2025-07-23@05:08:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1989
«ƙaramar sakandare»:
Kwamatin kananan hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya duba ayyukan raya kasa da karamar hukumar Kirikasamma ta samu nasarar gudanarwa daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya kafa kananan kwamitoci guda biyu domin samun nasarar tantance ayyukan a cikin garin Kirikasamma da kauyuka. Karamin Kwamati na daya bisa jagorancin...
Yau Talata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai na jerin taruka masu jigon “Kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”. Yayin taron, jami’in kungiyar nakasassu ta Sin ya bayyana cewa, yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, an kiyaye...
Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai...
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani...
Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga...
Jami’an tsaro sun hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ’yan rakiyarta shiga haramar Majalisar Dokoki ta Kasa, inda ta je da niyyar halartar zaman Majlasiar Dattawa a ranar Talata. Jami’an tsaro a daukacin kofofin shiga harabar majalisar sun hana ta shiga harabar majalisar ne a lokacin da ta yi yunkurin shiga domin halartar zaman ranar Talata,...
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin...
An wajabta wa ɗaliban makarantun firamare da Ƙaramar Sakandare mallakar lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) a Jihar Bauchi. Hukumar Kula da Ilimin Bai-ɗaya a Matakin Farko ta jihar (SUBEB) ce ta bayar da umarnin ta hannun shugabanta, Alhaji Adamu Mohammed Duguri. Ya bayyana cewa mallakar lambar NIN ta zama tilas lura da duk hukumomin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tashin farashin takin zamani yana hana manoma da dama noman wasu nau’ukan abinci. Manoma da dama sun ƙaurace wa noman masara da shinkafa da aka fi amfani da su a Najeriya sakamakon tsadar takin zamani, abin da masana ke ganin in ba a ɗauki mataki ba, hakan zai...
Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa yunwa na ƙara tsananta a Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe. A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa. Mutum 16...

Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yayin gudanar da taron manema labaru na yau da kullum da aka yi yau Litinin cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Tarayyar Turai EU. Kuma taron kolin kasar Sin da EU karo...
– Emmanuel Adegbola Aina – AIG na wucin gadi, sashen leƙen asiri – Omolara Ibidun Oloruntola – Hassan Abdu Yababet – CP, Kwalejin ‘Yan Sanda Jos – Bretet Emmanuel Simon – CP Jihar Taraba – Enyinnaya Inonachi Adiogu – CP, FCID, Gombe – Aminu Baba Raji – CP, FCID Alagbon – Mohammed Mu’azu Usman –...
A wani gagarumin mataki na karfafa yaki da rashin tsaro, gwamnatin jihar Zamfara ta gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Gusau, da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma kaddamar da sabbin dabarun yaki da ayyukan ta’addanci da masu aikata laifuka. Taron wanda aka gudanar a...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta nuna matukar gamsuwa tare da yabawa Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr Builder Muhammad Uba bisa kokarin sa na ayyukan raya kasa. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bude ofishin shugaban karamar hukumar da kuma dakin taro na karamar hukumar da aka gudanar a sakatariyar karamar...
Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ta ce ta ceto wani bene mai hawa biyu daga rugujewa gaba daya sakamakon wata gobara da ta tashi a garin Ilorin. Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda y ace gobara da ta tashi...
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zabi Hon. Kamilu Sa’idu (Wamban Kasuwar Daji) a matsayin dan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kaura Namoda ta Kudu da za a yi ranar 16 ga Agusta, 2025. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce Kamilu...
Ministocin tsaro na kasar Rasha ta JMI sun hadu a birnin Mosco don tattauna batun karfafa dangantakar tsaro a tsakaninsu a dai dai lokacinda al-amuran tsaro suke kara tabarbarewa a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar Iran a Mosco yana fadar haka. Kazem Jalali, ya bayyana cewa...
Sanata Yemi Adaramodu, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, ya ce matsalar tsaro a Najeriya na raguwa, kuma tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa. Ya yaba da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda. Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila WFP ya dakatar da tallafin abinci...
A bisa umarnin sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ, an yi nasarar gudanar da zaben majalisar jihar Zamfara a ranar Asabar din da ta gabata cikin kwanciyar hankali da lumana, inda aka dawo da dukkan mukamai ba tare da hamayya ba. Mukamin daya tilo da aka fara takaddama a kai ya sa daya...
Shugaba Trump da abokansa sun ce sun gano cewa ana tafka almundahana da zamba a hukumar. Rahoton na zuwa ne yayin da gomman shugabannin duniya ke taro a Birnin Sabeilla na kasar Sifaniya cikin makon nan domin tattauna batun katse tallafin, wanda ya fi kowane bayar da agaji a duniya. Bayan nazarin bayanan alkaluman tallafin...
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da lafta wa Tarayyar Turai da kuma Mexico harajin kashi 30 kan kayayyakin da ake shiga da su da su ƙasar daga ranar 1 ga Agusta. Bayanai sun ce ana ganin wannan matakin zai iya haddasa rikici mai tsanani tsakanin Amurka da biyu daga cikin manyan abokan kasuwancinta. An...
Ko za ka iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a Unguwar Adakawa cikin birnin Kano, na yi makarantar firamare a Adakawa, daga nan kuma na tafi zuwa makarantar sakandire (Gwammaja One), bayan na sauke Alkur’ani, daga baya na tafi sai na wuce zuwa ‘School of Health Technology’ ta Kano....

Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kama ‘Yan Leken Asirin Isra’ila A Lardin Mazandaran Na Kasar Iran
Dakarun juyin jaya halin Musulunci ta Iran sun kama wani wakilin hukumar leken asirin Isra’ila Mossad a arewacin kasar Iran Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanar da kame wani jami’in hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila “Mossad” a lardin Mazandaran (arewacin kasar Iran), wanda ke shirin kai harin ta’addanci a cikin kasar. Sanarwar...
Gwamantin kasar Mauritaniya ta musanta cewa shugabanta ya gana da Netanyahu, ta yi kira ga tashar Al Arabiya da ta tabbatar da sahihancin rahoton kafin watsa shi Ministan al’adu da sadarwa na Mauritaniya kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Hussein Ould Maddou ya musanta sahihancin rahotannin ganawar da ake zargin shugaban kasar Mauritaniya da...
Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗaukar musu. Waɗannan alƙawura sun haɗa da ƙarin albashi, biyan bashin da suke bi, da kuma barin jami’ar ta riƙa gudanar da harkokinta da ƙashin kanta. Lakurawa sun kashe ’yan...
Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗaukar musu. Waɗannan alƙawura sun haɗa da ƙarin albashi, biyan bashin da suke bi, da kuma barin jami’ar ta riƙa gudanar da harkokinta da ƙashin kanta. Lakurawa sun kashe ’yan...
Ali Mohammad Sabeghi, tsohon jami’in bangaren al-adu na ofishin jakadancin kasar Iran a kasar China ya karbi kyautar ‘Jakadan Abota’ na kasar China a wannan shekara ta 2025M. A bikin bada irin wannan kyauta karo na biyu. Labarin ya kara da cewa dangantaka tsakanin JMI ta kuma China yana daga cikin abota mafi kyau tsakanin...
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ja kunnen shuwagabannin kasashen yammacin Turai kan shiga yaki da kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Lavrov yana fadar haka, a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, labaran da suke isa kunnensa daga biranen Landan, Paris da kuma Berlin sun tabbatar...
Ana zargin wani direban tirela ya gudu da buhunan masara 463 da aka aike shi da su, bayan da ya bai wa ɗan rakiyarsa guba a cikin shayi a yankin Maraban Jos da ke Jihar Kaduna. Wani ɗan kasuwa da ke safarar hatsi daga Jihar Kano zuwa kamfanoni a sassa daban-daban na Nijeriya, Injiniya Jamilu...
Har ila yau, manufar ita ce; don rage yawan asarar da manoma ke tabkawa, bayan sun yi girbin farko da kuma jawo hankalin matasan kasar, domin su rungumi aikin na noma; musamman wanda za su yi, su samu riba. Kaddamar da Taraktocin na zuwa ne, daidai da lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar...

Magance Matsalar Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta: Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyarwa A Makarantun Jihar
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, ƙaddama da shirin na nuni da ƙwazon gwamnatinsa na yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin aiwatar da dabaru daban-daban na ƙara yawan ɗalibai a makarantun jihar Zamfara. Ya ci gaba da cewa, “Alƙawarinmu na yin garambawul ya haɗa da tsare-tsare na yaƙi da...

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Alaƙanta Shettima Da Kwatanta Jonathan Da Tinubu Kan Batun Tsige Gwamna
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yunƙurin da aka yi na haɗa waɗannan maganganun da abubuwan da suka faru a Jihar Ribas, musamman batun dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ayyana dokar ta-baci, fassara ce da aka yi ta ba daidai ba, ko kuma suka ne ga kundin tsarin mulkin ƙasa. “Domin kaucewa ruɗani, Shugaba Tinubu...
Kididdigar ta nuna cewa maimakon amfani da wannan kudaden shigar don rage basussuka, wasu jihohi suna kara amso bashin. Jihar Ribas ta zama ta farko a jerin jihohin da adadin bashin cikin gida na naira biliyan 364.39 a wata uku na farkon 2025, mafi girma tsakanin jihohi 10. Basukan Jihar Inugu sun tashi daga naira...
A nata bangaren, Mrs. Adeniji ta bayyana cewa akwai yawaitar yara marasa zuwa makaranta a ƙananan hukumomi 14 na jihar, tare da tabbatar da cewa ta hanyar wannan shirin zai taimakawa ɓangaren ilimi a jihar Zamfara. “Muna aiki tare domin tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari s baya,” Cewar ta. Daga...
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka raba sun haɗa da irin shinkafa kilogiram 34,800, irin masara kilogiram 80,000, da lita 23,740 na maganin ciyawa, lita 11,735 na maganin kwari, da buhunan sinadarai na gyaran iri 23,470. A yayin jawabin maddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon takin zamani kyauta na nuni...
Kamfanonin inshora za su kauracewa jiragen ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda tsoron fuskantar hare-haren Yemen Jiragen ruwan da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila za su fuskanci kaurace daga kamfanonin inshora, sakamakon munanan hare-haren baya-bayan nan da sojojin Yemen suka kai kan jiragen Magic Seas da Eternity Sea, wadanda...
A daya bangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; wadanda labarai a kansu babu dadin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, wadanda galibi labaransu marasa dadi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da...
Dantsoho ya kara da cewa, nuna kwarewar ma’aikata na kara taimaka wa, wajen cimma burin da aka sanya a gaba, musamman a bangaren nuna yin gasa, a tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa. “Ta irin wannan hanyar ce, za mu iya cimma bukatar da muke da ita da kuma cika muradin masu ruwa da tsaki, da...
An tsara Jirgin zai rinka yin zirga-zirga ne, zuwa daukacin kasashen da ke Afirka ta yamma da kuma sama da haka, musamman yin zirga-zirga daga Nijeriya zuwa kasashen, Jamhiriyar Benin, Togo, Ghana, Kamaru, Sierra Leone, Ibory Coast, Masar, Afirka ta Kudu da sauransu, tare da kuma nuna bukatar yin kasuwanci wadda tuni, aka fara ta....
Mai taimaka wa Sarkin Bayero kan harkokin yada labarai, Khalid Uba, ya shaida wa LEADERSHIP cewa magoya bayan Sarkin Bayero ba su da makamai. Uba, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin tawagar Sarkin Bayero da ke dauke da wani makami, sai dai an tilasta...
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa, sun kai hare-hare da makamai masu linzami ka tashar jiragen sama na Ben gurion kuma zasu...
Hukumomin tsaron uku su ne, na DIA, DSS da kuma NIA, inda kuma dokar, ta bayar da damar kafa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro wato ONSA, wadda a baya, ake kiran ofishin da Babban Jami’in Tsaro na Kasa wato CONS. Wannan Jaridar, na nuna matukar damauwarta kan ci gaba da...
Rahotanni na cewa ’yan fashin daji masu yawan gaske ne aka tabbatar da kashewa a wani kwanton ɓauna da sojoji suka yi musu a ranar Laraba a jihohin Zamfara da Kebbi. Sojojin ƙasa da na sama sun yi amfanin da bayanan sirri wajen buɗe wuta kan ayarin ’yan fashin da ke kan ɗaruruwan babura suna...
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya ta buƙaci Majalisar Tarayyar da ta amince da ƙudirin dokar da zai ba ta damar bincikar ɗaiɗaikun ’yan Najeriya game da yadda suka tara dukiyarsu. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito Shugaban EFCC, Ola Olukayode yana cewa ƙudirin mai suna...
An tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, tare da ƙona gidaje sama da 100, wanda ake zargin wasu makiyaya ne a unguwannin manoma da ke Ƙaramar hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba suka yi. An kai wa mazauna unguwar Bandawa Gwenzu, waɗanda suka haɗa da: Gwenzu da Langwanshin da Danzhan hari a daren Laraba. Kwastam ta...
A wani ɓangare na bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Afirka, Shugaban Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mr. Ola Olukoyede, ya yi gargaɗi kan barazanar da ke ƙara ƙamari na damfara ta hanyar kuɗaɗen zamani da kuma zuba jari na bogi a Najeriya da sauran sassan nahiyar. Mr. Olukoyede ya...
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin...
Kotun Ƙoli ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo. Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi biyo bayan zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024. Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Tinubu ne ya...
Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya. A wata ganawa...
Wani manazarci na Amurka ya bayyana sansanonin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Iran ta kaiwa hare-hare Wani manazarci Ba’amurke ya tattara jerin sansanonin da Iran ta kai wa hare-harer a wata makala inda ya bayyana cewa: Iran ta samu nasara a yakin da ta yi da ‘yan sahayoniyya. Wani mai sharhi kan harkokin siyasa da...