2025-07-11@19:45:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5519
«wata uku na»:
A dokar hukumar zabe ta 2010 sashe na 124, biyan kudi ga wani a matsayin cin hanci a kowane irin zabe ko karbar kudi ko kyauta domin jefa kuri’a ko hana jefa kuri’a a kowane zabe babban laifi ne da ke da hukuncin tarar naira dubu 500, 000 ko daurin watanni 12 a gidan gyaran hali ko kuma duka biyu. A kowane zabe kama daga na shugaban kasa zuwa kansila, Hukumar Zabe da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar kalubale daga masu sayen kuri’a da ke canzawa masu zabe zaben ra’ayin kan su zuwa zaben wanda aka ba su kudi ko ma kin yin zaben. Duk da kama masu sayen kuri’a da hukumomin yaki da cin hanci...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta bayyana dalilin da ya sa ta gayyaci malamin addini Sheikh Lawal Triumph. A wata sanarwa da ta fitar, ’yan sanda sun ce sun sani cewa wasu daga cikin wa’azozin da Sheikh Triumph ke yi suna haddasa rashin jituwa a tsakanin al’ummar jihar. Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote Rundunar ta ce kowa na da ’yancin faɗin albarkacin bakinsa, amma dole ne komai ya kasance bisa doka. Saboda haka ne Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, ya gayyaci Sheikh Lawal Triumph don tattaunawa da jami’an gwamnati, shugabannin addini da na al’umma. Manufar...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana a yau Juma’a da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a Kuala Lumpur na Malaysia, inda suka yi musayar ra’ayi kan danganatkar Sin da Amurka da batutuwan dake jan hankalin kasashensu. Wang Yi ya yi cikakken bayani kan matsayar Sin game da raya dangantakarta da Amurka, yana mai nanata bukatar bangarorin biyu su aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen suka cimma zuwa manufofi da ayyuka na hakika. Ya ce fatan ita ce Amurka ta kalli Sin da ra’ayi na sanin ya kamata da tsara manufar hulda da Sin bisa burin zaman lafiya da hadin gwiwar moriyar juna da tafiyar da dangantakarta da Sin bisa matsayi na daidaito da girmamawa da moriyar...
Tashar talabijin din “Cane” ta HKI ta bukaci Amurka da ta kafa kawance mai fadi na kasashe domin fuskantar kasar Yemen. A yayin ziyarar da Fira ministan HKI, Benjamin Netanyahu a Amurka ne dai ya bijiro da wannan bukatar, kamar yadda rahoton tashar talabijin din ta “Cane” ya ambata. Rahoton ya kuma ce, Jami’an HKI sun sanar da Amurka cewa, ci gaba da hare-haren Yemen, ya tashi daga zama matsalarta ita kadai, don haka da akwai bukatar kai hare-hare na hadin gwiwa da Amurka da kuma shigar da kasashen wannan yankin da kuma wasu na duniya.” Tun daga 2023 ne sojojin Yemen suke kai wa jiragen ruwa na HKI hare-hare a cikin tekun “Red Sea” ko kuma wadanda su ka...
Rundunar sojan mamaya ta sanar da kashe daya daga cikin jami’an sojojinta dake karkashin rundunar “Golani” a yankin Khan-Yunus dake Gaza. Da safiyar yau Juma’a ne dai sojojin mamayar HKI su ka snar da cewa wani daga cikin mayakansu mai mukamin Captain ya halaka a Gaza, kuma tuni sun bude bincike akan abinda ya faru. Rahoton tashar talabijin din ” Cane” ta HKI ya ambaci cewa, sojan da aka kashe yana cikin wadanda su ka kai hari a garin Khan-Yunus a jiya Alhamis. Sojojin mamaya sun kai hari ne a cikin wani gida a ci gaba da kashe ‘yan gwgawarmaya da suke yi, sai dai ginin gidan ya rufta da su, bayan da nakiyar da take cikinsa ta fashe. Tun...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministar Raya Al’adu, Hannatu Musawa, ta ce ya kamata shugabancin ƙasar nan ya ci gaba da kasancewa a hannun ’yan Kudu domin a samu adalci da daidaito. Ko da yake kundin tsarin mulkin Najeriya bai tilasta tsarin karɓa-karɓa ba, manyan jam’iyyun siyasa suna bin tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu. An tsare mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote A wata hira da ta yi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Hannatu Musawa ta ce tun da an samu Shugaba daga Arewa (Muhammadu Buhari) na tsawon shekaru takwas, to ya dace yanzu kuma a bar ’yan Kudu...
A yayin bincike, waɗanda ake zargin sun taimaka wajen gano bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da wata bindiga mai harsashi 16, wayar salula ƙirar Tecno guda ɗaya, da babur ƙirar Bajaj guda ɗaya. Kwamandan ya ƙara da cewa suna ci gaba da binciken su, kuma ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta bar masu laifi su samu wurin fakewa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ba laifi idan an yi murna ta shigar sabuwar shekarar Musulunci. Ba za a bi na wadanda za su bidi’antar da abin ba, domin hatta murnar haihuwar Manzon Allah (SAW) sun ce bidi’a ne. Har kai kanka ma za su iya ce maka bidi’a, saboda ba ka zo a zamaninsa ba. Masu wannan fahimtar Malamai sun ce ba wai suna nufin a koma wa Sunnar Manzon Allah ba ne, suna so ne a koma wa zamanin Annabi (SAW), ka ga ke nan sai mu ajiye su motoci da sauran kayan kere-kere na fasaha sda ake amfani da su yanzu har da su lantarki da su jirgin sama duk a ajiye, a koma amfani da su rakuma da dawaki da jakuna....
Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari. Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar. Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki Mutanen da aka kashe suna cikin wata motar haya da ta taso daga Basawa a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna. Baƙin suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kwa a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure. Wasu ɓata-gari ne suka...
Amurka ta bayyana dalilin sabunta manufofin, tare da lura da cewa “an tsara sharuddan bizar Amurka da ka’idoji domin kare tsarin shige da fice na Amurka.” Ofishin jakadancin ya kara da cewa “wadannan ka’idoji sun dogara ne kan ma’aunin fasaha da tsaro na duniya.” A cewar ofishin jakadancin Amurka yana aiki tare da hukumomin Nijeriya domin cimma wadannan matakan. Sanarwar ta ce “Tawagar Amurka tana aiki tare da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da cewa Nijeriya za ta iya cika sharuddan.” Misalin wannan sabon tsari ya hada da “Takardun tafiye-tafiye masu aminci: tabbatar da cewa kasashe suna ba da amintattun takaddun balaguro tare da ingantattun bayanan matafiyi, Kada aikin gudanar da Bisa ya wuce lokacin da aka dauka:.” Duk da sabbin...

Magance Matsalar Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta: Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyarwa A Makarantun Jihar
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, ƙaddama da shirin na nuni da ƙwazon gwamnatinsa na yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin aiwatar da dabaru daban-daban na ƙara yawan ɗalibai a makarantun jihar Zamfara. Ya ci gaba da cewa, “Alƙawarinmu na yin garambawul ya haɗa da tsare-tsare na yaƙi da rugujewar sassan ilimi da samar da haɗin gwiwa, kamar Bankin Duniya ta hanyar shirin AGILE da kuma UNICEF. A kwanakin baya Ma’aikatar Ilimi, Kimiya da Fasaha tare da haɗin gwiwar UNICEF, sun kafa wani kwamitin fasaha na shugabannin hukumomin da masu ruwa da tsaki domin ziyartar mananan hukumomi 14, da tantance yaran da ba su zuwa makaranta, da kuma tabbatar da shigar su makarantu. ...

