Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100
Published: 23rd, July 2025 GMT
Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi ta yanke hukunci a kan gwamnatin jihar Bauchi da ta biya tsohon Akanta-Janar na jihar, Dakta Sa’idu Abubakar, Naira miliyan 100 a matsayin diyyar take masa haƙƙi da kuma tsare shi ba bisa ƙa’ida ba. Kotun ta kuma umarci gwamnati ta wallafa ban haƙuri a manyan jaridu guda biyu cikin kwanaki 14.
Mai Shari’a Aminu Garba ya yanke wannan hukunci ne a ƙarar da Dakta Abubakar ya shigar, yana zargin gwamnati da jami’anta da take masa haƙƙi, da kama shi ba tare da bin ƙa’ida ba, da musgunawa. Ya bayyana cewa hakan ya saɓawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar kare haƙƙin bil’adama ta Afrika.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Ƴansanda Sun Kama Shahararren Ɗan Damfarar Yanar Gizo A BauchiWaɗanda kotun ta bayyana da laifi sun haɗa da shugaban ƴansanda na ƙasa, kwamishinan ƴansanda na Bauchi, gwamnatin jihar Bauchi, Antoni Janar na jihar da hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta jihar. Kotun ta tsame hukumar DSS daga cikin hukuncin, saboda babu isasshen hujja kan rawar da ta taka.
A ƙarshe, kotun ta hana duk wani ƙarin cin mutunci, tsarewa ko kama Dakta Abubakar ba tare da bin doka ba. Haka kuma ta jaddada cewa ya cancanci diyya saboda hana shi walwala da damuwa da aka jefa shi ciki daga ranar 9 zuwa 25 ga Disamba, 2024.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.