Allah Ya Yi Wa Wakilin Sadarwan Bauchi, Jafaru Ilelah, Rasuwa
Published: 23rd, July 2025 GMT
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin masani a harkar hulɗa da jama’a kuma ma’aikacin gwamnati na gari da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga jihar.
Ya ce aikin wayar da kai da ya yi ba za a manta da shi ba.
Gwamna Bala Muhammad, ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa, abokansa da masarautar Bauchi.
Ya bayyana Ilelah a matsayin mutum mai kishin ƙasa da jajircewa a bakin aiki.
Ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya jiƙansa kuma ya sanya shi a Aljanna Firdausi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: An ƙaddamar da aikin sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi
Gwamna Bala Muhammad ya ƙaddamar da aikin gyare-gyare da sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi kan kuɗin da ya haura Naira biliyan bakwai, wanda ya haɗa da inganta kayan aiki, ofisoshi, da kuma gina sabon ofishin hukumar kula da harkokin majalisa.
A yayin ƙaddamarwar da aka gudanar ranar Talata, Gwamna Bala ya bayyana cewa wannan gyara na cikin shirin gwamnatinsa na sauya fasalin birane da samar da muhalli mai kyau ga ma’aikata domin sauƙaƙa aikinsu.
Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen $21bn a ƙetare UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yaraYa ƙara da cewa tuni aka riga aka biya rabin kuɗin aikin domin tabbatar da cewa aikin ya kammala a kan lokaci.
Kwamishinan gidaje da muhalli, Danlami Ahmed Kawule, ya ce aikin zai ƙunshi gyaran zauren majalisar, ofisoshin mambobi, gina sabbin hanyoyin ruwa da wutar lantarki na masu amfani da hasken rana, da kuma gyara titunan cikin majalisar.
Tun da farko, mambobin majalisar sun koma ofishin tsohon mataimakin gwamna domin ci gaba da aikinsu yayin da ake gudanar da gyaran.
Gwamnan ya yaba wa fahimtar da ke tsakaninsa da majalisar, yana mai cewa hakan ne ke bai wa gwamnati damar aiwatar da ayyukan ci gaba.
Kakakin Majalisar, Abubakar Y. Suleiman, ya bayyana godiya bisa wannan ci gaba, yana mai cewa haɗin kai tsakanin majalisar zartarwa da majalisar dokoki na taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba a jihar.