Kungiyoyin kare hakkin dan’adam suna yin tir da takunkumin da Amurka ta kakaba wa Francesca Albanese wacce it ace jami’ar MDD mai kula da hakkokin bil’adam a Falasdinu.

Shugaban cibiyar siyasar kasa da kasa da ta shafi hukumomi Dylan Williams ya bayyana takunkumin da cewa; Yana nuni da da halayyar gwamnatin ‘yan daba’.

Ita kuwa shugabar kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa “Amnesty International” Agnès Callamard kira ta yi ga gwamnatocin duniya da dukkanin masu bakin fada da su ka yi Imani da aiki da dokokin kasa da kasa da su yi duk abinda za su iya, domin ganin an hana takunkumin yin tasiri akan ayyukan Francesca Albanese, da kuma bayar da kariya ga dukkanin aikin hukumar ta kare hakkin dan’adam da kare ‘yancinsu.”

A jiya Laraba ne dai Amurka ta kakaba takunkumi akan Francesca Albanese saboda ta soki yakin da  Isra’ila take yi a Gaza.

Ministan harkokin wajen Amurka Marco Rubio ne ya bayyana cewa: “A yau ina mai sanar da kakaba takunkumi na musamman akan jami’ar kula da hakkin dan’adam ta MDD Francesca Albanese, saboda ayyukan da take yi da su ka saba doka na Sanya kotun manyan laifuka ta duniya daukar matakan da suke cin karo da doka aakn kamfanoni da jami’ai na Amurka da Isra’ila.”

Francesca Albanese ta mayar da martani a sahfinta na X cewa: A cikin karsashi da gamsuwa, zan kasance a tare da adalci, kamar kowane lokaci.”

A wani rahoto da ta fitar jami’ar kare hakkin bil’adaman ta MDD ta zargi manyan  kamfanonin  fasahar zamani  fiye da 60 da masu kera makamai da suke taimakawa ‘yan share wauri zauna a Isra’ila da kuma yakin da suke yi a Gaza. Haka nan kuma ta yi kira ga wadannan kamfanonin da su dakatar da taimakawa Isra’ila da suke yi, sannan kuma ta bukaci ganin an hukunta manajojin wadannan kamfunan saboda keta dokokin kasa da kasa da suke yi.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Francesca Albanese kare hakkin

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

 

Ya ce barazanar kakaba karin haraji ba hanya ce da ta dace ta hulda da Sin ba, yana mai nanata cewa, kasar Sin ba ta sauya matsayarta kan batun yakin cinikayya ba, wato ba ta son hakan, amma kuma ba ta tsoro. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje October 12, 2025 Daga Birnin Sin Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace October 12, 2025 Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Cirar kudin kwastoma: Majalisa ta gayyaci CBN da bankuna
  • Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata
  • Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa
  • Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa
  • Matakan Da Sin Ta Dauka Na Mai Da Martani Ga Bincike Mai Lamba “301” Da Amurka Ta Gudanar Sun Zama Wajibi Don Kare Hakkinta
  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon
  • An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Ka Tattauna Batun Falasdinu