Taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adama, wanda aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga watan nan, mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya”, ya ja hankalin baki daga kasashe da yankuna 140 da suka hada da ‘yan siyasa da ministocin gwamnatoci da kuma wakilan bangarori daban daban, inda suka yi musayar ra’ayin tare da cimma matsaya a fannoni da yawa, da kuma fitar da sanarwar Beijing, bayan kammala taron.

Sanarwar ta bayyana cewa, mu’amalar wayewar kai muhimmin karfi ne wajen inganta ci gaban wayewar kan bil’adama da bunkasuwar zaman lafiyar duniya. Kuma ya kamata kasashe da kabilu daban-daban su tabbatar da mutunta juna, su ba juna goyon baya kan hanyoyi da tsarin samun ci gaba da suka zaba da kansu, da kiyaye bambancin al’adu, da inganta mu’amala, da tattaunawa, da zaman jituwa tsakanin wayewar kai daban-daban.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: wayewar kan

এছাড়াও পড়ুন:

Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu

Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan  sahayoniyya kan kasar Iran

Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren.

Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari.

A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a ranar talata mai taken “Hanyar Haramtacciyar kasar Isra’ila kan Iran: Abubuwan da za a samu a nan gaba,” Sajjadpour, yayin da yake magana kan halaye da matsayin Turai a yakin kwanaki 12 da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Iran, ya ce: “Turai na goyon bayan gwqwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila a kodayaushe, kuma shiru ko goyon bayan da wasu kasashen Turai suka yi kan zaluncin Isra’ila za su kasance da sun mummunar tasiri a cikin zukatan Iraniyawa.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • “Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai
  • Fahimtar Kyawun Bambance-Bambance Kyakkawar Hanya Ce Ta Wanzar Da Zaman Jituwa A Duniya
  • Mu’ammalar Al’adu Muhimmin Karfi Ne Na Ciyar Da Bunkasar Wayewar Kan Bil’adama Da Wanzar Da Zaman Lafiyar Duniya
  • Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam
  • An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing
  • An Fara Taron Nishan Karo Na 11 Game Da Wayewar Kai A Duniya
  • Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu
  • Rawar Ganin Da BRICS Ke Takawa Wajen Samar Wa Kasashe Masu Tasowa ‘Yanci A Tsarin Gudanar Da Harkokin Kasa Da Kasa
  • Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense