Ministar Raya Al’adu, Hannatu Musawa, ta ce ya kamata shugabancin ƙasar nan ya ci gaba da kasancewa a hannun ’yan Kudu domin a samu adalci da daidaito.

Ko da yake kundin tsarin mulkin Najeriya bai tilasta tsarin karɓa-karɓa ba, manyan jam’iyyun siyasa suna bin tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu.

An tsare mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote

A wata hira da ta yi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Hannatu Musawa ta ce tun da an samu Shugaba daga Arewa (Muhammadu Buhari) na tsawon shekaru takwas, to ya dace yanzu kuma a bar ’yan Kudu su yi shekaru takwas.

A shekarar 2023 ne Bola Ahmed Tinubu, wanda ɗan Kudu ne, ya gaji Buhari daga Arewa bayan kammala wa’adin mulkinsa.

Ministar ta ce: “Bayan shekara takwas na mulkin Buhari daga Arewa, ya kamata yanzu ’yan Kudu su ma su samu damar yin shekaru takwas don a samu adalci.”

A kwanakin baya, tsohon gwamnan Benuwe, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan ɗan takara daga Arewa ba.

Maganar karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu wani batu ne da ake ta muhawara a kai a siyasar Najeriya, kuma wasu masana na ganin yana hana dimokuraɗiyya ci gaba yadda ya kamata.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Buhari Hannatu Musawa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ne ya buɗe wa Buhari ƙofar zama shugaban ƙasa — Hadimi

Hadimin Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi, ya mayar wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha martani, kan cewa Tinubu bai taimaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba wajen zama shugaban ƙasa a 2015.

Ajayi, ya ce Buhari yana da ƙarfi sosai a Arewa amma hakan bai hana shi faɗuwa zaɓukan 2003, 2007 da 2011 ba.

Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata

Ya bayyana cewa a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi a 2014, Tinubu ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya lashe.

Ya ce Tinubu ne ya shawo kan gwamnonin APC da wakilan Kudu maso Yamma su mara wa Buhari baya a lokacin zaɓen da aka yi a filin wasa na Teslim Balogun a Legas.

Ya ce ba don wannan goyon baya ba, da Buhari bai samu tikitin takarar shugaban ƙasa ba.

Ajayi, ya ce bai dace a raina ƙoƙarin Tinubu da sauran waɗanda suka taimaka wa Buhari ba.

Ya ce Boss Mustapha bai faɗi gaskiyar abin da ya faru ba.

“Mu bar maganar babban zaɓen da Buhari ya lashe. Ai da bai zama ɗan takara a jam’iyyar APC ba, da ba zai taɓa zama shugaban ƙasa ba.

“Kuma da babu goyon bayan Tinubu a zaɓen fidda gwanin APC da aka yi a Legas a 2014, da Buhari bai lashe ba.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna tunanin sayar da matatun man Najeriya — NNPCL
  • Matatun Man Fetur Na Nijeriya Ba Za Su Ci Gaba Da Aiki Yadda Ya Kamata Ba – Dangote
  • Bafarawa Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Mai Suna “Arewa Cohesion Initiative” Don Maganin Kalubalen Da Yankin Arewa Ke Fuskanta
  • Tinubu ne ya buɗe wa Buhari ƙofar zama shugaban ƙasa — Hadimi
  • NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
  • 2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo
  • Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross
  • Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense
  • DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu?