamfara tun daga shekarar 2011 zuwa 2023. A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho tare da karbar rahoto daga kwamitocin haɗin gwiwa kan biyan bashin kuɗaɗen garatuti da aka yi a gidan gwamnati da ke Gusau. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, warware tarin bashin kuɗaɗen guratuti da fansho da aka tara daga shekarar 2011 zuwa 2023 na ɗaya...
    Masu kwacen da aka fi san da ’yan ‘One Chance’, sun kashe Freda Arnong, wata ma’aikaciya a ofishin jakadancin kasar Ghana da ke babban birnin tarayya Abuja. Bayanai sun nuna matar, wacce daga bisani ta mutu a asibitin kasa da ke Abuja, ta hau motar da ake zargin ta masu kwacen ce a bisa rashin sani. Wata majiya daga jami’an tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa Freda ta hau motar ta tasi ne daga marabar otal din Transcorp a makon da ya gabata. Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda ‘Abin da zai sa APC ba za ta taɓa mantawa da Ganduje ba’ Majiyar ta ce a lokacin da matar ta shiga,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin Amurka da JMI sun lalace ne saboda zagon kasar HKI da farwa kasar da yaki. Yace gwamnatin Amurka idan tana so zata farfado da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a wani rubutun da yi wa jaridar ‘Financial Times ta Amurka. Inda y ace : Har yanzun JMI tana bukatar hanyar Diblomasiyya, amma kuma hakkinta ne mu yi shakku a kan ninyar Amurka niyyar Amurka a tattaunawa da ita. Idan Amurka da gaske take ta nuna cewa ta warware wannan matsalar to tana iya yin haka da adalci. Sai dai, inji ministan, yakamata Amurka ta san cewa al-amura sun sauya...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin Amurka da JMI sun lalace ne saboda zagon kasar HKI da farwa kasar da yaki. Yace gwamnatin Amurka idan tana so zata farfado da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a wani rubutun da yi wa jaridar ‘Financial Times ta Amurka. Inda y ace : Har yanzun JMI tana bukatar hanyar Diblomasiyya, amma kuma hakkinta ne mu yi shakku a kan ninyar Amurka niyyar Amurka a tattaunawa da ita. Idan Amurka da gaske take ta nuna cewa ta warware wannan matsalar to tana iya yin haka da adalci. Sai dai, inji ministan, yakamata Amurka ta san cewa al-amura sun sauya...
    Tsohon babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci wato IRGC ya bayyana cewa a yakin da JMI ta fafata a cikin watan da ya gabata , ya tabbata cewa JMI tana iya yaki da Amurka da HKI a lokaci guda. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Mohsen Rezaei, yana fadar haka a lokacinda wata talabijin ta cikin gida take hira da shi a jiya Talata . Labarin ya kara da cewa Janar Rezaei ya taba rike mukamin babban kwamandar rundunar IRGC jim kadan bayan nasarar juyin juya halin musulunci a shekara 1979. Yace: Shahid Janar Qasem Sulaimani, Babban kwamandan rundunar Qudus ne  ya fara furta zancen cewa , Iran tana da karfin fuskantar Amurka....
    Babban sakataren kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya godewa shugabancin JMI, wato Imam Sayyif Aliyul Khaminaei kan goyon bayan da yake bawa kungiyar babu kakkautawa don yakar makiyar kasar HKI. Shugaban kungiyar ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon, a karon farko tun bayan shahadr shugaban kungiyar Sayyid Hassan Nasarallah a shekarar da ta gabata. Babban malamin ya kara da cewa, taimakon da Imam Khaminae yayiwa kungiyar Hizbullah, ya kai matsayinda ba zamu tambaya, ko roka ba. Musamman bayan fara yaki a cikin watan Octoban shekara ta 2023, kuma ta bada wadannan taimakon ba tare da ta shiga yakin kai tsaye ba. Sheikh Qasem ya bayyana cewa, bamu...
    Wani babban jami’I a kungiyar Hamas ya bayyana cewa sojojin HKI sun kashe falasdinawa guda 6 a zirin gaza a ci gaba kissan kiyashin da takewa falasdinawa a yankin. Abdul-Karim Hanini, ya kara da cewa wadanda ta kashen tsoffin fursinoni a hannun yahudawan a shekarun da suka gaba 5 daga cikinsu an yi musayarsu ne a shekara 2011 a lokacinda aka yi musayarsu da fursinan yahudawan Galid Shalit a shekarar. Sannan dayan kuma an yi musayarsa ne a shekara ta 2002 wanda yahudawan suka kora daga Cocin Nativity daga birnin Bethlaham a yankin yamma da kogin Jordan. Abdul-Karim Hanini  ya kammala da cewa a dai dai lokacinda muke makokin yan’uwammu da yahudawan suka kai ga shahata, muna rokon All..ya karbi...
    Wannan nasarar ta sa Chelsea ta ƙara samun kuɗi fam miliyan 22 wanda ya ƙaru kan fam miliyan 60 da suka riga suka samu a gasar. Hakan yana nuna cewa suna samun riba daga siyan Joao Pedro da suka yi a fam miliyan 55. Fluminense ta nuna rashin jin daɗi lokacin da alƙalin wasa ya soke bugun daga kai sai gola da aka ba su, bayan duba na’urar VAR. Amma Chelsea na fuskantar damuwa da yiwuwar raunin ɗan wasan tsakiya Moises Caicedo ya samu. Chelsea za ta kara da Real Madrid ko Paris Saint-Germain a wasan ƙarshe a ranar Lahadi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    A yau Talata, hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC) ta sanar da cewa, ta ware karin kudi yuan biliyan 10, kimanin dalar Amurka biliyan 1.4, a cikin asusun kasafin kudi na gwamnatin tsakiya, don karfafa rawar da shirye-shiryen ba da tallafin ayyukan yi ke takawa wajen bunkasa daukar aiki da karuwar kudin shiga ga manyan kamfanoni.   Kudaden za su tallafa wa yankuna na lardi 26, da kungiyar masana’antu da gine-gine ta Xinjiang wajen aiwatar da ayyuka 1,975, wadanda ake sa ran za su samar da jimillar kudi yuan biliyan 4.59 a matsayin albashin ma’aikata, tare da taimaka wa muhimman mutane 310,000 wajen daidaita ayyukansu da kuma kara samun kudin shiga. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)...
    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka hana jiharsa sakat ba baki ba ne, ’yan cikinta ne. Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Talata. Ya ce tuni gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro mallakin jihar mai suna Katsina Community Watch Corps, inda aka debi matasa daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaron domin a dakile ta tun daga tushe. DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Malaman firamare sun janye yajin aiki a Abuja Katsina dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga, inda mutane dauke...