Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da umarninsa ga sabbin kwamandojin da kansu a lokacin yakin baya-bayan nan

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, yayin da yake ishara da umarnin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar a yakin kwanaki 12 da aka kakabawa Iran, ya ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kasance a dakin kwamandoji sau biyu a lokacin yakin tare da bayar da umarninsa ga sabbin kwamandojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A wata hira da aka yi da shi ta gidan telebijin, Qalibaf ya kara da cewa kwamandojin da aka nada sa’o’i bayan fara kai hare-hare kan kasar Iran, kwararru ne da suka yi kama da tsararsu kwamandojin da suka yi shahada kuma suka shiga filin nan take.

Qalibaf ya jaddada cewa: Cikin sa’o’i kadan ne Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya samu nasarar kubutar da sojojin kasar daga irin firgicin da suka shiga na fuskantar hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan Iran.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Jagoran juyin juya halin Musulunci Musulunci ta Iran

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Yace Huldar kasar Iran Da IAEA Zai Ci Gaba Ne Idan Ta Daina Fuska Biyu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya fadawa shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa, kan cewa huldar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA zai kasance tare da sharudda. Saboda hukumar ta yi watsi da ayyukanta na asali ta koma siyasa. Ta fita daga bangaren kwararru ta zama tana bin bukatun wasu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar ta IAEA a da can ta zuciya guda ce, bata boyewa hukumar wani abu a cikin ayyukanta na makamashin Nukliya. Amma a halin yanzu mun gano cewa hukumar ce take bawa HKI bayanai dangane da ayyukammu na Nikliya ta kuma bada sunaye dadireshin masana fasahar Nukliya na kasar HKI ta zo ta kashesu kai tsaye ko kuma ta yi amfani da wakilanta a cikin Iran don yin wannan aikin.

Banda haka Hukumar ta rufe idanunta kan shirin makaman Nukliya na HKI gaba daya.  Daga karshe yace Iran zata sauya yadda take hulda da hukumar a lokaci guda tana bin hanyar diblomasiyya don warware matsalolin da suke rage tsakaninta na hukumar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah  Wadai Da Kakaba Takunkumi Kan Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya
  • Shugaban Kasar Iran Yace Huldar kasar Iran Da IAEA Zai Ci Gaba Ne Idan Ta Daina Fuska Biyu
  • Majalisar Limaman Turai Ta Nesanta Kanta Daga Wadanda Su Ka Ziyarci HKI
  • Kwamandan Sojin Iran Ya Jaddada Kare Kan Iyakokin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci  ya Bayyana Yadda Iran Da Mayar Da Martani Mai Gauni Kan Isra’ila
  • Babban Kwamandan Sojin Iran Ya Bayyana Cewa Iran Ta Koyawa Gwamnatin Isra’ila Hankali
  • Manazaecin Kasar Amurka Ya Ce; Isra’ila Ta Sha Kashi A  Yakinta Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba
  • Iran Ta Tabbatar Da Cewa Tana Iya Yakar Amurka Da HKI A Lokaci Guda