Trump ya fitar da Amurka daga UNESCO saboda amincewa da Falasdinu a matsayin Mamba
Published: 23rd, July 2025 GMT
Amurka ta yanke shawarar ficewa daga hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a karo na biyu saboda matakin da ta dauka na shigar da Falasdinu a matsayin mamba.
Mataimakiyar sakatariyar yada labaran fadar White House Anna Kelly ta sanar da matakin a cikin wata sanarwa a ranar Talata.
Kelly ta ce dalilin da ya suka dauki wannan kan hukumar UNESCO, shi ne ta tallafa wa shirye-shiryen da Amurka ke kallonsu a matsayin wadanda ba su dace da muradunta ba.
“Shugaba Trump ya yanke shawarar janye Amurka daga UNESCO, wadda ke kula da ayyuka a bangaren raya al’adu da ilimi da zamantakewar al’umma, saboda daukar wau matakai wadanda ba su dace da manufofin Amurka ba,” in ji Kelly.
Ta ci gaba da cewa, shigar da Falasdinu a matsayin mamba a hukumar UNESCO, Amurka na Kallon hakan a matsayin babbar matsala kuma ya saba wa manufofin Amurka, wanda hakan ke ke kara haifar da karuwar kalaman kyama ga Isra’ila a cikin kungiyar.
Darakta-janar na UNESCO, Audrey Azoulay, ya bayyana matukar Rashin jin dadinsa kan matakin da Trump ya dauka na ficewa daga kungiyar, amma ya kara da cewa dama tuni aka yi hasashen haka, kuma UNESCO ta shirya ma hakan, tare da yin nuni da cewa hukumar ta dauki matakin karkata hanyoyin samar da kudadenta, inda kusan kashi 8% na kasafin kudin ta ke fiowa daga Washington.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne
Jami’in harkar shari’ar kasa da kasa ya bayyana cewa: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhu
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya ce: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne, kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.
A yayin wani taron manema labarai da ya yi da wakilan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya fiye da 110 a birnin New York na kasar Amurka a jiya Litinin, Gharibabadi ya bayyana ma’auni na wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauka kan yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma sakamakonsa ga zaman lafiya da tsaro a duniya.
Ya dauki gwamnatin yahudawan sahayoniya a matsayin babbar mai haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a yankin cikin shekaru 80 da suka gabata, yana mai jaddada cewa: Wannan ita ce gwamnatin da ya zuwa yanzu ta aiwatar da ayyukan ta’addanci sama da 3,000, tare da raba Falasdinawa sama da miliyan bakwai da muhallansu, da kashe dubban daruruwan Falasdinawa, tare da kame Falasdinawa sama da miliyan guda.