Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra\ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa A Zirin Gaza
Published: 12th, July 2025 GMT
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban na Gaza, kuma Falasdinawa da dama sun yi shahada
Jiragen yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun ci gaba da ruwan bama-bamai a yankuna daban-daban na zirin Gaza a rana ta 117 da yakin ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama.
A cewar majiyoyin kiwon lafiya, sama da Falasdinawa 45 suka yi shahada tun daga wayewar garin Juma’a a zuwa safiyar yau a yankuna daban-daban na zirin Gaza.
Yousuf Al-Zaq, wanda aka bayyana shi a matsayin fursuna mafi ƙanƙanta bayan mamayar da aka kai wa gidansa da ke kan titin Al-Thawra a tsakiyar Gaza ya yi shahada.
An haifi Yousuf a cikin gidan yarin Isra’ila a shekara ta 2008, kuma sunansa yana da nasaba da labarin mahaifiyarsa, ‘yar fursuna Fatima Al-Zaq, wacce ta haife shi a gidan kurkuku.
Fararen hula 4 ne suka yi shahada yayin da wasu goma suka jikkata sakamakon harin bam da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida da ke kan titin Jaffa a unguwar Tuffah da ke gabashin birnin Gaza.
Kanun labarai
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NYT: Natanyahu Yana Tsawaita Yaki A Gaza Don Ci Gaba Da Kasancewa Kan Iko A HKI
Jaridar NYT ta kasar Amurka ta bayyana cewa firai ministan HKI Benyamin Natanyaho da gangan yake tsawita yaki a Gaza don tsawaita zamansa a kan kujerar shugabancin kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani binciken da Jaridar New York Times ta yi, inda take cewa Natanyahu ya san cewa matukar ya sauya matsayinsa na shugaban gwamnatin HKI to kuwa sammashin kamasi da kuma tuhume-tuhumen da ake masa zasu tashi wadanda zasu zama masa matsala, kuma a lokacin hatta gwamnatin Amurka ba zata iya yi masa wani taimako ba.
An fara yaki a Gaza ne a ranar 07 ga watan octoban shekara ta 2023 . daga lokacin ya zuwa yanzu sojojin Natanyahu sun kashe falasdinawa kimani 57,000. Sannan an jikata wasu fiye da 12000. Banda haka sun rusa fiye da kasha 90% na gaza. Sannan sun hana shiga abinci da ruwa har ya kaiga falasdinawa da dama sun mmutan saboda yuwan da rashin lafiya da wasu dalilai.