Wang Yi Ya Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Published: 11th, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana a yau Juma’a da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a Kuala Lumpur na Malaysia, inda suka yi musayar ra’ayi kan danganatkar Sin da Amurka da batutuwan dake jan hankalin kasashensu.
Wang Yi ya yi cikakken bayani kan matsayar Sin game da raya dangantakarta da Amurka, yana mai nanata bukatar bangarorin biyu su aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen suka cimma zuwa manufofi da ayyuka na hakika.
Bangarorin biyu sun amince cewa, ganawar ta su ta yi ma’ana, kuma za su karfafa hanyoyin diplomasiyya na tuntubar juna da tattaunawa a dukkan matakai da bangarori, da ba sassan diplomasiyya masu kula da raya dangantakar kasashen biyu damar taka rawar da ta kamata da lalubo bangarorin fadada hadin gwiwarsu yayin da suke hakuri da bambance-bambancen dake tsakaninsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza
Amma yanzu, sabon tsarin ya rage wa’adin bizar zuwa wata uku kacal, kuma mutum zai iya shiga sau ɗaya ne kawai da ita.
Ma’aikatar ta ce wannan mataki yana daga cikin gyaran tsarin alaƙar diflomasiyya da tsaro da Amurka ke yi da sauran ƙasashe.
Sai dai ta bayyana cewa za a iya sauya wannan tsari a nan gaba, idan an samu canji a dangantakar diflomasiyya, tsaro ko dokokin shiga ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp