Ministan Tsaron Iran ya bayyana cewa: Hare-haren da Iran ta kai ne suka tilasta wa gwamnatin mamayar Isra’ila daukan matakin tsagaita bude wuta

Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewa: Munanan hare-haren da sojojin kasar Iran suka kaddamar a matsayin mayar da martani ga yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita bude wuta.

A wata tattaunawa ta wayar tarho guda biyu da ya yi da ministocin tsaron Venezuela da Armeniya, Birgediya Janar Nasirzadeh na rundunar sojin sama ya jaddada cewa: Hare-haren da sojojin Iran suka kaddamar kan yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita wuta.

Ministan tsaron na Iran ya kara da cewa: Sojojin kasar Iran sun shirya tsaf domin mayar da martani ga duk wani yunkuri ko wauta daga ‘yan sahayoniyya da masu mara musu baya a cikin yanayi mai raɗaɗi da nadama.

Ya ci gaba da cewa: Hare-haren da yahudawan sahayoniyya suka kai a lokacin tattaunawa da Amurka wani karin shaida ne na rashin dogaro da Amurka da kasashen yamma.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kasar Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Kasar Yemen

Kakakin ma’aikatar harkokin  wajen kasar Iran Isma’el Baka’e ya yi allawadai da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai kan wasu yankuna a kasar Yemen a ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya litinin ya kuma yi tir da hare-hare kan a Hudaydah, Ras-Isa, as-Salif da kuma tashar wutan lantarki na Ras al-Kathib.

Har’ila yau Baka’ee ya yi allawadai da kai hare-hare kan cibiyar tattalin arziki na kasar ta Yemen a Hudaida, wadanda suka hada da kayakin jama’a wadanda suka hada da gadoji da hanyoyiu da tashar Jiragen sama, da tashar jiragen ruwa da kuma rumbunan ajiyar abinci. Wandanda gaba dayansu yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Hare-harin ranar Lahadi  dai sune na farko bayan kimani wata guda, sannan sun zo ne bayan da yahudawan suke ce wai sun kakkabo dukkan makamai masu linzami wadanda sojojin kasar Yemen suke kaiwa kan HKI.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci  ya Bayyana Yadda Iran Da Mayar Da Martani Mai Gauni Kan Isra’ila
  • Babban Kwamandan Sojin Iran Ya Bayyana Cewa Iran Ta Koyawa Gwamnatin Isra’ila Hankali
  • Manazaecin Kasar Amurka Ya Ce; Isra’ila Ta Sha Kashi A  Yakinta Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu
  • Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Amince Iran ta Kai Hare-Hare Kan cibiyoyin Sojojinta Guda Biyar
  • Za A Horas Da Jami’an Tsaron Sakkwato, Kaduna Da Benue Sabbin Dabarun Aiki
  • Kakakin Rundunar Izzuddeen Qassam ya Bayyana Yadda Suka Yi Kofar Rago Ga Sojojin Mamayar Isra’ila
  • Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Kasar Yemen