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yunƙurin da aka yi na haɗa waɗannan maganganun da abubuwan da suka faru a Jihar Ribas, musamman batun dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ayyana dokar ta-baci, fassara ce da aka yi ta ba daidai ba, ko kuma suka ne ga kundin tsarin mulkin ƙasa. “Domin kaucewa ruɗani, Shugaba Tinubu bai cire Gwamna Fubara daga mukaminsa ba,” sanarwar ta jaddada. “Abin da aka aiwatar dokar dakatarwa ce, ba tsige wa ba. Wannan mataki da kuma ayyana dokar ta-baci an ɗauke su ne sakamakon rikicin siyasa mai tsanani da ya faru a Jihar Ribas a wancan lokacin.” Sanarwar ta ce rikicin da ya faru a Ribas ya cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya gindaya na...
Kididdigar ta nuna cewa maimakon amfani da wannan kudaden shigar don rage basussuka, wasu jihohi suna kara amso bashin. Jihar Ribas ta zama ta farko a jerin jihohin da adadin bashin cikin gida na naira biliyan 364.39 a wata uku na farkon 2025, mafi girma tsakanin jihohi 10. Basukan Jihar Inugu sun tashi daga naira biliyan 82.48 a farkon wata uku na 2024 zuwa naira biliyan 188.42 a farkon wata uku na 2025, wanda ke nuna karuwa na naira biliyan 105.95 ko kashi 128.4 cikin dari. Jihar Neja ta biyo baya da karuwar naira biliyan 57.68 a kowanne shekara, daga naira biliyan 86.07 zuwa naira biliyan 143.75, wanda shi ne karuwa na kashi 67 cikin 100. Jihar Taraba ta nunka...
A nata bangaren, Mrs. Adeniji ta bayyana cewa akwai yawaitar yara marasa zuwa makaranta a ƙananan hukumomi 14 na jihar, tare da tabbatar da cewa ta hanyar wannan shirin zai taimakawa ɓangaren ilimi a jihar Zamfara. “Muna aiki tare domin tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari s baya,” Cewar ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata Kotu a Jos, Babban Birnin Jihar Filato, ta tura mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Jihar Filato zuwa gidan yari. Ana zarginsu da kashe wasu ’yan ɗaurin aure a ƙauyen Mangun da ke Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar. Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Wasu Matasa Ba Sa Aiki Tukuru Wajen Neman Arziki Mutanen da aka kashe suna cikin wata motar haya da ta taso daga Basawa a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna. Baƙin suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kwa a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan da ke Jihar Filato domin halartar ɗaurin aure. Wasu ɓata-gari ne suka...
Malaman Bita na kananan hukumomin Jihar jigawa sun karrama Darakta Janar na Hukumar Jin dadin Alhazan jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa nasarorin da aka samu a aikin hajjin bana. A lokacin da jagoran Malaman Bitan yake jawabi wajen bikin karramawar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar, Ustaz Sa’idu Aliyu Galamawa ya bayyana cewar, makasudin karramawar shine ganin yadda Darakta Janar na hukumar ya bada gagurumar gudumawa wajen samun nasarar aikin hajjin 2025 a nan gida da kuma kasa mai tsarki. Ya kara da cewar, sun karrama Labbo ne domin nuna godiya da kuma farin ciki da yadda aikin hajjin bana ya gudana a fannoni dabam dabam. Shi kuwa Daraktan tsare-tsare na...
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka raba sun haɗa da irin shinkafa kilogiram 34,800, irin masara kilogiram 80,000, da lita 23,740 na maganin ciyawa, lita 11,735 na maganin kwari, da buhunan sinadarai na gyaran iri 23,470. A yayin jawabin maddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon takin zamani kyauta na nuni da yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin kawo sauyi a jihar Zamfara ta hanyar noma mai ɗorewa da bunƙasa karkara. Ya ce, “Aikin noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jiharmu, ba sashe kaɗai ba ne, amma asalin al’ummarmu ne. “Gwamnatinmu ta rungumi taken ‘noma abin alfaharinmu ne’. Noma na nuna ainihin ko su wane ne mu da kuma abin da ya kamata mu ba da...
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce yana da shakku a kan ko matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya za su ƙara aiki a nan gaba. Najeriya dai na da matatun mai guda hudu mallakinta a biranen Fatakwal da Warri da Kaduna. Amma attajirin ya ce matatun man waɗanda ke ƙarƙashin kulawar Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), sun laƙume sama da Dalar Amurka biliyan 18 wajen gyaransu, amma har yanzu sun ƙi aiki. Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC Ɗangote ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin shugabannin kamfanoni wadanda ke Karatu a Lagos...
“A wajen jahilai, tsagaggen lebe lahani ne a kan makogwaro da lebe, amma idan akwai shinge tsakanin hanci da baki, ana kiran sa da suna handa. Wani abu ne da ba a san abin da yake kawo shi ba, amma kuma ana danganta shi da abubuwa da dama kamar karancin rashin sinadarin bitamin B.” “Don haka, muna shawartar mata masu juna biyu da su mayar da hankali wajen yawan zuwa awon ciki, sannan kuma su rika shan magungunan da ake ba su na yau da kullum, ta yadda za a rage haihuwar masu dauke da wannan cuta. “Hakika wannan babban abin takaici ne a cikin al’umma, shi yasa kwararrun likitoci, ma’aikatan jinya, jami’an jin dadin al’umma da likitocin makogwaro, hanci...
“An tsara kungiyar ne domin hada kan Arewa da magance matsalar rashin aikin yi Wanda hakan ya sanya aka tattaro manyan hafsoshin soja da suka yi ritaya, da tsaffin gwamnoni, da masu rike da sarautun gargajiya, da masu fafutukar kare hakkin jama’a, da kungiyoyin matasa, da kwararrun a fannin ci gaban kasa wadanda da yawa daga cikinsu sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da mulki da kuma mayar da muradun Arewa saniyar ware a ‘yan shekarun nan” “Yankin arewa na iya shawo kan kalubalen da suke fuskanta ta hanyar hadin kai da kuma sabunta kudurin samar da ci gaba,” Bafarawa ya kuma tabbatar da cewa ba an kafa kungiyar bace a matsayin dandalin siyasa ba, kuma...
Kamfanonin inshora za su kauracewa jiragen ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda tsoron fuskantar hare-haren Yemen Jiragen ruwan da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila za su fuskanci kaurace daga kamfanonin inshora, sakamakon munanan hare-haren baya-bayan nan da sojojin Yemen suka kai kan jiragen Magic Seas da Eternity Sea, wadanda suka kai ga nutsewa, a teku a ranar Alhamis. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa ya bayyana cewa: Majiyoyin masana’antar inshora sun ce “kamfanonin inshora za su yi kokarin kauce wa rufe duk wani jirgin ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ko da kuwa alakar a kaikaice ne.” Kamfanin dillancin na Reuters ya nakalto daga Munro...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Jagora Da Kansa Ya Shiga Dakin Ba Da Umarnin Sojin Lokacin Yaki
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da umarninsa ga sabbin kwamandojin da kansu a lokacin yakin baya-bayan nan Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, yayin da yake ishara da umarnin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar a yakin kwanaki 12 da aka kakabawa Iran, ya ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kasance a dakin kwamandoji sau biyu a lokacin yakin tare da bayar da umarninsa ga sabbin kwamandojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A wata hira da aka yi da shi ta gidan telebijin, Qalibaf ya kara da cewa kwamandojin da aka nada sa’o’i bayan fara kai hare-hare kan kasar Iran,...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah Wadai Da Kakaba Takunkumi Kan Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi tsokaci kan takunkumin Amurka ta kakaba kan jami’ar Majalisar Dinkin Duniya da cewa: Ba za a iya murkushe gaskiya ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi tsokaci kan takunkumin da Amurka ta kakaba wa wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese. A cikin wani rubutu a dandalin “X” a ranar Juma’a, Baqa’i ya bayyana cewa: “Ba za a iya murkushe gaskiya ba.” Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu, Francesca Albanese, ta fuskanci takunkumi da girman kai saboda fallasa gaskiya da kuma tsayin...
