Jaridar Washington Post ta bayyana cewa: Cikakken gurgunta tashar jiragen ruwa na Eilat da ke haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana tasirin ikon Yemen

Jaridar Washington Post ta Amurka ta tabbatar da cewa rufe tashar jiragen ruwa ta Umm al-Rashrash na karshe ya nuna tasiri da karfin hare-haren Yemen ke da shi.

A cikin wani babban rahoto da aka buga a ranar Litinin, jaridar ta lura cewa, bayanan da jami’an mamayar Isra’ila suka yi game da gurguncewar da tashar jiragen ruwa ta yi, sun bayyana a fili “cikakkiyar nasarar da ‘yan Yemen suka yi.”

Jaridar ta yi hasashen cewa: Kasar Yemen za ta iya aiwatar da sauye-sauyen dabarun yaki a yankin, inda ta yi nazari kan wasu ayyukan sojojin ruwan kasar Yemen da suka tilastawa jiragen yakin Amurka gudu daga yankin, tare da sanadin nutsewar jiragen ruwa da dama da suka sabawa umarninsu, lamarin da ya sa sojojin Amurka da na yammacin Turai suka kasa yin komai a kansu.

Jaridar ta lura cewa ayyukan Yemen sun sanya tasirin su tun farkon harin da suka kai ga jirgin ruwan jigilar gwamnatin mamayar Isra’ila a karshen shekara ta 2023, da ya tabbatar da cewa ayyukan sun ragu da kashi 90 cikin 100 cikin kankanin lokaci, kafin tashar ta kai ga barin aiki kwata-kwata.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: jiragen ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne

Jami’in harkar shari’ar kasa da kasa ya bayyana cewa: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhu

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya ce: Harin da aka kai wa Iran babban laifi ne, kuma jarrabawa ce ta tarihi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.

A yayin wani taron manema labarai da ya yi da wakilan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya fiye da 110 a birnin New York na kasar Amurka a jiya Litinin, Gharibabadi ya bayyana ma’auni na wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauka kan yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma sakamakonsa ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

Ya dauki gwamnatin yahudawan sahayoniya a matsayin babbar mai  haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a yankin cikin shekaru 80 da suka gabata, yana mai jaddada cewa: Wannan ita ce gwamnatin da ya zuwa yanzu ta aiwatar da ayyukan ta’addanci sama da 3,000, tare da raba Falasdinawa sama da miliyan bakwai da muhallansu, da kashe dubban daruruwan Falasdinawa, tare da kame Falasdinawa sama da miliyan guda.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
  •  Iran Ta Yi Kira Ga “FIFA” Da Ta Kori “Isra’ila” Daga Cikinta
  • Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet
  • WHO Ta Buƙaci Isra’ila Ta Saki Ma’aikacinta Da Aka Kama A Gaza
  • Gwamna Namadi Ya Jinjinawa Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Bisa Ayyukan Raya Kasa
  • MDD Ta Gargaɗi Isra’ila Kan Tilasta Wa Al’ummar Deir al-Balah Na Gaza Tashi
  • Magudnar Ruwa Ta Yi Ajalin Rayuka Hudu A Zangon Kaya, Kano
  • Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Jinjinawa Gwamnan Kano Bisa Ayyukan Cigaban Jihar
  • Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne