Majalisar Limaman Turai Ta Nesanta Kanta Daga Wadanda Su Ka Ziyarci HKI
Published: 10th, July 2025 GMT
Majalisar limaman musulmin nahiyar turai ta fitar da wani bayani da ta nesanta kanta daga wasu mutane da su ka kai ziyarar HKI tare da bayyana kansu a matsayin limamai daga kasashen turai, tana mai cewa, ko kadan ba su wakiltar al’ummar musulmin da suke cikin nahiyar ta turai.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai ofishin shugaban HKI Ishaq Herzog ya fitar da bayani da a ciki yake cewa; A ofis dinsa dake birnin Kudus ya karbi bakuncin limaman musulmi daga kasashen Faransa,Belgium, Holland, Italia da kuma Birtyaniya.
Ofishin majalisar limaman musulmin na turai, mai matsugunni a Faransa ya bayyana ziyarar mutanen zuwa Isra’ila da cewa, tana da daure kai, haka nan kuma lokacin da aka yi ta.”
Majalisar ta limaman turai din ta yi kira ga dukkanin ‘yantattu a duniya da su kasance a tare da al’ummar Falasdinu da ake zalunta, domin ganin an kawo karshen kisan kiyashin da sojojin mamaya suke yi musu.
Bugu da kari majalisar ta ce, wannan ziyarar tana nuni da yadda wadanda su ka yi ta ba su da lamiri na ‘yan’adamtaka da rashin riko da mafi karancin koyarwar musulunci ta yin kira da a taimaki gaskiya.”
Majalisar limaman na Turai ta kuma kara da cewa; ziyarar wani kokari ne na wanke ‘yan mamaya, kuma cin amanar Allah da manzon Allah ne da jinanen raunana.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar limaman
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa.
Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin
A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa.
Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa garkuwar jiki.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Muhammad Abdullahi, ya yi wa mahalarta horon bayani kan muhimmancin tsafta yayin al’ada domin gujewa kamuwa da cututtuka.
Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun Gabas, ya shawarci mahalarta da su mai da hankali ga sashen aikace-aikace na yadda ake sarrafa audugar mata a gida yayin horon.
Usman Muhammad Zaria