Aminiya:
2025-11-02@18:11:14 GMT

Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC

Published: 22nd, July 2025 GMT

Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa yunwa na ƙara tsananta a Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa.

Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet

ICRC ta bayyana cewa fiye da mutum miliyan 3.7, wadanda galibi manoma ne na fuskantar barazanar matsanancin rashin abinci a yankin da aka shafe shekaru ana rikici.

Churi Ibrahim, wani tsohon manomi dan shekara 70 da ke ciyar da iyalinsa goma, ya ce farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi, kuma kudin ɗinki da yake samu da dare bai isansu.

Modu Umar, wani shugaban al’umma, ya bayyana cewa yunwa tana haddasa cututtuka kamar gudawa a cikin yara da manya saboda rashin abinci da magani.

“Mutane na fita nesa su tara itace domin samun kudin siyan abinci,” in ji shi.

ICRC dai ta ce ta fara wani shiri na taimaka wa noma ta hanyar raba iri da kayan aikin noma ga sama da iyalai 21,000 a bana, domin tallafa musu a lokutan kaka da rani.

“Ana kuma shirin rarraba famfunan ban-ruwa masu aiki da hasken rana domin noman rani,” in ji ƙungiyar ICRC.

Shugabar ofishin ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, ta ce ana fargabar za a fuskanci matsanancin ƙarancin abinci daga Yuli zuwa Satumba, inda mutane ke buƙatar sayen abinci, amma ƙarancin kudi yana hana su cika buƙata.

A cewarta, matsananciyar yunwar na janyo tsamurewar jiki saboda rashin abinci mai gina jiki musamman a tsakanin ƙananan yara ’yan ƙasa da shekaru biyar da kuma mata masu shayarwa.

Ƙungiyar ICRC na aiki a Borno tun 2012 inda take taimaka wa al’ummomin da rikici ya shafa da kuma kare martabar fararen hula bisa dokokin Geneva na 1949.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa maso Gabas jihar Borno Nijeriya yunwa

এছাড়াও পড়ুন:

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025 Wasanni Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?
  • Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC
  • Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu