Gwamnan Katsina Ya Dakatar Da Ma’aikatan Gidan Gyaran Hali Saboda Azabtar Da Wani Matashi
Published: 12th, July 2025 GMT
Gwamnatin ta ce ba za ta lamunci cin zarafi da amfani da iko ba da gangan wajen cutar da waɗanda ke cikin irin wannan cibiya ba.
Domin rage wa matashin raɗaɗi ta tallafa masa, gwamnatin jihar ta ba shi Naira dubu dari tara da saba’in (₦970,000) don yin magani, da kuma Naira miliyan 3.5 (₦3,500,000) domin sayen hannun roba da zai taimaka masa wajen yin rayuwa.
Gwamnan ya kuma amince da shirin sake fasalin cibiyar ta Babbar Ruga domin inganta ta da kuma hana irin wannan abu faruwa a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Radda
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina
Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 30 a ƙauyukan Kadisau, Raudama, da Sabon Layi da ke Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.
Jami’an tsaron sun haɗa da ’yan sanda, sojoji, da rundunar sojin sama ta Najeriya.
HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAANJami’an sun kai ɗauki ne bayan samun rahoton ’yan bindigar sun kai farmaki a lokaci guda a wurare daban-daban.
Amma, ’yan sanda uku da sojoji biyu sun rasa rayukansu a yayin artabu da ’yan bindigar.
Wani jami’in tsaro mai suna Ya’u Aliyu ya samu rauni.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.
Ya ce gwamnatin jihar tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan jami’an da suka rasu da kuma ragowar da abin ya shafa.
Ya ƙara da cewa iyalan waɗanda suka rasu za su samu tallafin gwamnati, kuma ba za a taɓa mantawa da sadaukarwarsu ba.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga da wanzar da zaman lafiya a jihar.
Ya roƙi al’umma da su kasance cikin shiri a koda yaushe kuma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.
Ya kuma ce bincike na ci gaba, kuma za a riƙa bayar da sabbin bayani a kai a kai.
“Ba za mu huta ba sai mun kawar da duk wani mai aikata laifi daga Jihar Katsina.
“Harkokin tsaro na ƙara inganta, kuma muna aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaron Tarayya domin tabbatar da tsaron kowa,” in ji Mu’azu.
“Da haɗin kanmu, za mu shawo kan wannan matsala kuma mu gina Katsina mai cike da zaman lafiya ga kowa da kowa.”