Kakakin ma’aikatar sharia a nan Iran ya bayyana cewa shi bai da wata masaniya dangeneda cewa HKI ta kai hare-hare kan gidan yarin Evin na Tehran ne don kashe ma’aikatanta da aka kama aka kuma tsare a gidan yarin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin na ma’aikatar sharia yana fadar haka a nan Tehran ya kuma kara da cewa, a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata jami’an tsaron kasar Iran sun kama ma’aikatan leken asirin na HKI da dama a lokacin, suna aikawa Haramtacciyar kasar Rahotanni a cikin yakin.

A lokacinda aka tambayeshi kan cewa kun gano cewa hare-haren ranar 22 ga watan Yunin da ya gabata a cikin yakin kwanaki 12, HKI ta kai wadannan hare hare kan Evin ne don halaka wadan nan ma’aikata saboda kada su fallasa aspirant? Asghar Jahangir, y ace bai da masaniya kan hakan, amma kuma dukkan ma’aikatan leken Asirin HKI da aka kama , a lokacin yakin 12  ba wanda ya ji ciwo ko aka kashe.

Asghar Jahangir ba bukaci bukaci manya-manyan kungiyoyin da abin ya shafa sun yi All..wadai da kissan fursinoni da jami’ai masu kula da gidajen yari da kuma kashe mutanen da suka ziyarar yanuwansu da suke tsare. Mutane akalla 71 ne HKI ta kashe a hare-haren.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka

Wani sojan Ƙasar Amurka ɗan asalin Jihar Kano, Suleiman Isah, wanda yake aiki a rundunar sojin Amurka, ya ce ba zai yaƙi da ƙasarsa ta haihuwa ba saboda yaɗa labaran ƙarya game da yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.

Isah, wanda ya shiga rundunar sojin Amurka shekaru biyu da suka gabata, yana aiki ne da rundunar California Army National Guard, mai dakaru sama da 18,000.

Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda Aminiya ta tabbatar, Isah ya mayar da martani kan jita-jitar cewa Amurka za ta ɗauki matakin yaƙi a kan Najeriya saboda zargin yi wa Kiristoci kisan gilla.

Ya bayyana cewa ba zai taɓa amfani da makami a kan mutanensa ba.

“Ba zan shiga Najeriya na kashe iyayena ba saboda ƙaryar cewa ana kashe Kiristoci,” in ji shi.

Ya ce duk da yake yana Allah-wadai da kashe-kashe da tashin hankali, bai kamata matsalar tsaro a Najeriya a danganta da wani addini ba.

“Ba zan ƙaryata batun kisan Kiristoci da Musulmai ba,” in ji shi.

“Shekau, Bello Turji, Dogo Gide da sauransu ba suna kai wa wani addini ɗaya hari ba ne kaɗai.”

Maganganun Isah na zuwa ne daidai lokacin Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi a kan Najeriya.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa matsalar tsaro a Najeriya ba ta addini ba ce, inda ta ce matsalar na shafar Musulmai da Kiristoci baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano