Iran Ta Yi Tir Da Takunkuman Tattalin Arzikin Da Amurka Ta Dorawa Ma’aikaciyar MDD
Published: 12th, July 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakai yayi tir da gwamnatin Amurka kan takunkuman da ta dorawa Francesca Albanese jami’a Ta musamman a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD wacce take aikin tattara bayanai dangane da yakin da ke faruwa a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Bakaei yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa ; Ba wanda ya isa ya rufe bakin gaskiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Manazaecin Kasar Amurka Ya Ce; Isra’ila Ta Sha Kashi A Yakinta Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
Wani manazarci na Amurka ya bayyana sansanonin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Iran ta kaiwa hare-hare
Wani manazarci Ba’amurke ya tattara jerin sansanonin da Iran ta kai wa hare-harer a wata makala inda ya bayyana cewa: Iran ta samu nasara a yakin da ta yi da ‘yan sahayoniyya.
Wani mai sharhi kan harkokin siyasa da ke zaune a birnin Washington Mike Whitney ya yi nazari kan dalilan da ba a bayyana dalilan da suka sa Iran ta yi nasara kan haramtacciyar kasar Isra’ila ba a yakin kwanaki 12 a wani bincike da ya gudanar.
Yana mai cewa; “Me yasa ba zato ba tsammani gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta da Iran?” Whitney ta rubuta a cikin wannan bincike a cikin mujallar Bincike ta Duniya. “Wannan tambaya ce da kafafen yada labarai na Yamma ba su amsa ba, da ke sanya al’ummar Amurka cikin duhu. Watakila kun ji cewa tsaron sararin samaniyar Isra’ila na gab da rugujewa, lamarin da ya bar ta cikin hadari ga hare-haren Iran, amma wannan wani bangare ne na labarin kawai.
Ya kara da cewa: Kasa da makonni biyu da fara wannan rikici, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta mika wuya, Iran tana lalata muhimman wuraren a Isra’ila daya bayan daya bisa zurfin tunani da karfi, ba tare da nuna wata alamar ja da baya ba, don haka Isra’ila ba ta da wani zabi illa amincewa da shan kaye.