Aminiya:
2025-10-15@12:20:49 GMT

Matsalar tsaro na raguwa, tattalin arziƙi na farfaɗowa — Sanata Adaramodu

Published: 13th, July 2025 GMT

Sanata Yemi Adaramodu, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, ya ce matsalar tsaro a Najeriya na raguwa, kuma tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa.

Ya yaba da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda.

Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka

“Sojoji suna ƙoƙari saboda muna ba su isasshen kuɗi don siyan makamai da kula da jin daɗinsu.

Yanzu matsalar ’yan bindiga ta ragu a wasu jihohi, kuma ana magance ta.”

Ya ƙara da cewa satar mutane ta ragu: “A da, mutane ba sa iya bacci saboda tsoro. Amma yanzu abubuwa sun ɗan gyaru. Sai dai waɗanda za su sa siyasa ne ba su yadda da hakan ba.”

A ɓangaren tattalin arziƙi kuwa, Adaramodu ya ce ana samun ci gaba kamar ƙarin fita da kayayyaki sama da shigowa da su kamar yadda aka saba a baya.

“A karon farko cikin shekaru, muna fitar da kaya sama da abin da muke shigowa da su. Yanzu muna fitar da gangar ɗanyen mai miliyan biyu a rana.”

Ya kuma bayyana cewa an biya wasu manyan basuka da ake bin Najeriya.

“IMF sun tabbatar min biya bashin da ya kai kimanin Naira tiriliyan huɗu. Yanzu mun kashe kashi 63 kacal don biyan bashi, ba 97 kamar yadda aka saba ba.”

Sai dai ya amince cewa mutane ba su fara ganin sauyin tattalin arziƙi ba tukunna.

“Kamar marar lafiya ne da aka fara yi masa magani sai an ɗan jima kafin ya warke. Haka ma tattalin arziƙinmu ke buƙatar lokaci.”

Ya ce yanzu gwamnatin ba ta ciwo bashi sai don yin ayyuka masu muhimmanci.

“Majalisa ba za ta amince da bashi ba sai an bayyana ainihin abin da za a yi da shi, kamar tituna ko ayyukan jin-kai.”

Adaramodu, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ƙara hakuri kafin su fara sharɓar romon tattalin arziƙi.

“Tattalin arziki yana farfaɗowa. Ba da daɗewa ba mutane za su fara ganin sauyi.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Mai Magana Da Yawun Majalisar Dattawa Tattalin Arziƙi Tsaro tattalin arziƙi

এছাড়াও পড়ুন:

ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.

Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro

Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.

ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.

A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.

Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.

Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.

Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya
  • Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato
  • Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya Abdullahi
  • Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan
  • Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu
  • ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
  • Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?