Iran Tana Nazarin Sakon Amurka Na Bukatar Farfado Da Tattaunawa Shirin Makamashin Nukliya Na kasar
Published: 12th, July 2025 GMT
Mai bawa jagoran Juyin Juya halin musulunci Imam Sayyid Ali Khamina’i, shawara Dr Ali Larijani ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana nazarin sakon gwamnatin Amurka na bukatar a farfado da tattaunawar shirin makamashin Nukliyar kasar tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Dr Larijana yana cewa gwamnatin kasar Iran tana shakkar Amurka a cikin duk abinda zai hada su musamman bayan yaki kwanaki 12 da ita Amurka da kuma HKI suka dora mata.
Dr Larijana ya fadawa tashar talabijin ta Aljazeera na kasar Qatar kan cewa, HKI da Amurka sun farwa kasar Iran da yaki ba tare da wani dalili ba, tana ma cikin tattaunawa da Ita kan shirin ta na makamas suka yi hakan. Suka kashe manya-manyan jami’an sojojin kasar da masana fasahar Nukliya da dama. Har’ila yau har da mutanen kasar Iran fararen hula suka kashe.
Ya ce HKI ta farwa yaki a ranar 13 watan Yunin shekara sannan amurka ta shiga a ranar 22 ga watan. Idan an hana wadannan duka da wasu da ban ambata ba, da sauki haka irin ba zata koma teburin tattaunawa ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NYT: Natanyahu Yana Tsawaita Yaki A Gaza Don Ci Gaba Da Kasancewa Kan Iko A HKI
Jaridar NYT ta kasar Amurka ta bayyana cewa firai ministan HKI Benyamin Natanyaho da gangan yake tsawita yaki a Gaza don tsawaita zamansa a kan kujerar shugabancin kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani binciken da Jaridar New York Times ta yi, inda take cewa Natanyahu ya san cewa matukar ya sauya matsayinsa na shugaban gwamnatin HKI to kuwa sammashin kamasi da kuma tuhume-tuhumen da ake masa zasu tashi wadanda zasu zama masa matsala, kuma a lokacin hatta gwamnatin Amurka ba zata iya yi masa wani taimako ba.
An fara yaki a Gaza ne a ranar 07 ga watan octoban shekara ta 2023 . daga lokacin ya zuwa yanzu sojojin Natanyahu sun kashe falasdinawa kimani 57,000. Sannan an jikata wasu fiye da 12000. Banda haka sun rusa fiye da kasha 90% na gaza. Sannan sun hana shiga abinci da ruwa har ya kaiga falasdinawa da dama sun mmutan saboda yuwan da rashin lafiya da wasu dalilai.