Wata Kungiyar Ta Bukaci Shugaban Kasa Ya Cika Alkwarin Marigayi Shugaba Buhari Game Da Shehu Usman Aliyu Shagari
Published: 22nd, July 2025 GMT
A wani roko da wata kungiya da aka fi sani da Sokoto Heritage Reloaded Initiative ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika alkawarin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a lokacin wata ziyarar aiki da ya kai a jihar.
An yi wannan roko ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a jihar Sokoto, inda shugaban kungiyar Farfesa Uthman Abdulqadir, ya jaddada muhimmancin girmama abubuwan da Shagari ya bari.
Ya tuna cewa shugaba Buhari ya yi wannan alkawari ne a ziyarar da ya kai Sokoto.
Farfesa Uthman ya bayyana irin rawar da Shehu Shagari yake takawa wajen ciyar da ilimi gaba a Najeriya, inda ya bayyana cewa ya taka rawa wajen aza harsashin kafa Budaddiyar Jami’ar Nijeriya.
Ya bayyana Shagari ba wai kawai shugaba ba, a’a a matsayin alama ce ta tawali’u, rikon amana da kishin kasa, mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa kasarsa hidima.
Farfesa Uthman ya bayyana kwarin guiwar cewa shugaba Tinubu, wanda ya shahara da mutunta shuwagabannin kasa da jajircewar hadin kai, zai gane muhimmancin tunawa Shehu Shagari.
Ya yi imanin cewa wannan aikin zai bayyana a fili karara Tinubu a matsayin jagora mai girmama kimar tawali’u, hidima, da kishin kasa.
Farfesa Uthman ya jaddada cewa sanyawa wurare sunayen Dattijai ba karamin alfanu ne ga rayuwa jama’ar ba.
Ya bayyana shi a matsayin muhimmin kayan aiki don ilimi, zaburarwa, da kuma kiyaye dabi’un da suka dace da al’ummomin yanzu da na gaba.
NASIR MALAL
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Shagari Farfesa Uthman
এছাড়াও পড়ুন:
Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
A yau, 17 ga watan Satumba, Shugaba Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa al’ummar jihar Ribas biyo bayan rashin jituwa da yaƙi ci yaƙi cinyewa da ya dabaibaye ɓangaren zartarwa da na dokokin jihar. Cikakken bayani na nan tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp