HKI Ta Roki Amurka Ta Taimake Ta A Fada Da Kasar Yemen
Published: 11th, July 2025 GMT
Tashar talabijin din “Cane” ta HKI ta bukaci Amurka da ta kafa kawance mai fadi na kasashe domin fuskantar kasar Yemen.
A yayin ziyarar da Fira ministan HKI, Benjamin Netanyahu a Amurka ne dai ya bijiro da wannan bukatar, kamar yadda rahoton tashar talabijin din ta “Cane” ya ambata.
Rahoton ya kuma ce, Jami’an HKI sun sanar da Amurka cewa, ci gaba da hare-haren Yemen, ya tashi daga zama matsalarta ita kadai, don haka da akwai bukatar kai hare-hare na hadin gwiwa da Amurka da kuma shigar da kasashen wannan yankin da kuma wasu na duniya.
Tun daga 2023 ne sojojin Yemen suke kai wa jiragen ruwa na HKI hare-hare a cikin tekun “Red Sea” ko kuma wadanda su ka nufi tasoshinta na jirgin ruwa. Sojojin na Yemen dai sun sha bayyana cewa ba za su daina kai hare-haren ba har sai an kawo karshen yakin Gaza, da kuma dauke takunkuman da aka kakabawa yankin.
Shugaban kungiyar Ansarullah ta Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya sha bayyana matsayar kasar ta Yemen yana mai cewa; Hare-haren nasu martani ne akan laifukan yakin da HKI take yi a Gaza, ba kuma za su daina ba, sai an dakatar da aikata wadannan laifukan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Zagaye na 5 A Tattaunawar Gaza da HKI Ya tashi ba tare da Sun Dai-daita ba A Doha
Tattaunawa na baya-bayan nan tsakakin HKI da Hamas ya tashi ba tare da wani ci gaba ba a birnin Doha na kasar Qatar. Idan an cimma wannan yarjeniyar dai ana saran musayan fursinoni 10 na HKI sannan za’a saki wasu da dama dake hannun HKI,
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa rashin nasarar wannan taron ya sanya makomar yaki a Gaza cikin rudu don yanzun kuma ba’a san abinda zai faru ba. Kuma bamu san manufar HKI ba a wannan yakin.
Wani jami’in Falasdinawa ya fadawa tashar talabijin ta Al-Sharq kan cewa da alamun tawagar yahudawan sunzo ba taren da niyyar cimma wani Abu ba, tunda duk abunda aka tambayesu sai suce sai sun tambayi tel-Aviv, wanda ya nuna basu zo don cimma wata yarjeniya ba.
Don haka jami’in ya zargi HKI da wargaza tattaunawar. Mai yuwa kuma suna kan shirin na korar Falasdinawa daga Gaza gaba daya,