Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin
Published: 22nd, July 2025 GMT
Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ta ce ta ceto wani bene mai hawa biyu daga rugujewa gaba daya sakamakon wata gobara da ta tashi a garin Ilorin.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda y ace gobara da ta tashi a hanyar Muritala Muhammed, daura da Cocin C & S, Ilorin.
A cewarsa da isar su, ma’aikatan kashe gobara sun gano cewa wani gini mai hawa biyu da ya kunshi dakuna 8 da shaguna 10 na fuskantar barazana. Ya bayyana cewa, ta hanyar daukar mataki cikin gaggawa da hadin kai, jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar yadda ya kamata, tare da hana yaduwarta zuwa gine-ginen da ke kewaye, inda ta kara da cewa a sakamakon haka, daki daya ne lamarin ya shafa.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa wutar lantarki ce dalilin ta tashin gobarar.
Da yake mayar da martanin Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara Prince Falade Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su kasance cikin shiri da kiyaye lafiya a gidajensu da wuraren kasuwancinsu.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gobara kashe gobara ta
এছাড়াও পড়ুন:
Shirin Ba Da Horo A Kasar Sin Ya Taimaka Wa Inganta Masana’antar Gyadar Senegal
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp