Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote
Published: 11th, July 2025 GMT
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce yana da shakku a kan ko matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya za su ƙara aiki a nan gaba.
Najeriya dai na da matatun mai guda hudu mallakinta a biranen Fatakwal da Warri da Kaduna.
Amma attajirin ya ce matatun man waɗanda ke ƙarƙashin kulawar Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), sun laƙume sama da Dalar Amurka biliyan 18 wajen gyaransu, amma har yanzu sun ƙi aiki.
Ɗangote ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin shugabannin kamfanoni wadanda ke Karatu a Lagos Business School, a rangadinsu a matatar Dangote da ke Legas.
Ya ce matatar man shi mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kullum yanzu kusan kaso 50 na aikinta a kan tace man fetur ne, yana mai cewa hatta matatun man gwamnati kaso 22 na karfinsu suke sakawa a harkar tace man fetur ɗin.
A cewar attajirin na Afirka, “Mun taɓa sayen matatun man Najeriya daga hannun tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a watan Janairun 2007.
“Amma lokacin da marigayi Shugaban Kasa Umaru Yar’aduwa ya zo, tsofaffin manajojin matatun sai suka ce masa an sayar da matatun a ƙasa da ainihin ƙimar su a kasuwa, Obasanjo ya ba mu kamar kyauta ne kawai lokacin da zai tafi. Dole sai da muka mayar da su saboda an samu canjin gwamnati.
“A lokacin, manajojin matatun sun shaida wa Yar’aduwa cewa matsayin za su tashi, kawai ƙanin kyauta Obasanjo ya ba mu lokacin da zai tafi.
“Yanzu haka maganar da ake yi, an kashe sama da Dala biliyan 18 wajen gyaran su, amma har yanzu ba sa aiki. Kuma ba na tunani, ina da kokwanto a kan yiwuwar sake aikinsu a nan gaba,” in ji shi.
Dnagote ya kwatanta ƙoƙarin da ake yi na gyara matatun da na mutumin da ke kokarin zamanantar da motar da ya saya sama da shekaru 40 da suka wuce ne, alhalin zamani ya riga ya wuce wajen.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp