Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)
Published: 11th, July 2025 GMT
Ba laifi idan an yi murna ta shigar sabuwar shekarar Musulunci. Ba za a bi na wadanda za su bidi’antar da abin ba, domin hatta murnar haihuwar Manzon Allah (SAW) sun ce bidi’a ne. Har kai kanka ma za su iya ce maka bidi’a, saboda ba ka zo a zamaninsa ba.
Masu wannan fahimtar Malamai sun ce ba wai suna nufin a koma wa Sunnar Manzon Allah ba ne, suna so ne a koma wa zamanin Annabi (SAW), ka ga ke nan sai mu ajiye su motoci da sauran kayan kere-kere na fasaha sda ake amfani da su yanzu har da su lantarki da su jirgin sama duk a ajiye, a koma amfani da su rakuma da dawaki da jakuna.
Kur’anin da Allah ya saukar mana zamaninsa ba ya shudewa, ya dace da kowane irin zamani da ya zo, ko zai zo a nan gaba. Ayoyin da suka sauka suna nan suna mana hukunci, ba a kula da ko dan waye suka sauka, ko don me suka sauka, abin ya zama hukunci ga al’ummar Annabi duka tun daga wancan zamanin da aka saukar har zuwa tashin kiyama.
Misali ayar da ta ce, “ku sani, hakika Annabi yana cikinku”, wasu sai su ce da su Sayyidina Abubakar ake, ban da mu a zamanin nan. Alhali kuwa ba haka ba ne, duka Malamai na Allah sun fassara wannan da cewa Annabi (SAW) yana nan a cikin al’ummarsa har zuwa tashin kiyama. Idan kuwa masu wancan fahimtar suka dage sam sai an tsame Annabi ba ya tare da da al’ummarsa, sai mu ce, ke nan ayar da ta umurce mu mu kadaita Allah “ku yi sani babu abin bautawa da gaskiya sai Allah” da Sahabbai kawai ake yi. Kun ga ai babu wanda zai karbi wannan. To, haka shari’ar Manzon Allah take, ta dace da duk irin sauyin da za a samu na zamani.
Akwai hadisai da yawa da Annabi (SAW) yake so ya ga al’ummarsa tana cikin nishadi ba cikin kunci ba. Manzon Allah yana so ya ga Musulmi ya fita daban da saura kamar kitse a cikin nama, ya yi ado ya yi kyau. Don haka, za mu yi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, ba bidi’a ba ne, sunnah ce ta Manzon Allah, sunnah ce ta Khalifofinsa, Musulmi su yi murna su yi nishadi. Addini ba ya zo ne ya tattakure mutane ya hana su sakat ba, har ma a samu wasu suna barin addini zuwa wasu saboda takura, a uzu billahi. Irin haka ta faru a Ibadan, wasu Musulmi sun kawo kara wurin Shehu Ibrahim cewa matasansu suna zuwa coci saboda kidar da ake yi a can, Shehu ya ce musu to ku wa ya hana ku kidar? Ka ga dole (masu irin waccan fahimtar) su shiga karatu sosai a nan wurin (kafin su kai ga cewa kaza ya haramta, kaza ya halasta). Saboda haka a bar mutane su yi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, Sarkin Musulmi ya sanar, Malamai su yi bayani, al’ummar musulmi su taya juna murna, Alhamdu lillah.
Kamar yadda muka fada, yana daga cikin abin da ya sa Sahabbai ba su sanya farkon shekarar Musulunci a Rabi’ul Auwal ba don kar a hade manyan bukukuwanmu biyu a wuri daya, ga bikin haihuwar Annabi (SAW) ga kuma na shiga sabuwar shekara, kamar dai yadda Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu) ya hana a yi ramakon Ramadan a cikin goman farko na watan Zulhajji, don kar wani ya kwace wani, alhali kowannensu yana da girmansa da falalarsa. Don haka, a bar Mauludin Manzon Allah da girmansa da falalarsa, shi ma shiga sabuwar shekarar Musulunci a barshi da nashi.
Sannan me ya sa Sahabbai ba su kafa shekarar ta Musulunci da ranar da aka aiko Manzon Allah da Manzanci ba, sai dai Hijira?. Haka nan me ya sa ba su kafa da ranar da aka kammala saukar da Shari’ar Manzon Allah (SAW) ba, ko ranar Fatahu Makkata (ranar da aka bude Makka)? Sahabbai duk sun san da girma da falalar wadannan ranakun, amma duk idan aka hadasu, daya zai kwace wa daya.
Alheran da ke cikin falalar Hijira suna da yawa. Daga ciki shi ne ‘yan’uwatanka da Manzon Allah ya hada a tsakanin Muhajirai da Ansaru, mutanen Makka da masu masaukinsu na Madina. Haka nan da ‘yan’uwantaka a tsakanin su kansu Muhajiran, kamar yadda ya hada a tsakanin Sayyidina Hamza (RA), wanda yake Baffansa, Balarabe, Bakuraishe da kuma bawansa mai masa hidima Zaidu bin Harisata. Kuma saboda wannan ‘yan’uwantakar, Zaidu ya shiga cikin su Sayyidina Aliyu da wansa Ja’afaru bin Abiy Dalibi wajen neman a bashi rainon ‘yar Sayyidina Hamza wadda Manzon Allah ya taho da ita daga Makka lokacin da ya je ramuwar Umura.
Da aka tambaye shi me ya sa yake so a bashi rainonta, Zaidu ya ce saboda ‘yar dan’uwana ce. To daga baya dai Manzon Allah ya bai wa Ja’afar ita saboda bayan kasancewarta ‘yar Baffansa yana kuma aure da ‘yar’uwar mahaifiyarta. To, ka ga girman ‘yan’uwantaka ta Musulunci. Irin wannan ma ana gani kuru-kuru a tsakanin wadanda suka sha Faila, ‘yan’uwa su shaku da juna su zama uwa daya uba daya. Haka shauran Musulmi ma duk a yi kokari a zama haka. ‘Yan’uwantaka in ta faru, komai ya faru, idan soyayya ta samu komai ya samu.
Kafin Hijira, Manzon Allah (SAW) ya koya mana yadda za mu yi addini idan ka tsinci kanka a cikin wadanda ba musulmi ba kuma ba su yarda da Musulunci ba, kamar yadda ya rika yin sallah a Ka’aba duk kuwa da kasancewar daruruwan gumaka a ciki. Yana sallah yana kallon Ka’aba kuma da gumaka a ciki sannan bai ce zai cire ko daya ba, shi dai ya san Allah yake wa sallah ba gumaka ba. Haka nan ya koyar da yadda za a yi addini a wurin mutanen da za su barka ka yi addininka, amma ba su so ka kawo musu naka ka bata musu tsarinsu, kamar yadda Sahabbai suka yi a Habasha. Saboda kyawawan halayensu da wasu ‘yan garin suka gani suka musulunta bisa radin kansu. Don haka kar mutum ya yi ta fada ya ce dole sai ya sauya wa mutanen da yake cikinsu tsarinsu da suka yarda da shi.
Manzon Allah ya nuna mana zama a kasar da Musulmi sun fi yawa amma kuma akwai wadanda ba musulmi ba a ciki, kamar zaman Madina. Ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya da wadanda ba musulmin ba. A kare wa duk ‘yan kasa hakki bisa tsarin zamantakewarsu, duk abin da zai amfani kasa na kowa ne, haka nan duk abin da zai cuci kasa ya shafi kowa za a fito a yi taron dangi a kai. Haka aka zauna har sai da Yahudawa suka ha’inci Manzon Allah (SAW) ya kore wasu daga Madina wasu kuma aka kashesu. Kuma duk da wannan, Manzon Allah (SAW) saboda shi Annabin Rahama ne ya ba Yahudawan dama su zabi alkalin da zai musu hukuncin abin da suka yi, suka zabi Sa’adu bin Mu’azu.
Hukuncin da ya yanke kuma Manzon Allah (SAW) ya ce ya yi dai-dai da hukuncin da Allah ya yanke. Don haka, ko da wani zai ce ai Manzon Allah ya yanka Yahudawan Banu Kuraiza don ya samu kafar ta da rikici a kasa, sai a ce masa ba haka abin yake ba. Su Banu Kuraiza hukuncin da ya dace da su kenan a ka’idar duniya. Duk wanda ya ha’inci kasarsa ya hada kai da abokan gaba ana yaki hukuncin kisa ya hau kansa. Kuma ko waye ba Musulmi ba kawai irin hukuncin da zai yi kenan. Haka aka kori Banud Nadir da Banu Kainu Ka’a, Madina ta zama kasar Musulunci, Manzon Allah (SAW) shi ne shugaba mai shari’a da littafin Allah Alkur’ani. Duk dai abin da za mu koya mu yi aiki da shi ne zaman Manzon Allah a Makka, zaman Sahabbansa a Habasha da kuma zamansa a Madina (SAW). Wannan yana daga cikin albarkar Hijira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: sabuwar shekarar Musulunci Manzon Allah ya shiga sabuwar kamar yadda
এছাড়াও পড়ুন:
Asibitin Kula Da Masu Lalurar Ƙwaƙwalwa Na Kaduna Na Bunƙasa Ta Fannoni Daban-Daban
Asibitin Kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Kaduna na Jagorantar Sauye-Sauren Lafiyar ƙwaƙwalwa a Arewacin Najeriya — Farfesa Aishatu Armiya’u Ta Bayyana Muhimman Nasarori a Shugabanci da Ayyuka da Hadin Gwiwa
Shugabar gudanarwa kuma daraktar lafiya ta Asibitin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa dake Kaduna, Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u, ta tabbatar da kudirin asibitin na ci gaba da jagorantar gyaran tsarin kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, inda ta ce an samu gagarumin ci gaba wajen fafutukar manufofi, kara yawan ayyuka, da karfafa hadin gwiwa tsakanin sassa daban-daban a cikin shekaru uku da suka gabata.
