Jami’ar Yobe sun tsunduma yajin aiki
Published: 12th, July 2025 GMT
Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗaukar musu.
Waɗannan alƙawura sun haɗa da ƙarin albashi, biyan bashin da suke bi, da kuma barin jami’ar ta riƙa gudanar da harkokinta da ƙashin kanta.
Shugaban ASUU na Jami’ar Yobe, Dokta Ahmed Karage, ya bayyana hakan bayan kammala wani taro da suka gudanar.
Ya ce sun fara yajin aikin ne bayan dogon lokaci da suka ɗauka suna tattaunawa da gwamnati, amma ba su cimma matsaya ba.
“Mun kwashe watanni muna magana da gwamnati, amma abin takaici shi ne dole ne yanzu mu tafi yajin aiki saboda gwamnati ta ƙi cika alƙawuran da ta ɗauka,” in ji Dokta Karage.
Daga cikin buƙatunsu akwai aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, biyan bashin albashin da ya fara tun daga shekarar 2019, da kuma wasu haƙƙoƙinsu.
Ya ce jami’o’i su riƙa tafiyar da al’amuran su da kansu shi ne mafita don warware matsalolin da ake fama da su a fannin ilimi.
ASUU ta ce ba za su koma aiki ba har sai gwamnati ta magance matsalolin da suka gabatar.
Sun gargaɗi gwamnatin jihar kan ɗaukar matakin gaggawa don kaucewa kawo cikas ga kalandar karatu.
Har ila yau, ƙungiyar ta roƙi dalibai da su yi haƙuri, inda ta ce ta fara yajin aikin ba don cutar da su ba, illa dai domin neman haƙƙinsu da ya wajaba gwamnati ta biya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Jami ar Yobe Ƙarin Albashi Yajin aiki gwamnati ta da gwamnati
এছাড়াও পড়ুন:
Bida Poly ta kawo sojoji su kula da jarrabawar ɗalibai
Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa.
Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus ɗin ƙarin aiki na watanni 18 da suka wuce.
Ƙungiyar ta umarci mambobinsu da kada su gudanar da jarrabawar zangon da ta fara ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025.
Wani ma’aikacin makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin an gayyace su ne domin kare ɗalibai da wasu malamai daga shirin da ASUP ke yi na hana gudanar da jarrabawa.
’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu An kama su kan satar zinarin Naira miliyan 110 a Kebbi“Ba wai don su gudanar da jarrabawar aka kawo sojojin ba, sai don su kare ɗalibai da malamai daga duk wani cikas. Amma abin mamaki shi ne, me ya sa aka kawo sojoji maimakon ’yan sanda ko Sibil Difens?” in ji shi.
Shugaban ASUP na kwalejin, Kwamared Kolo Joshua, ya tabbatar da komawar su yajin aiki, yana mai cewa gwamnati ta yi biris da haƙƙoƙin malaman.
“Shekaru biyu ke nan muna jurewa, amma yau malaman suna bin bashin watanni 18 na kuɗin ƙarin aiki.
“Duk da tattaunawa da saƙonni da muka aika, ba a ɗauki mataki ba. Sai ma aka dakatar da ƙungiya sannan aka fara tsoratar da shugabanninmu da tambayoyi. Wannan ya jefa malaman cikin rashin kuɗi da raguwar ƙwarin guiwa,” in ji shi.
Ya ce sai dai idan gwamnati ta biya hakkokin malamai da kuma ta koma kan tattaunawa ta gaskiya ne za a samu zaman lafiya a makarantar.
Wata sanarwa da Babban Sakataren Makarantar, Hussaini Mutammad Enagi, ya fitar, ta ce an dakatar da ayyukan ƙungiyar ne bisa dalilin “fargba da kuma rahoton tsaro mai tayar da hankali.”
Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Malam Abubakar Dzukogi, ya musanta cewa sojoji aka kawo.
“Na zagaya duk cibiyoyin jarrabawa, ban ga sojoji ba. ASUP ne kawai suka shiga yajin aiki, sai makaranta ta ci gaba da gudanar da jarrabawar. Wannan lamari na farar hula ne, ba na soja ba,” in ji shi.