Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa
Published: 23rd, July 2025 GMT
Dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta lashi takobin sake maka shugabancin Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a gaban kotun daukaka kara bayan an hana ta shiga harabar majalisar a ranar Talata.
Cikin bacin rai, Natasha ta shaida wa ’yan jarida cewa za ta tattauna da lauyoyinta cikin gaggawa domin fara shigar da karar, tana mai cewa matakin ya saba da hukuncin kotun da ta bayar da umarnin a mayar da ita kan kujerarta.
Lamarin dai ya biyo bayan yadda jami’an tsaron da ke gadin majalisar suka tare hanya suka hana tawagar motocinta shiga majalisar, duk kuwa da umarnin kotu na mayar da ita.
HOTUNA: An ƙaddamar da aikin sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen $21bn a ƙetareTa kuma ce hatta dakatar da itan ma da farko ba ya kan ka’ida.
A cewar ta, “Yanzu zan je na tattauna da lauyoyina domin shirin daukaka kara alabasshi kotu ta fassara mana abin da ya faru. Ni mace ce mai bin dokokin kasa.”
Sanatar ta kuma yi alla-wadai da matakin da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya dauka na hana ta shigar, inda ta ce hakan tamkar raina kotu ne.
Ta kuma ce, “Akpabio bai fi karfin kundin tsarin mulkin Najeriya ba. Ina so ’yan Najeriya su sani cewa ba Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ne ya mayar da ni Sanata ba.
“Duk da cewa ya tafi daukaka kara, hakan ba yana nufin cewa ya soke hukuncin Mai Shari’a Binta Nyako ba ne kuma hakan ba zai dakatar da ni daga kasancewa Sanata ba.
“Mutanen Kogi ta Tsakiya ne suka zabe ni kuma su nake wakilta,” in ji Natasha.
Tun da farko dai Sanatar ta yi yunkurin shiga majalisar tare da magoya bayanta amma, amma aka hanata, dole sai da ta sauka ta tafi a kafa.
An dai girke tarin jami’an tsaron da ba a saba ganin irin su ba a majalisar, inda aka ga wasu jami’an na duba motoci tare da ma takaita yawan wadanda za su ajiya ababen hawa a wajen fakin na wajen majalisar.
Akalla an ga motocin sintiri na jami’an ’yan sanda guda biyar da aka girke a muhimman wuraren shiga majalisar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: a majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250 a Jami’ar Ilorin
Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.
An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin.
Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin.
Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.
Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar RuwaYa ce an riga an rattaba hannu kan yarjejeniya da Jami’ar Ilorin wadda ta ba wa masallacin damar mallaka da gudanar da ɗakin kwanan ɗaliban na tsawon shekaru 21 kafin a miƙa shi ga jami’ar.
Baya ga aikin ginin, Ɗangote ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira miliyan 5 a kowane wata domin kula da masallacin har sai an kammala aikin.
AbdulGafar ya ce wannan taimako zai rage nauyin kuɗin aikin, tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan masallacin.
Ya ƙara da cewa ɗakin kwanan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin wurin kwana ga ɗaliban jami’ar.
Shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa Ɗangote, sun bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi na yadda za a iya haɗa kai tsakanin cibiyoyin addini da ’yan kasuwa wajen ci-gaban al’umma.