Farfesa Armiya’u ta bayyana cewa horon da ta samu a shirye-shiryen shugabancin harkokin lafiya na Africa ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta salon shugabancinta da kare muradun lafiyar kwakwalwa, da kuma gina ƙwarewa a fannin.
Ta bayyana shirin a matsayin ginshiƙi wajen karfafa mata kwarewar tsara manufofi da aiwatar da gyare-gyaren tsarin lafiya.
Sauya Fasalin Babban Asibitin na kasa dake Kaduna
A matsayinta na shugabar daya daga cikin manyan asibitocin kula da lafiyar kwakwalwa guda goma na tarayyar Najeriya, Farfesa Armiya’u ta jagoranci sauye-sauren da suka mayar da Asibitin Kaduna cibiyar kula da lafiya ta tunani da jiki, bincike, da horas da kwararru a hanya mai dacewa da al’adu.
A karkashin jagorancinta, asibitin ya kafa dimbin yarjejeniyar hadin gwiwa da kungiyoyin cikin gida da na waje don bunkasa lafiyar kwakwalwa ga al’umma.
Daya daga cikin manyan hadin gwiwar ita ce wadda ake yi da Hukumar Rigakafin Shan Miyagun Kwayoyi da Kula da Lafiyar ƙwaƙwalwa ta Jihar Kaduna wadda ta taimaka wajen samun ci gaba sosai a bangaren manufofi da ayyuka a jihar.
Manyan Nasarorin Manufofi a Jihar Kaduna
Ta hanyar hadin gwiwa da KADSAMHSA, asibitin ya bada goyon bayan fasaha wajen tsara dokoki da tsarin aiki da ake amfani da su wajen sauya fasalin kula da lafiyar kwakwalwa a fadin jihar. Muhimman nasarorin sun hada da:
Sanya magungunan psychotropic a cikin Jerin Muhimman Magungunan Jihar Kaduna na 2025, wanda zai tabbatar da samunsu a cibiyoyin lafiya na matakin farko da na biyu.
Taimakawa wajen tabbatar da dokar Lafiyar ƙwaƙwalwa ta Jihar Kaduna, da amincewa da wata manufa da ke haɗa lafiyar kwakwalwa da cibiyoyin kiwon lafiya na al’umma.
Shirin horaswa da ya kara yawan aikace-aikacensu a fadin jihar, wanda ya bai wa ma’aikatan lafiya 165 horo a manyan asibitoci 15, ciki har da masu kula da samari masu dauke da cutar HIV.
Ta kuma ce asibitin yanzu yana da tsofaffin dalibai 10 na Africa CDC Mental Health Leadership Programme — waɗanda aka horar a Ibadan, Nairobi, da Cairo — kuma kowannensu yana jagorantar muhimman ayyukan gyara.
Inganta Walwalar Ma’aikata da Ingancin Ayyuka
Farfesa Armiya’u ta jaddada cewa jin dadin ma’aikata na daga cikin manyan abubuwan fifiko, inda aka kirkiro sababbin shirye-shiryen da ke inganta lafiyar jiki, tunani da zamantakewa.
Wadannan sun hada da makon lafiya na kowane kwata, wasanni, tarukan zamantakewa, da ingantaccen tsarin inshorar lafiya.
Asibitin ya kuma hade kula da lafiyar jiki cikin ayyukan lafiyar kwakwalwa, tare da kyautata muhalli domin karfafawa da rage wariya.
Wadannan matakai sun kai ga samun babban gamsuwa daga marasa lafiya, inda sama da kashi 90 cikin dari suka bayyana jin dadi da kulawar da suka samu.
Fadada Ayyuka Ta Hanyar Karin Hadin Gwiwa
Asibitin na kara fadada tasirinsa ta hanyar aiki tare da rundunar sojoji, cibiyoyin ilimi, kungiyoyin farar hula, da sauran abokan hulda.
Wadannan hadin gwiwar na taimakawa wajen ba da dama ga karin al’umma su samu kula da lafiyar kwakwalwa a Arewa, tare da karfafa kula da marasa lafiya a cikin al’umma.
Shirye-Shiryen Gaba: Kirkire-Kirkire da Kula da Al’umma
Dangane da makomar asibitin, Farfesa Armiya’u ta bayyana cewa za a kara karfafa tsarin kula da lafiyar kwakwalwa na al’umma, habaka bincike da kirkire-kirkire, fadada amfani da kayan aikin lafiyar kwakwalwa na dijital, da gina karfin ma’aikatan lafiya domin biyan bukatun al’umma da ke ta ci gaba da sauyawa.
Ta jaddada himmar gina tsarin lafiyar kwakwalwa mai tausayi, wanda ba ya takaituwa ga manyan cibiyoyi kawai, kuma ya dace da al’adu — wanda za a iya yada shi a fadin kasar.