Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
Published: 22nd, July 2025 GMT
Yau Talata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai na jerin taruka masu jigon “Kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”.
Yayin taron, jami’in kungiyar nakasassu ta Sin ya bayyana cewa, yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, an kiyaye hakki da moriyar nakasassu na kasar yadda ya kamata.
A halin yanzu, kasar tana da dokoki da ka’idoji sama da 180 da suka shafi kare nakasassu, ciki har da “Dokar gina muhalli marar shinge”, kuma akwai dokoki da ka’idoji 41 na kasa da suka kara tanade-tanade don kare hakkoki da muradun nakasassu a lokacin tsarawa da gyara abubuwan da suka shafi muhalli.
Bugu da kari, a lokacin aiwatar da “shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”, an aiwatar da wani shirin na tsawon shekaru uku (2022-2024) domin taimakawa nakasassu wajen samun ayyukan yi, inda yawan nakasassun dake samun ayyukan yi ya karu akai-akai. Ban da haka kuma, a cikin wannan wa’adi, nakasassu fiye da miliyan 9 ne aka ba su ayyukan yi a fadin kasar, kuma adadin sabbin ayyukan yi na nakasassu a birane da kauyuka ya kai miliyan 2.31. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA