Fizishkiyan: Batun Kare Hakkin Bil’adama Ba Komai Ba Ne Sai Karya
Published: 22nd, July 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Batun kare hakkin bil’adama da ake yi a duniya ba komai ba ne sai karya.
Shugaba Fizishkiyan ya yi ishara da yadda masu ikirarin kare hakkin bil’adama suke sa kafafunsu suna take hakkin mutanen Gaza da cikin kasashen yammacin Asiya da kuma tafka manyan laifuka.
A yau Talata ne dai shugaban kasar ta Iran ya gabatar da jawabi a wurin bikin girmama shahidan kallafaffen yaki na kwanaki 12, ya bayyana cewa: “A cikin wannan duniyar wacce take riya ci gaba da wayewa, a gaba idon duniya, ake yanke wa mutanen Gaza ruwan sha da abinci, a hana mata da kananan yara. Haka nan kuma ake tafka laifukan da su ka kunshi kisan kiyashi, amma kuma wai su ne ke Magana akan kare hakkin bil’adama.”
Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce, masu yin Magana akan kare hakkin bil’adama din ne suke sa kafafunsu suna take shi.
Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce, HKI da Amurka, sun kawo hari bisa riya cewa Iran tana son kera makamin Nukiliya, kuma wadanda su ka kai wa harin mata ne, kananan yara da kuma sauraren hula da ba su da makamai.
Shugaban kasar ta Iran ya ambato hudubar da Imam Hussain ( a.s) ya yi wa abokan gabarsa a karbala cewa: “Idan ba ku da addini, to ku zama ‘yantattun a cikin harkokinku na duniyu.”
Shugaba Fizishkiyan ya kara da cewa: A wannan lokacin suna yanke abinici da ruwa ga mutanen Gaza, sannan kuma a lokaci daya suna Magana akan kare hakkin bil’adama. Wane annabi ko addinin Allah ne ya halarta tafka laifuka irin wannan ?
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shugaban kasar ta Iran ya kare hakkin bil adama
এছাড়াও পড়ুন:
Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom
Ya ce ya dinga ƙorafi ne domin gwamnatin Buhari ba ta ɗauki matakin da ya dace ba game da kashe-kashen da ake yi a Benuwe.
“Ba zan iya zama na yi shiru ina ci gaba da binne mutane ba. Dole ne na faɗi gaskiya,” in ji shi.
“Amma ban tsaya a magana kawai ba, gwamnatina ta kawo hanyoyin magance matsalar da muka ga za su taimaka.”
Ortom ya ƙara da cewa da gwamnatin Buhari ta karɓi shawararsa kuma ta yi aiki da ita, da matsalar tsaro a Benuwe ta ƙare.
Ya ce ya sha kokawa a lokacin, kuma shirye-shiryen da gwamnati ta kawo kamar Ruga ba su da amfani.
Ya ce ba wai rikici ne tsakanin makiyaya da manoma kawai ba, wasu daga cikin makiyaya suna kai wa ƙauyuka hari, suna kashe mutane, lalata gonaki, yi wa mata fyaɗe da aikata wasu laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp