Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Published: 22nd, July 2025 GMT
Ya ce PDP ce kaɗai ke da ƙarfin gina ƙasa.
“Wannan gwamnati ce da ke cewa mutane su yi azumi alhali su suna cin abinci sannan suna jin daɗi. Babu ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa ko wata jam’iyya mai jin zafin halin da mutane ke ciki da za ta goyi bayan Tinubu a 2027. Gwamnatinsa kasuwanci ne mara riba,” in ji Ologunagba.
Kakakin PDP ya kuma nuna damuwa kan halin rashin tsaro, inda ya ambaci kisan gillar da aka yi wa mutane a Jihar Filato da kuma hari kan ɗan takarar PDP daga Anambra a Abuja, a matsayin alamu cewa rashin tsaro ya zama ruwan dare.
Ya ce ƙarfin PDP yana hannun talakawa, ba sai da manyan ’yan siyasa ba.
“Karfinmu yana hannun jama’a. Ko da wasu manya sun fice daga jam’iyya, talakawa suna tare da mu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen $21bn a ƙetare
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta karɓo bashin ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatarwa da cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026.
Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more rayuwa, da tsaro, da noma da kuma gina ɗan Adam.
UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDCShugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan basussukan cikin gida da na waje, Sanata Aliyu Wamako ne ya gabatar da rahoton karbar bashin yayin zaman majalisar a yau Talata.
Sanata Wamakko wanda yake wakiltar shiyyar Sakkwato ta Arewa a zauren majalisar, ya ce an jinkirta amincewar rahoton ne saboda hutu na majalisa da kuma jinkiri wajen samun takardun daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO).
Shugaban kwamitin kasafi, Sanata Olamilekan Solomon, ya ce bayyana cewa sahale wa shugaban kasar karbo rancen yana kan tsarin da doka ta bayar da dama kuma tuni an riga an haɗa bashin cikin tsare-tsaren kasafin kuɗi.
Shi ma takwaransa mai wakiltar shiyyar Neja ta Gabas, Sanata Sani Musa, ya bayyana cewa wannan shiri ba na shekara ɗaya ba ne, amma zai shafi rabon kuɗi na tsawon shekara shida, yana mai jaddada cewa Nijeriya ba ta taɓa gazawa wajen biyan bashinta ba.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin bankuna da harkokin kuɗi, Sanata Adetokunbo Abiru mai wakiltar shiyyar Legas ta Gabas, ya tabbatar da cewa karbo rancen ya yi daidai da ƙa’idojin dokar kula da bashi da ta ɗabi’un da suka dace da dokar kuɗi.
Sai dai Sanata Abdul Ningi mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Tsakiya ya nuna damuwa game da ƙarancin bayanai kan yadda za a raba bashin da kuma hanyoyin da za a biya su.
Ya nemi a bayyana adadin da kowace jiha ko hukuma za ta samu, da kuma amfanin bashin domin a iya bayyana wa al’umma gaskiya.