Gwamnatin Mauritaniya Ta Karyata Rahoton Cewa Shugaban Kasarta Ya Gana Da Netanyahu
Published: 12th, July 2025 GMT
Gwamantin kasar Mauritaniya ta musanta cewa shugabanta ya gana da Netanyahu, ta yi kira ga tashar Al Arabiya da ta tabbatar da sahihancin rahoton kafin watsa shi
Ministan al’adu da sadarwa na Mauritaniya kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Hussein Ould Maddou ya musanta sahihancin rahotannin ganawar da ake zargin shugaban kasar Mauritaniya da Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Kamfanin dillancin labaran Jamus ya nakalto ministan na cewa rahoton da tashar Al Arabiya ta watsa game da ganawar da ake zargin shugaba Mohamed Ould Ghazouani da Fira ministan Igwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba shi da tushe balle makama.
Ya yi nuni da cewa, labaran ba su da inganci, inda ya yi kira ga tashar Al-Arabiya da ta kasance mai gaskiya wajen samun bayanai tare da kaucewa yada labaran karya.
Kakakin gwamnatin ya kuma jaddada cewa: Daya daga cikin muhimman ayyuka na sana’ar jarida shi ne dogaro da majiyoyin hukuma, musamman idan aka yi la’akari da budi da saukin da ake baiwa wadannan majiyoyi manyan a tsakanin kafafen yada labarai masu neman sahihan bayanai.
Shugaban Mauritaniya ya halarci taron hadin gwiwa tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da wasu shugabannin Afirka biyar kan hadin gwiwar tattalin arziki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
2027: Takarar Shugaban Kasa Zan Yi Ba Mataimaki Ba – Peter Obi
An dai yi ta tsokaci kan cewa ko Obi zai amince da mukamin mataimakin shugaban kasa tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kamar yadda ya yi a 2019.
Obi ya ce, “Takarar shugaban kasan Nijeriya zan yi a 2027, kuma na tabbatar da cancanta.”
A kan ko zai hakura ya zama mataimakin takarar Atiku a 2027, Obi ya bayyana cewa, “Wannan abun wasa ba ne, babu wanta ya tattauna hakan. Mutane ne kawai yin irin wannan tunani. Amma a zahirin gaskiya babu wanda ya bayyana hakan.”
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya kuma jaddada cewa har yanzu yana shi mamba ne a jam’iyyar LP.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Obi yana daga cikin shahararrun mutane a cikin hadakar ADC da ‘yan adawar masu kokarin karbe mulki a wurin Shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC, wanda ke neman zarcewa a wa’adi na biyu a zaben 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp