Qalibof: Asarorin HKI A Yakin Kwanaki 12 Yafi Abinda Ta Bayyana
Published: 11th, July 2025 GMT
shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibof ya bayyana cewa asarorin da HKI ta yi a yakin kwanaki 12 da JMI suna da yawa. Kuma babu shakka ya fi abinda ta bayyana.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a lokacinda yake hira da wata tashar talabijin a nan Tehran .
Qalibof ya ce yana da tabbacin cewa yahudawa akalla 500 suna halaka sanadiyyar hare-haren da sojojin Iran suka kai a kan HKI a yankin kwamaki 12. .
Ya ce sojojin yahudawan sun saba boye yawan mutanen da suka halaka a yake-yaken da take fafatawa da masu gwagwarmaya a yankin. suna kuma hana yada hutunan bidyo na asarorin da suka yi a yaki. masili daga cikin wasu da dama shi ne yadda suka hada yar rahoton tashar talabijin ta Aljazeera daukar hotuna a yakin saboda basa son muatane su san gaskiya. su kuma ga irin yawan asarorin da suka yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Hafsan Hafsoshin Sojin Iran Ya Ce: Iranta Dorawa Amurka Alhakin Duk Harin Da Ta Fuskanta
Kakakin hafsan hafsoshin sojojin Iran ya ce; Iran tana dora wa Amurka alhakin duk wani hari da za a kai mata
Kakakin hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Birgediya Janar Abul-fazl Shekarchi ya jaddada cewa: Iran tana dorawa Amurka alhakin duk wani harin wuce gona da iri da za a kaddamar kan kasarta.
A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen, Shekarchi ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran ba su ne suka kaddamar da harin kan wata kasa ba, amma sun mayar da martani cikin kwanaki 12 na arangama da munanan hare-hare da suka fuskanta daga mabartan ‘yan sahayoniyya makiya.
Ya kara da cewa, “An sanya wa makiya tsagaita bude wuta ne bayan da suka fuskanci munanan hare-hare daga sojojin Iran,” yana mai cewa, “Iran sakamakon karfin martanin sojojinta ne ta tilastawa makiya dakatar da yakin, ba kamar yadda suke ikirari ba, cewa su ne suka dakatar da yakin a kashin kansu, sannan kuma Iran ce karshen wacce ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka ciki kan mabarnata ‘yan sahayoniyya.”