Ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana alfahari da rusa Gaza da tarwatsa mazauna yankin!

Isra’ila Katz, ministan yakin gwamnatin mamayar Isra’ila, ya wallafa wani hoto da ya nuna yadda aka lalata garin Beit Hanoun a arewacin zirin Gaza, yana mai alfahari da yadda aka rusa gine-ginen garin”.

Kuma ta hanyar dandalin “X”, Kats yayi sharhi game da hoton, yana cewa: “Bayan Rafah da Beit Hanoun.. babu mafaka ga ‘yan ta’adda.

Hoton da aka dauka ta sama yana nuni da dimbin baraguzan gine-gine da kango da kuma irin barnar da aka yi wa daukacin garin da ke daura da layin da aka shimfida da tarwatsewar kango da ragowar gine-ginen da suka ruguje a hoton inda ke nuni irin girman bala’in da ya afku a yankin.

Beit Hanoun shi ne yanki na farko da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka mamaye a farkon harin na kasa a Gaza a ranar 28 ga watan Oktoban shekara ta 2023, a ci gaba da yakin kisan kiyashi bayan barna da Falasdinawan sama da dubu 195 suka yi shahada da kuma jikkata.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye

Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma.

 

A nasa bangaren, mahaifin budurwar, Malam Aliyu dake Garin Dakasoye, ya tabbatar da cewa za su gudanar da bikin domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya ba su.

 

Ya kara da cewa: “Mun gode wa Allah bisa wannan arziki, kuma muna sa ran gudanar da bikin tare da sanya musu suna domin nuna godiya ga Allah mai daukaka.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta
  • Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
  • Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki