Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana
Published: 22nd, July 2025 GMT
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara.
Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce a watan Yuni, yawan wadanda ba su da aiki a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, watau bai sauya ba daga yadda ya kasance shekara 1 da ya wuce.
Kasar Sin na da burin adadin marasa aikin yi ya tsaya kan kaso 5.5 a bana, tare da burin samar da guraben aikin yi sama da miliyan 12. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hisbah Ta Lalata Barasa Ta Naira Miliyan 5.8 A Jigawa
Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa.
Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnatiYa ce an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin shugaban hukumar da ke Kazaure, Mansur Dabuwa, inda aka lalata katan 400 na barasa da darajar kudinsu ya kai naira miliyan 5.8.
Ya bayyana cewa an kama barasa da aka kona a lokacin samamen da aka kai a sassa daban-daban a yankin.
Kwamandan wanda ya jaddada cewa an haramta shan barasa a duk sassan jihar, ya kuma kara da cewa hukumar za ta ci gaba da yaki da munanan dabi’u da suka hada da shan barasa.
Don haka hukumar ta Hisbah ta bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bai wa hukumar goyon baya da muhimman bayanai domin ta samu damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ya kuma shawarci mazauna garin da su daina aikata miyagun ayyuka da za su iya lalata tarbiyyar al’umma.