Mataimakin shugaban kasar na farko ya jaddada cewa: Kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Iran Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: kalmar mika wuya ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron kasar. Arif ya ce: Kamar yadda kuke gani kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa, su mutane ne masu wayewa, tare da ingantaccen tarihin al’adu wanda ya wuce dubban shekaru. Ba su neman yaki, kuma ba su fara shi ba. Sun yi imani da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma a shirye suke don tattaunawa, amma ba za su mika wuya a...
A daya bangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran munanan laifuka. Daga labarun da ake samu yau da kullum, za ka yi tsammanin cewa; wadannan jihohi tuni sun tashi daga aiki, amma daga ziyarar da na kai musu; na ga abubuwan ban mamaki, tsoratarwa da kuma hadari duk da ke dauke cikin wannan labari. Duk da cewa, kowace jiha akwai abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci, su ma kamar sauran jihohin; suna...
Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana aiwatar da shirye-shirye masu ɗaukar hankali ta hanyar manyan ayyukan gine-gine, shirye-shiryen tallafa wa matasa, da kuma sauye-sauye a fannonin noma, makamashi, ilimi da ƙere-ƙere. Ministan ya bayyana cire tallafin fetur a matsayin ɗaya daga cikin manyan matakan da gwamnatin ta ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziki. Ya ce: “Ɗaya daga cikin manya kuma mafi tasiri daga cikin matakan da wannan gwamnati ta ɗauka shi ne cire tallafin fetur, wanda ko da yake ya kasance mai raɗaɗi, amma sauyi ne da ya zama dole. Bayan ceton tattalin arzikin ƙasa daga rugujewa, wannan mataki ya hana ɓarna da asarar kuɗi sosai a tattalin arzikin mu.” A cewar sa, kuɗaɗen da aka ceto...
An tsara Jirgin zai rinka yin zirga-zirga ne, zuwa daukacin kasashen da ke Afirka ta yamma da kuma sama da haka, musamman yin zirga-zirga daga Nijeriya zuwa kasashen, Jamhiriyar Benin, Togo, Ghana, Kamaru, Sierra Leone, Ibory Coast, Masar, Afirka ta Kudu da sauransu, tare da kuma nuna bukatar yin kasuwanci wadda tuni, aka fara ta. A martaninsa kan wannan nasarar, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, “ Wannan nasarar ta nuna irin mayar da hankalin da NPA ke ci gaba da yin a kara bunkasa ayyukan Hukumar wanda ta zo daidai da ta irin ma’aikatar bunkasa tattalin arzikin kasa. A na ta bayanain Mataimakiyar Shugabar kamfanin na On her Clarion Shipping West Africa Limited, Bernadine Eloka,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matasan Najeriya da dama suna son yin arziki amma ba tare da sun sha wahala ba. Sau da yawa matasa sun fi neman hanya mafi sauki da za ta basu arziki ba tare da sun sha wahala ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa bin yanke don tara abin duniya. Domin sauke shirin, latsa nan
Mai taimaka wa Sarkin Bayero kan harkokin yada labarai, Khalid Uba, ya shaida wa LEADERSHIP cewa magoya bayan Sarkin Bayero ba su da makamai. Uba, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin tawagar Sarkin Bayero da ke dauke da wani makami, sai dai an tilasta musu dakile harin. A cewarsa, wannan ba shi ne karo na farko da Sarkin Bayero ya taba bi ta wannan hanyar ba. “Bayan isowarmu daga gidan Dantata domin jaje, wasu matasa sun mamaye titin da duwatsu da makamai a Kofar Kudu. “Lokacin da muka isa Kofar Kudu, sai suka fara jifan mu, amma aka yi sa’a, mun yi nasarar fatattakar su zuwa cikin gida, kuma...
shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibof ya bayyana cewa asarorin da HKI ta yi a yakin kwanaki 12 da JMI suna da yawa. Kuma babu shakka ya fi abinda ta bayyana. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a lokacinda yake hira da wata tashar talabijin a nan Tehran . Ya kuma kara da cewa. Maganar cewa uahudawa 3500 kawai suka ji rauni a yakim gaba daya karya ce. Qalibof ya ce yana da tabbacin cewa yahudawa akalla 500 suna halaka sanadiyyar hare-haren da sojojin Iran suka kai a kan HKI a yankin kwamaki 12. . Ya ce sojojin yahudawan sun saba boye yawan mutanen...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar tattaunawa da Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya a bude take, amma kafin haka sai gwamnatin kasar Amurka ta biya diyyar kura kuran da ta yi a bayan. A wata hirar da yayi da Jaridar Le Monde na kasar Faransa Aragchi ya kara da cewa da farko Amurka yakamata ta canza halayenta, na rashin kaiwa kasar Iran hare-hare a lokacin tattaunawa. Ya ce diblomasiyya hanyace mai tituna biyu na zuwa da komawa, amma Trump ya zo ya rufe dayar. Kuma tattaunawar diblomasiyya a wajen Iran a ko yauce a bude yake, Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Iran a cikin yakin kwanaki 12 keta hurumin diblomasiyya...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya fadawa shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa, kan cewa huldar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA zai kasance tare da sharudda. Saboda hukumar ta yi watsi da ayyukanta na asali ta koma siyasa. Ta fita daga bangaren kwararru ta zama tana bin bukatun wasu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar ta IAEA a da can ta zuciya guda ce, bata boyewa hukumar wani abu a cikin ayyukanta na makamashin Nukliya. Amma a halin yanzu mun gano cewa hukumar ce take bawa HKI bayanai dangane da ayyukammu na Nikliya ta kuma bada sunaye dadireshin masana fasahar Nukliya na kasar HKI ta zo ta kashesu...
Hukumomin tsaron uku su ne, na DIA, DSS da kuma NIA, inda kuma dokar, ta bayar da damar kafa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro wato ONSA, wadda a baya, ake kiran ofishin da Babban Jami’in Tsaro na Kasa wato CONS. Wannan Jaridar, na nuna matukar damauwarta kan ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro, da Nijeriya ke fuskata, musamman na rashin gazawar hukumomin tsaro na sirri saboda gasar da suke nuna wa, a tsakaninsu. A bisa ra’ayinmu, wannan matsalar, abu ne da ke bukatar a kara mayar da hankali cikin gaggawa domin a magance wannan kalubalen na rashin na rashin tsaron. Sai dai, muna kuma yabawa kokarin da hukumomin tsaron ke ci gaba da yi,...
Rahotanni na cewa ’yan fashin daji masu yawan gaske ne aka tabbatar da kashewa a wani kwanton ɓauna da sojoji suka yi musu a ranar Laraba a jihohin Zamfara da Kebbi. Sojojin ƙasa da na sama sun yi amfanin da bayanan sirri wajen buɗe wuta kan ayarin ’yan fashin da ke kan ɗaruruwan babura suna zirga-zirga a yankin Yarbuga da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara. Kakakin Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Alhamis, inda ya ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun rika kokarin guduwa a kafa da kuma kan baburan, amma sojojin suka ci gaba da yi musu ruwan wuta ta ko ina. Muna so a...
Ƙwallon da Chinwendu Ihezuo ta zura a minti na 89 ya isa ya kai babbar tawagar mata ta Nijeriya da akeyiwa lakabi da Super Falcons zuwa matakin Kwata Fainal na gasar cin kofin Afrika ta mata da hukumar CAF ke shiryawa ta shekarar 2025, Super Falcons ta doke kasar Botswana da ci 1-0 a wasan da suka buga yau Alhamis da karfe 8 na dare agogon Nijeriya a Casablanca. A fafatawar da aka yi a filin wasa na Stade Larbi Zaouli, Ihezuo ce gwarzuwar wasan, sakamakon kwallo daya tilo da ta jefa a ragar kasar Botswana dake Kudancin Afirika, Nijeriya ta lallasa Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga, duk da cewa an tafi hutun rabin lokaci...
Mataimakin babban magatakardan MDD, kana sakataren zartarwa na kwamitin tattalin arzikin Afirka Claver Gatete, ya bayyana cewa, kasar Sin aminiya ce da kasashen Afirka za su iya dogaro da ita. Gatete ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da ya karbi takardar wakilcin kasa daga sabon wakilin kasar Sin a kwamitin tattalin arzikin Afirka na MDD, kana shugaban tawagar jakadun kasar Sin dake kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Jiang Feng a birnin Addis Ababan kasar Habasha, mazaunin kwamitin na tattalin arzikin Afirka na MDD. A yayin ganawarsu, Claver Gatete ya taya Jiang Feng murnar gudanar da sabbin ayyuka, ya kuma yi fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, domin ba da taimako ga bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen...
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya ta buƙaci Majalisar Tarayyar da ta amince da ƙudirin dokar da zai ba ta damar bincikar ɗaiɗaikun ’yan Najeriya game da yadda suka tara dukiyarsu. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito Shugaban EFCC, Ola Olukayode yana cewa ƙudirin mai suna “Unexplained Wealth Bill” ya je gaban ’yan majalisar tun a majalisa ta tara, wanda suka yi watsi da shi. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba “Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɓarnar da ake yi arzikin ƙasarmu da kuma matsalar tsaro,” a cewarsa yayin wani taro da kwamatocin majalisar...
Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 24 a wasu sabbin hare-hare da suka ƙaddamar a maɓoyar ’yan ta’addan a yankunan daban-daban a Arewa maso Gabashin Nijeriya. Kwamandan haɗakar rundunar Operation Haɗin Kai a Arewa Maso Gabas, Janar Abdulsalam Abubakar ya ce an kai samamen ne bayan tattara bayanan sirri. A cewarsa, an kuma kashe mutum biyar da suke samar wa ’yan ta’addan kayayyakin amfani, a wani kwanton ɓauna da aka yi musu da daddare. An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu An gudanar da waɗannan ayyuka ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Yuli a...
An tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, tare da ƙona gidaje sama da 100, wanda ake zargin wasu makiyaya ne a unguwannin manoma da ke Ƙaramar hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba suka yi. An kai wa mazauna unguwar Bandawa Gwenzu, waɗanda suka haɗa da: Gwenzu da Langwanshin da Danzhan hari a daren Laraba. Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno Da yake magana da tashar Talabijin na Channels TV ta wayar tarho a ranar Alhamis, shugaban matasan Uunguwar yankin, Ishaya Peter ne ya bayyana harin a matsayin rashin gaskiya da abu mai muni kuma ya yi Allah-wadai da harin. A cewarsa, mazauna garin na zaune suna...
Har ya zuwa yanzu, ’ya’yan JKS na ci gaba da nuna kyawawan misalai a fannin yayata manufar samar da ci gaba mai inganci, da kyautata jagoranci tun a matakin farko, da sauke nauyin dake wuyansu, da gudanar da ayyuka masu cike da kalubale, wanda hakan ya zamo kashin bayan ingiza nasarar jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban yahudawan Iran Rabbi Younes Hamami Lalezar ya ce, Isra’ila tana amfani da addini yahudanci domin cimma manufofinta, tana kuma bayyana Iran a matsayin wacce take fada da addinin yahudanci,alhali a cikin iran da akwai zaman lafiya tsakanin Mabiya dukkanin addinai. Haka nan kuma ya ce, kiyayyar da Isra’ila take da shi akan Iran ne, yake sa take jinginawa Iran din kin jinin yahduawa,wanda aikin ‘yan sahayoniya ne su samar da rabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Iran bisa addini da kuma kabila. Isra’ila tana bayyana kanta a matsayin mai bai wa yahudawa kariya, sai dai da dama daga cikin Mabiya addinin yahudanci, wadanda ba ‘yan sahayoniya ba, suna zarginta da amfani da addini saboda manufofi na siyasa. Fiye da shekaru ...
A wani ɓangare na bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Afirka, Shugaban Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mr. Ola Olukoyede, ya yi gargaɗi kan barazanar da ke ƙara ƙamari na damfara ta hanyar kuɗaɗen zamani da kuma zuba jari na bogi a Najeriya da sauran sassan nahiyar. Mr. Olukoyede ya bayyana hakan ne a yayin bukin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Afirka a wajen wani taron tattaunawa da aka gudanar a ofishin EFCC na shiyyar Kaduna. Darakta na riko na shiyyar Kaduna, Bawa Usman Kaltungo wadda ya wakilici Shugaban EFCC ya bayyana cewa nahiyar Afirka na ci gaba da fama da mummunar illar cin hanci da rashawa, musamman ta hanyar fitar...
Majalisar limaman musulmin nahiyar turai ta fitar da wani bayani da ta nesanta kanta daga wasu mutane da su ka kai ziyarar HKI tare da bayyana kansu a matsayin limamai daga kasashen turai, tana mai cewa, ko kadan ba su wakiltar al’ummar musulmin da suke cikin nahiyar ta turai. A ranar Litinin din da ta gabata ne dai ofishin shugaban HKI Ishaq Herzog ya fitar da bayani da a ciki yake cewa; A ofis dinsa dake birnin Kudus ya karbi bakuncin limaman musulmi daga kasashen Faransa,Belgium, Holland, Italia da kuma Birtyaniya.”. Ofishin majalisar limaman musulmin na turai, mai matsugunni a Faransa ya bayyana ziyarar mutanen zuwa Isra’ila da cewa, tana da daure kai, haka nan kuma lokacin da aka yi...
Kungiyar al-shabab mai alaka da alka’ida ta kai harin kunar bakin wake a wani barikin soja da yake birnin Magadishu a jiya Laraba da marece. Shaidun ganin ido sun ce, harin ya yi kara mai tsanani wacce ta girgiza babban birnin kasar Magadishu, sannan kuma harbe-harbe su ka biyo baya. Kungiyar al-shabab mai alaka da alka’ida ce ta dauki alhakin kai harin. Sai dai kuma babu wani cikakken bayani akan ko harin ya yi sanadin jikkata ko rasa rayuka. Ita dai kungiyar al-shabab ta dade tana kai hare-hare a cikin kasar Somalia da hakan ya sa gwamnatin kasar take daukar ta a matsayin kungiyar ta’addanci. A shekarar 2023 ma dai kungiyar ta al-shabab ta kai wani harin kunar bakin wake...
Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya (Kwastam), ta ce ta kama wata mota da ke ɗauke da wata kontena maƙare da mazaƙutar jakai a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hukumar ta Kwastam ta sanar da kama motar ne a ranar Alhamis. Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos An gano waɗanda suka yi safarar ne da ake zargin suna shirin fitar da shi zuwa ƙasashen waje ba bisa ƙa’ida ba. An samu nasarar ne a ranar Juma’a 5 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 9 na dare, bayan wani haɗin gwiwa da jami’an ofishin kula da namun daji na musamman da na hukumar...

Bafarawa Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Mai Suna “Arewa Cohesion Initiative” Don Maganin Kalubalen Da Yankin Arewa Ke Fuskanta
Ganin irin yawan kalubalen tattalin arziki da siyasa a Arewacin kasan nan ya sanya Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya kaddamar da wata sabuwar kungiya mai taken Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative. An kaddamar da wannan kungiyoyi ce a wajen wani babban taro da aka gudanar a Arewa House, Kaduna, inda manyan baki da mahalarta daga sassa daban-daban na Arewa suka halarta. A yayin taron, Bafarawa wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na tafiyar, ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon hanyar da za ta yi maganin baraka da inganta fahimtar juna da kuma karfafa ci gaban mai dorewa a yankin Arewa. Ya ce Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ban da haka, bayan da aka tsara “shirin shekaru 5”, yana da muhimmanci a aiwatar da shi. A kasar Sin, bayan da aka gabatar da wani “shiri na shekaru 5”, dole ne a aiwatar da shi yadda ake bukata. Kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar za su tsara salon aiwatar da dukkan ayyuka, da raba su ga sassa da yankuna daban-daban, don a aiwatar da su a matakai daban daban. Bayan haka, hukumomi daban daban su kan gudanar da ayyukan sa ido a tsakiyar wa’adin shirin, kuma za a tantance ainihin sakamakon da aka samu bayan karewar shirin. Ta wadannan halayen musamman, za a iya ganin abubuwan da za su tabbatar da aiwatar da...
Dakarun sojojin Nijeriya na rundunar sojojin sama tare da haɗin gwiwar Operation Haɗin Kai sun kai farmaki kan wasu muhimman wuraren da ’yan ta’adda suka mamaye a tsaunin Mandara da ke Jihar Borno. An samu labarin cewa rundunar sojin sama ta gudanar da samamen ta ne a wani wuri da aka san shi da tudu mai tsauni, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, bayan samun bayanan sirri. An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Daily Trust ta ruwaito cewa, samamen share fagen ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umurci sojoji da su kawar da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa unguwar Qua da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato. ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Adadin waɗanda aka kashe mutum 32 da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara suna cikin...
Wannan sabon birni na da ganuwa mai tsawon kilomita 8.5 da zai kare Legas daga ambaliyar ruwa, kuma yana da gidaje, ofisoshi da wuraren kasuwanci da na nishaɗi. Dangote ya ce wannan aiki yana daga cikin manyan abubuwan tarihin da Shugaba Tinubu zai bari. Hakazalika, ya nuna godiyarsa bisa fara aikin titin gaɓar teku daga Legas zuwa Kalaba da kuma aikin titin Sakkwato zuwa Badagry, waɗanda za su inganta sufuri da tattalin arziƙi a faɗin ƙasar. Ya kwatanta hangen nesan Tinubu da yadda ƙasar Netherlands ta kasance wajen samar da muhallai a cikin ruwa don raya birane. Dangote ya ƙara da cewa kamfaninsa na jin daɗin irin goyon bayan da gwamnati ke ba shi wajen sauƙaƙa kasuwanci da bunƙasa tattalin...
Gwamna Malam Umar Namadi na Jihar Jigawa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na farfado da harkar kasuwanci mara shinge a Maigatari, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin ginshikin bunkasar tattalin arziki, kasuwanci da masana’antu a jihar. Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kwamandan Yankin K da Jigawa na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Kwamanda Dalhat Abubakar, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a Fadar Gwamnati da ke Dutse. Gwamna Namadi ya taya Kwamanda Abubakar murnar nadin nasa, tare da yaba wa hukumar Kwastam bisa goyon bayan manufofin cigaban jihar Jigawa, musamman wajen farfado da aikin Maigatari da aka yi watsi da shi. Ya nuna godiya bisa goyon bayan Kwamandan ya bayar, tare da yabawa da rahotannin da ke...
Kotun Ƙoli ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo. Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi biyo bayan zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024. Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Tinubu ne ya buɗe wa Buhari ƙofar zama shugaban ƙasa — Hadimi Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ne, suka yanke hukuncin a ranar Alhamis. Sun yi watsi da ƙarar da ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo, ya shigar, kan cewar hujjojin da ya gabatar ba su da inganci. Mai Shari’a Garba, ya ce Ighodalo da jam’iyyarsa PDP ba su kawo hujjoji masu ƙarfi da za...

Ministan Tsaron Iran Ya Bayyana cewa: Martanin Da Iran Ta Mayar Ne Ya Sanya Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta
Ministan Tsaron Iran ya bayyana cewa: Hare-haren da Iran ta kai ne suka tilasta wa gwamnatin mamayar Isra’ila daukan matakin tsagaita bude wuta Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewa: Munanan hare-haren da sojojin kasar Iran suka kaddamar a matsayin mayar da martani ga yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita bude wuta. A wata tattaunawa ta wayar tarho guda biyu da ya yi da ministocin tsaron Venezuela da Armeniya, Birgediya Janar Nasirzadeh na rundunar sojin sama ya jaddada cewa: Hare-haren da sojojin Iran suka kaddamar kan yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita wuta. Ministan tsaron na Iran ya kara da cewa: Sojojin kasar Iran sun shirya tsaf domin mayar da martani ga...
Kwamandan sojojin kasa na sojojin Iran ya jaddada wajabcin Karin daukan matakan kare iyakokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kwamandan sojojin kasa na kasar Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya jaddada wajibcin kare cikakken kan iyakokin kasar akida, al’adu, da yanki, yana mai cewa: Dole ne dukkanmu al\umma su zama masu kare wannan kasa da kuma samun kwarin gwiwa daga tafarkin shahidai. A yayin wata ganawa da iyalan shahidan kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyawa ta kakaba wa Iran a birnin Sarpol-e Zahab na lardin Kermanshah a ranar Larabar da ta gabata, Birgediya Janar Heidari ya bayyana cewa: Sojojin kasar suna kan gaba wajen kare ‘yancin kai da yankinsu na kasar, kuma a kodayaushe suna nuna godiya da irin hakurin da iyalan...
“Mun yi watsi da ƙarar saboda babu ingantacciyar hujja a cikinta. Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke,” in ji Mai Shari’a Garba. Wannan hukunci ya tabbatar da cewa Sanata Okpebholo na jam’iyyar APC ne, halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Edo na shekarar 2024. PDP ta zargi cewa an yi maguɗi a zaɓen, inda ta nemi a soke sakamakon. Amma kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yi watsi da ƙorafinta, wanda ya sa suka kai ƙarar zuwa Kotun Ƙoli. Da wannan hukunci, an rufe duk wata shari’a da ta shafi zaɓen gwamnan Jihar Edo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya Bayyana Yadda Iran Da Mayar Da Martani Mai Gauni Kan Isra’ila
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Mayar da martanin Iran ga ‘yan sahayoniyya sun murkushe girman kan makiya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Martanin da Iran ta mayar wa yahudawan sahayoniyya a lokacin arangamar da suka yi a baya-bayan nan abin nuni ne, domin kuwa a duk tsawon tarihin haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta taba samun irin wannan martanin mai gauni ba. Ghalibaf, wanda ya karbi bakwancin jakadan Belarus a birnin Tehran, Dmitry Kaltsov, a jiya Laraba, ya yaba da matakin da gwamnatin Belarus ta dauka dangane da hare-haren da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauika na kai wa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran hare-haren wuce gona da iri. Yana mai...
Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya. A wata ganawa da iyalan shahidi Kanar Bostan Afrouz, Manjo Janar Hatami ya kara da cewa: Makiya sun kasa cimma tsare-tsare da shirye-shiryensu da suka rigaya sukaaniyar cimmawa, kuma sun fuskanci mummunar martani da shan kashi. Ya ci gaba da cewa: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya duk da karfin soja da kudi da suke da su, baya ga bayanan sirri da suke tabbatar...
Wani manazarci na Amurka ya bayyana sansanonin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Iran ta kaiwa hare-hare Wani manazarci Ba’amurke ya tattara jerin sansanonin da Iran ta kai wa hare-harer a wata makala inda ya bayyana cewa: Iran ta samu nasara a yakin da ta yi da ‘yan sahayoniyya. Wani mai sharhi kan harkokin siyasa da ke zaune a birnin Washington Mike Whitney ya yi nazari kan dalilan da ba a bayyana dalilan da suka sa Iran ta yi nasara kan haramtacciyar kasar Isra’ila ba a yakin kwanaki 12 a wani bincike da ya gudanar. Yana mai cewa; “Me yasa ba zato ba tsammani gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta da Iran?” Whitney ta rubuta a cikin...
Ya ce: “Ba mu kai inda muke so ba a fannin tattalin arziki, amma muna iya gani cewa abubuwa suna tafiya a hankali. Shugaban Ƙasa ya faɗa sau da dama cewa mun fara fitowa daga ƙunci. “Na san mutane da yawa za su ce ba mu kai ga cikakken cigaba da jin daɗin tattalin arziki ba tukuna. Gaskiya ne! Ni ma na yarda. Amma ba za mu ce babu cigaba ko kaɗan ba.” Ya ƙara da cewa: “Ko hukumomin ƙididdiga na duniya suna fara ba Nijeriya kyakykyawan matsayi. Muna ganin alamu na ɗagawa a hanyar da ake tafiyar da tattalin arzikin mu.” Idris ya ce manyan matakan sauyi kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar...
Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa (FUGA) a jihar Yobe za ta gwangwaje Uwargidan Shugaban Sasa, Sanata Remi Tinubu, da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, da wasu fitattun ’yan Najeriya shida da digirin girmamawa. A cewar jami’ar, za a ba su shaidar ce saboda gudunmawar da suka bayar a bangarori da daman a ci gaban kasa. Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri ce ta bayyana hakan a lokacin da take ganawa da manema labarai a jami’ar. Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza Ba Tinubu kaɗai ne ya sa Buhari ya ci zaɓe a 2015 ba – Boss Mustapha Ta ce za a karrama su ne a yayin bikin yaye dalibai karo na farko na jami’ar da zai gudana...
Hadimin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi, ya mayar wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha martani, kan cewa Tinubu bai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba wajen zama shugaban ƙasa a 2015. Ajayi, ya ce Buhari yana da ƙarfi sosai a Arewa amma hakan bai hana shi faɗuwa zaɓukan 2003, 2007 da 2011 ba. Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Ya bayyana cewa a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi a 2014, Tinubu ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya lashe. Ya ce Tinubu ne ya shawo kan gwamnonin APC da...
Tattaunawa na baya-bayan nan tsakakin HKI da Hamas ya tashi ba tare da wani ci gaba ba a birnin Doha na kasar Qatar. Idan an cimma wannan yarjeniyar dai ana saran musayan fursinoni 10 na HKI sannan za’a saki wasu da dama dake hannun HKI, Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa rashin nasarar wannan taron ya sanya makomar yaki a Gaza cikin rudu don yanzun kuma ba’a san abinda zai faru ba. Kuma bamu san manufar HKI ba a wannan yakin. Wani jami’in Falasdinawa ya fadawa tashar talabijin ta Al-Sharq kan cewa da alamun tawagar yahudawan sunzo ba taren da niyyar cimma wani Abu ba, tunda duk abunda aka tambayesu sai suce sai sun tambayi tel-Aviv,...
Ya ƙara da cewa, Tinubu na mutunta dimokuraɗiyya da doka. Haka kuma, gwamnati ta san cewa ba za ta iya aiki yadda ya kamata ba tare da kafafen yaɗa labarai ba. Idris ya ce a baya, wasu jami’an gwamnati suna sukar gwamnati, amma shi kullum yana tattaunawa da ƙungiyar ’yan jarida da masu wallafa jaridu domin warware matsaloli cikin lumana. “Idan muna yin daidai, ku yabe mu,” in ji shi. “Idan kuma muna kuskure, ku faɗa mana cikin lumana domin mu inganta ayyukanmu.” Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawar mu’amala da kafafen labarai kuma hakan zai ci gaba. Ya roƙi ’yan jarida ka da su ɗauki wasu ƙananan matsaloli su yi wa gwamnati hukunci a kai gaba ɗaya....
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattaunawa da Firay minister da kuma yerma mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya Mohammad bin Salman kan karfafa dankon zumuncim tsakanin kasashen biyu da kuma abubuwan da ke faruwa a yankin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran Aragchi ya hadu da dan sarkin ne a Makka, a ranar talata , kafin haka ministocin harkokin wajen kasashen biyu wato Faisal Bin Farhan kan wadan nan batutuwan. Dangantaka tsakanin kasashen biyu masu karfi a yankin, ya shiga cikin tsarin JMI na makobta da farko. Bin salman dangane rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da HKI da kuma Amurka, y ace yana fatan karshensa ya zama mai samar da zaman lafiya a mai dorewa...
Labaran da suke fitowa daga kasar Yemen sunn bayyana cewa sojojin ruwan kasar sun nutsar da wani karin tankar dakon mai mallakin HKI a cikin tekun Red sea. Sojojin kasar sun bayyana cewa jigin ya sabawa Haramcin don haka sun tsutsar da ita. Sun yi haka ne don nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu wadanda ake zalinta a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jirgin yana nufin zuwa ummu Rash Rash ko Ilat kamar yadda yahudawan suke kiransa. Sojojin kasar Yemen sun kara da cewa sun dauki wannan matakin kan jirgin ne bayan an gargade shi da ya koma amma yaki sauraro. Da wannan talilin sojojin ruwa na kasar yemen suka yi amfani da jiragen...
Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa wata ma’aikaciyar MDD takunkumi saboda yadda take amfanin laifukan yaki da take yi a gaza da kuma irin tallafin da Amurka take bawa HKI yasa tana da hannun a kissan kiyashin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa shi ya sa hannu a kan umurnin takunkuman da aka dorawa Francesa Albanese, jami’a mai kula da tattara bayanai na musamman a kan Falasdinu ga hukumar kare hakkin bil’dama da MDD. Rubio ya bayyana cewa sanadiyyar rahoton ta ne kotun ICC ta fidda samacin kama Banyamin Natanyaho, da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yoav Galant. Banda haka takan bada rahoto kan yadda Amurka da...
Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, ciki har da ɗan sanda da ’yan sa-kai guda uku, a wani hari da ’yan bindiga suka kai garin Mongoro da ke Ƙaramar Hukumar Mariga, a Jihar Neja. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Laraba. Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II ’Yan ƙabilar Ibo ne suka fi aikata laifi a Jihar Anambra ba Fulani ba — Gwamna Soludo Mazauna garin Wamba, sun ce har yanzu suna cikin fargaba saboda ‘yan bindigar ba su bar yankin ba. A ranar 24 ga watan Yuni, maharan sun kai hari wani sansanin sojoji da ke Kwanan-Dutse, inda suka kashe sojoji 17, tare da jikkata wasu 10. A cewar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A gabanin bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD, taron kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD wato UNHRC karo na 59 ya zartas da kudurin da kasar Sin ta gabatar dangane da muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam. Wannan ne karo na farko da aka zartas da kudurin ta hanyar tattaunawa a maimakon kada kuri’a. Kasar Sin ta gabatar da kudurin ne a shekarar 2017. Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da kungiyoyin kasa da kasa a kasar Switzerland ya yi karin bayani kan kudurin da cewa, kudurin ya sake nanata muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam daga dukkan fannoni, tare da jaddada yadda ci gaba mai inganci kuma...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tashin hankali ya sake kunno kai a Masarautar Kano, inda aka zargi wasu magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da kutsawa cikin fadar Sarki Muhammadu Sanusi II ta Gidan Rumfa da ke Kofar Kudu. Shaidu sun bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne lokacin da tawagar Sarki Aminu ke dawowa daga gaisuwar rasuwar attajirin ɗan kasuwa, marigayi Alhaji Aminu Ɗantata. Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya A wata sanarwa da kakakin masarautar Kano, Sadam Yakasai, ya fitar ya bayyana cewa Sarki Sanusi ba ya cikin fadar lokacin da abin ya faru ba. “Sun fasa kofar shiga fadar, sun kai wa masu gadi hari,...
Gwamana Charles Soludo na Jihar Anambra ya ce mafi rinjayen kaso na waɗanda jami’an tsaro ke kamawa da aikata laifuka tsawon shekara uku da suka gabata ’yan kabilar Ibo ne. BBC ya ruwaito Soludo yana bayyana hakan a yayin wani taro da ’yan asalin jihar mazauna ƙetare suka gudanar a Amurka. Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya Soludo wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne ya yi watsi da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya na aikata satar mutane a jihar. “Yanzu shekara uku da wata uku ke nan ina kan mulki. Idan muka kama masu laifi 100 to kashi 99 cikin 100 matasan ƙabilar...

An Yi Hasashen Karuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Tiriliyan 35 Tsakanin 2021 Zuwa 2025
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Game da koma bayan tattalin arziki da duniya ke fuskanta, ana matukar bukatar bullo da sabbin hanyoyin samun bunkasa. Shi ya sa, yin kirkire-kirkire da habaka hanyoyin samun bunkasa, ya zama mataki mafi jawo hankula daga cikin tsarin hadin gwiwar mambobin BRICS. Sin ta sanar a wannan taro cewa, za ta kafa cibiyar nazarin sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ta Sin da kasashen mambobin BRICS. Kazalika, game da babakeren da Amurka ke nunawa, mambobin BRICS sun yi kira da a kiyaye ra’ayin kasancewar mabambantan bangarori a duniya da gaggauta kafa kyakkyawan tsari da dokar tattalin arziki da cinikin duniya mai adalci da bude kofa. Albarkacin cika shekaru 10 da kafuwar bankin NDB na BRICS, Sin...
Tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgediya Muhsin Rizai, ya sanar da cewa; Dakarun IRGC sun yi nasarar harbo jirage manya da marasa matuki na HKI har guda 80, kuma da akwai baraguzai 32 daga cikinsu da ake rike da su. Birgediya Rizai ya kuma kara da cewa; Daga cikin wadanda aka harbo din da akwai samfurin “Hermes” da “Hermon” da sune kira ta karshe da ‘yan sahayoniya suke takama da su. Birgediya Muhsin Rizai wanda memba ne a majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci ta Iran, wanda tashar talbijin ta yi hira da shi da marecen jiya Talata, ya yi Magana akan bangarori da dama na kallafaffen yakin kwanaki 12 inda ya ce:” Gabanin mu yi...
Sojojin Yemen sun sanar da nitsar da jirgin ruwa “Eternity’ wanda yake hanyar zuwa tashar jiragen ruwan HKI ta Eliat, bayan da matukinsa ya ki jin girgadin da aka yi masa. Janar Yahya Sari ne ya bayyana cewa; Jirgin ruwan ya ki jin gargadin da aka yi masa na hana kowane jirgi wucewa zuwa tasoshin jiragen ruwan HKI. Sanarwar sojojin kasar ta Yemen ta kunshi cewa, sun yi amfani da karamin jirgin ruwa maras matuki da kuma wasu makamai masu linzami guda shida domin dakatar da jirgin ruwan. Sai dai, tun da fari sojojin na Yemen sun tseratar da matukin jirgin da ma’aikatan da suke cikinsa, tare da ba su kulawa ta kiwon lafiya. Janar Sari ya ce; Suna daukar...
Shugaban kungiyar Kurdawa ta kasar Turkiya ( PKK) Abdullah Ojlan ya sanar da kawo karshen amfani da makamai a fafutukar da kungiyarsu take yi na kare hakkokinsu a kasar Turkiya. Shugaban kungiyar Kurdawan na Turkiya wanda yake tsare a kurkuku na shekaru masu tsawo, ya aiko da sako na bidiyo da a cikin ya ce; Har yanzu ina kan kiran da na yi a ranar 27 ga watan Febrairu na ajiye makamai”. Ojlan ya kara da cewa; Muna sanar da kawo karshen amfani da makamai ne bisa radin kanmu, haka na kuma ya ce; Mun shiga Zangon aiki da doka da kuma siyasa da tsarin demokradiyya, wanda shi kanshi nasara ce mai dimbin tarihi ba asara ba.” Kuniyar PKK ta...

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Kara Kamfanoni 8 Na Yankin Taiwan Cikin Jerin Wadanda Aka Takaita Sayar Musu Kayayyaki
A yau Laraba, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanya wasu kamfanoni 8 na yankin Taiwan cikin jerin sunayen wadanda aka takaita sayar muku kayayyaki. Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar ta ce, an dauki matakin ne domin kiyaye tsaron kasa da kare muradunta da kuma cika wajibcin hakkin kasa da kasa kamar hana yaduwar abubuwa masu cutarwa. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ziyarci iyalin marigayi, Alhaji Aminu Dantata a Jihar Kano, don yi musu ta’aziyya. Obi, ya bayyana cewa ya yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar Alhaji Ɗantata, inda ya bayyana shi a matsayin “uba ga kowa.” An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN 2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo Ya yaba yadda Ɗantata ya zama babban attajiri kuma ya taimaka wa mutane da dama suka samu nasara a rayuwarsu. Ya ce Ɗantata ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya. “Mun zo nan yau don jimami tare da iyalinsa da kuma ɗaukacin ‘yan Najeriya, saboda...
Sanarwar ta ƙara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga ƙarananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin kuɗaɗen garatuti. Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen daidaita biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati, musamman waɗanda suka yi ritaya bayan shekaru 35 suna aiki kuma suka kai shekaru 60. “Gwamnatinmu ta gaji sama da Naira Biliyan 13 a matsayin bashin kuɗaɗen garatuti na waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomin daga 2011 zuwa 2023, jinkirin ya jawo wahalhalu, kuma wasu da suka yi ritaya sun mutu su na...
Karuwar tasirin da kasar Sin ke yi a fagen ci gaban kimiyya da fasaha a duniya ba barazana ba ce, sai dai wata dama ce ta kawo ci gaba mai gamewa. Diamond ya kara da cewa, “Kasancewar na yi aiki kafada da kafada da wasu jami’o’i da cibiyoyin kasar Sin na tsawon shekaru masu yawa, na yi amanna da yadda kasar Sin ta dukufa ga samar da kimiyya da fasaha mai bude kofa ga duk duniya bisa adalci.” Kazalika, masanin kimiyya, mamba a makarantar nazarin kimiyya da fasaha ta Afirka, Farfesa Felix Dapare Dakora, ya nuna yadda kasar Sin ke karfafa shigar kasashe masu tasowa cikin harkokin kimiyya a duniya. Yana mai cewa, “A halin yanzu, an gode da samuwar...
Firaministan Sin Li Qiang ya bayyana a yau Laraba cewa, a matsayinsu na muhimman membobin kasashe masu tasowa, ya kamata Sin da Masar su karfafa hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare, domin kare muradunsu na bai daya. Li Qiang ya bayyana haka ne bayan isarsa birnin Alkahira, a ziyarar aiki da yake yi a kasar bisa gayyatar takwaransa na Masar din, Mostafa Kamal Madbouly. Firaministan Masar da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar ne suka tarbi Li Qiang tare da shirya biki domin yi masa maraba. Kafin isarsa, Li Qiang ya halarci taron kungiyar BRICS karo na 17 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
An gabatar da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a matsayin Shugaban Kwamitin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN). Wannan naɗin ya biyo bayan murabus ɗin da Ganduje ya yi daga shugabancin APC kwanan nan, inda ya bayyana cewa ya yi hakan saboda wasu muhimman dalilai na ƙashin kansa. 2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai Jam’iyyar ta maye gurbinsa da Ali Bukar Dalori a matsayin shugaban riƙon ƙwarya. Gbenga Saka, mai bai wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, shawara kan harkokin dijital, ya wallafa bidiyon bikin rantsar da Ganduje a shafin X. Ganduje, wanda tsohon...
Tsohon jigo a Jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya ce dole ADC ta tsayar da ɗan Arewa takara idan tana son ta kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Okonkwo, ya ce idan ADC ta tsayar da ɗan Kudu takara, Tinubu zai sake lashe zaɓe ba tare da wata tangarɗa ba. Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross Ya ce dole ne ’yan adawa su yi aiki da hikima da dabaru idan suna son yin nasara. “Shirina a wannan karon shi ne zan goyi bayan ɗan Arewa a 2027,”...
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ta ƙara sanya wa ’yan Najeriya da ke son ziyartar Dubai sabbin sharuɗa. Haka kuma, ta dakatar da bayar da bizar wucin gadi ga ’yan Najeriya. Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Aminiya ta samu labarin cewa hukumomin shige da fice na Dubai ne suka bayar da umarnin sabbin matakan ga ofishin jakadancin ƙasar da ke Najeriya. Daga cikin sabbin dokokin, duk ɗan Najeriyar da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 45 ba zai samu bizar yawon buɗe ido ba sai idan zai yi tafiya tare da wani. Wannan na nufin cewa yawan ’yan Najeriya...
Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce akwai yara akalla miliyan biyar da dubu 400 da ke fama da matsalar karancin abinci a jihohi tara na arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro. A cewar kungiyar, jihohin su ne Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, Zamfara, Neja, Binuwai da kuma Kano. Mai rikon mukamin Darktan Lafiya da Kula na kungiyar Dr Aminu Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a yayin taron gangamin neman tallafi kan karancin abinci na kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma da ya gudanar a Kano ranar Talata. Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja...

Iran Ta Musanta Neman Ci Gaba Da Gudanar Da Tattaunawa Da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sanar da cewa: Iran ba ta gabatar da wata bukatu na ganawa ga bangaren Amurka ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta kalaman shugaban Amurka dangane da muradin Iran na gudanar da tattaunawa, yana mai jaddada cewa: A bangaren Iran ba a gabatar da wata bukata ta yin wata ganawa da bangaren Amurka ba. Da yake mayar da martani ga kalaman Donald Trump, Ismail Baqa’i ya ce: Iran tana musanta abin da Trump ya fada game da bukatar Iran na gudanar da tattaunawa, kuma ba ta gabatar da wata bukata ta ganawa da Amurkawa ba. Yayin ganawarsa da Fira ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu da yammacin ranar Litinin, Trump ya yi ikirarin cewa an...
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojojinta Wani jami’in sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci a ranar Talata cewa; Hare-haren da Iran ta kai a watan da ya gabata sun afkawa wuraren sojojin mamayar Isra’ila, matakin da tuni duniya ta amince da kai irin wadannan hare-hare kan cibiyoyin sojin mamaya. Jami’in da ke magana da kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ki bayar da karin bayani, ciki har da gano wuraren da abin ya shafa ko kuma irin barnar da harin ya yi ga kayayyakin aikin soja. Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki kan haramtacciyar kasar Isra’ila a watan da ya gabata...

Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa
Shi ma Uban taro mai masaukin baki, shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana a jawabinsa na taron kolin cewa, “Idan har ba a samu sauyi a tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa a wannan karni na 21 ba, to ya zama wajibi kasashen BRICS su taimaka wajen ganin an sabunta shi.” BRICS taska ce ta hadin kai, daidaito da kuma kokarin tafiya tare don samun ci gaba da tsira tare, da kuma karfafawa kasashe masu neman ‘yancin fadin albarkacin bakinsu a harkokin tsare-tsare na hadin kan kasashen duniya. Taron kolin kungiyar na bana, na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwannin duniya ke cike da firgici biyo bayan yakin cinikayya da kasar Amurka ta kaddamar,...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki. Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a...
Shugaban Majalisar Kolin siyasar kasar Yemen ya jaddada ‘yancin kowa da kowa wajen gudanar da zirga-zirga a teku in banda makiya ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen, Field Marshal Mahdi al-Mashat, ya jaddada aniyar kasar ta Yemen na ba da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa ga kowa da kowa in banda makiya yahudawan sahayoniyya da kuma masu goya musu baya a lokacin da suke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza. A cikin wata sanarwa da Al-Mashat ya fitar ya ce: Ba su da wani sha’awar kai hari ga duk wanda ba shi da alaka da goyon bayan makiya yahudawan sahayoniyya, yana mai kira ga dukkanin kamfanonin jiragen ruwa da su...
Ministan Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen sake kara kudin wutar lantarki domin rage yawan bashin da bangaren lantarkin ke bi. Bayanai dai sun nuna yanzu haka, bashin lantarkin da ake bi a Najeriya ya haura Naira tiriliyan hudu. Amma a cewar ministan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki 300 a Abuja, yunkurin wani bangare ne na tabbatar da cewa bangaren lantarki ya tsaya da kafarsa. Matar tsohon Gwamnan Adamawa ta sauya sheka daga PDP zuwa ADC Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda Idan dai za a iya tunawa, duk da Karin kudin wutar da aka yi wa kwastomomin da ke tsarin Band A,...

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A CPC, Haruna Sa’eed Kajuru, Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Kisan ‘Yan Zariya A Filato
Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan. Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a Zaria, inda ya nuna alhini da ta’aziyya ga dangin waɗanda wannan al’amari ya shafa. Tsohon Akanta Janar na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Kajuru, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na kashe...
Jam’iyyar ADC ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu shugabanni daga yankin Kudu sun buƙaci Atiku Abubakar, da ka da ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan labari ƙarya ne, wanda aka ƙirƙira don haddasa rikici , musamman a wannan lokaci da ake ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya. Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense Jam’iyyar ta ce: “Ba mu taɓa zama da wasu wakilai daga Kudu domin yin irin wannan magana ba. “Wannan rahoto ba kawai ƙarya ba ne, yana kuma...
Matar tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Zainab Boni Haruna, ta fice daga tsohuwar jam’iyyarta ta PDP zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. Zainab, wacce asalinta ta fito ne daga karamar hukumar Nangere a Jihar Yobe ta bayyana haka ne a wani taro da mata magoya bayan jam’iyyar ta ADC da aka gudanar a Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe. Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda Zainab Boni ta kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Shugaban Kasa Bola Tinubu kan rashin tsaro, wahalhalu, cin hanci da rashawa da kuma rashin shugabanci na gari a kasar nan. “Mutane suna shan...
Amma yanzu, sabon tsarin ya rage wa’adin bizar zuwa wata uku kacal, kuma mutum zai iya shiga sau ɗaya ne kawai da ita. Ma’aikatar ta ce wannan mataki yana daga cikin gyaran tsarin alaƙar diflomasiyya da tsaro da Amurka ke yi da sauran ƙasashe. Sai dai ta bayyana cewa za a iya sauya wannan tsari a nan gaba, idan an samu canji a dangantakar diflomasiyya, tsaro ko dokokin shiga ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan ya janyo tambayoyi kan ko za ta iya komawa nan take. A lokacin da aka tambaye ta me take yi a lokacin da aka dakatar da ita, Sanata Natasha ta ce ba ta tsaya ba, har yanzu tana gudanar da ayyuka tare da wakiltar mutanenta. “Na kasance ina aiki a duk lokacin. Na ci gaba da aiki kuma ina shirin gabatar da wasu dokoki a kan ma’adanai. Ba zan iya miƙa su ga wani ba,” in ji ta. Ta ƙara da cewa duk da cewa ba ta halartar zaman majalisa, ta ci gaba da yin ayyukan ci gaba ga mutanenta. “Fitar da ni daga majalisa ba kawai ni aka daƙile ba, an hana muryar Kogi ta Tsakiya fitowa fili,”...
Gwamnan jihar Texas ta Amurka ya ce sama da mutane 160 ne har yanzu ba a gano ba sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Juma’ar da ta gabata. Greg Abbott ya ce wannan adadi na lardin Kerr ne kaɗai, ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya fi muni. Hukumomi dai sun bayar da rahoton mutuwar fiye da mutum 100. Masu aikin ceto na aiki a sannu a ƙoƙarin kawar da tarkacen da ruwan ya janyo domin gano ko akwai mutanen da ke maƙale a ƙarƙashinsu musamman a yankin gaɓar kogin Guadalupe. A jihar New Mexico da ke makwabtaka da Texas, ruwa ya tafi da wani gida inda wani uba ke zaune da ‘ya’yansa biyu a yankin Ruidoso, kuma...